14/10/2025
KAMAR A MAFARKI ZAKAJI ANA CEWA
Kamar a mafarki za ka ji ana cewa ai kuwa yamutu
Sai ka ji ana cewa a auna tsawansa Dan a gina maka Qabari Sai ka ji an ce Suwa s**a tafi ginin Qabarin โ
Kana ji ana cewa a nemo mai masa wanka. A je a samo likafani. ๐ญ
Kawai sai ka ji ana maka wanka k**ar a mafarki, sai ka ji ance an gama wanka a nemo mankara,
kwatsam sai ka ji ka a ciknta. Sai ka ji an ce wa Iyalanka, " Ku matso ku yi bankwan da shi ku yi masa addu'a"
Sai ka ji an ce: Liman ya zo a fito da shi,Kawai sai ka ji an daukoka za ka yi fitowa ta karshe daga cikin Yan uwanka da Iyalanka, wasu na kuka ๐ญ wasu kuma suna maka Addu'a ๐คฒ
Sai ka ji mutane suna yin kabbara ana maka sallah, sai ka ji ana tafiya da kai zuwa makabarta. ๐ญ
Ana zuwa bakin Qabari sai kji an ce ku aje shi a nan, sai kaji ance yan uwanka su matso ๐ญ k**ar a mafarki sai ka ji an daukoka daga cikin makara an ajiyeka cikin Kabari,
Sai ka ji ana cewa a kawo itatuwa ko tukane ๐ญ sai ka ji ana cewa a kawo ganye ๐ญ sai ka ji ana cewa a kwaba kasa, kana ji kana gani ba yanda ka iya ๐ญ
A haka za a yi maka Addu'a abarka daga kai sai halinka, ba mai iya yi maka komai
A haka za a dawo tun a cikin Makabarta wasu za su fara fira , a haka dai za a dawo gida a cigaba da dafa abinci ana baiwa masu zaman makoki kai kuwa sai dai in wani ya zo ya ce a yi maka Addu'a da an gama kuma a dasa fira
Kana can ga duhu ga kewa da kadaici, ga zafi ga yinwa ga kishirwa.
Kana cikin wannan halinne sai kuma masu tambaya su zo maka ๐ญ
Ya Allah ka bamu ikon yin guzuri na Alkairi sabida wannan rana ๐คฒ๐คฒ
๐Ya Allah ka sanya wannan tunatarwa ta zama SADAKATUL JARIYA a gareni da Iyayena da duk wanda ya taimaka wajan yadawa
Kada ka/ki Wuce Baka turawa jama'a ba. Allah Ya samuna daga cikin ma su samun babban rabo ranar gobe kiyama