09/06/2024
Tsohon sanatan Jihar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce gwamnatin Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai tafi ko wacce gwamnati sata a tarihin Jihar.
Haka zalika Shehu Sani ya bayyana cewa, sau ba adadi an masa barazanar kisa kawai ɗan ya bayyana gaskiya akan gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai.
Shehu Sani ya bayyana haka ne yayin wata hira da ayi da shi a gidan talabijin na Arise TV
Majiyar mu ta ruwaito cewa Sanata Shehu Sani yayi rubuce rubuce da dama akan irin zargin satar da aka yiwa gwamnatin jihar Kaduna keyi a lokacin mulkin El-Rufai.
A cewar Shehu sani a baya ana masa kallon kamar adawa ce take saka shi furta irin kalaman cewa gwamnatin El-Rufai tayi sata sai gashi Gaskiya tayi halinta.
Shehu Sani a wani sako da ya wallafa shafinsa na X ya bayyana binciken majalisar jihar Kaduna a matsayin bincike na gaskiya