M yusuf

M yusuf Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from M yusuf, Grocers, Dutsen alhaji bwari f c t abuja, Abuja.

12/04/2026
12/11/2025

🥀🌹🥀

Kana son rayuwa cikin aminci da nutsuwa da kwanciyar hankali?

Absheer ga sirri:
Kayi hakuri ka rayu cikin yarda da abinda Allah MaÉ—aukaki ya kaddara maka; domin duk wanda ya yarda da abinda Allah ya raba ya bashi zai rayu cikin Aljannar duniya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
"Duk wanda ya yarda to yana da yarda daga Allah, wanda kuwa yayi fushi shima Allah zai yi fushi da shi".
[Tirmizi].

Ka yarda da abin da ya kaddara maka ka rayu cikin nutsuwa da aminci da kwanciyar hankali.

Ya Allah ka sanya mu cikin bayinKa masu nutsuwa da hakuri da yarda da dukkan abin da Ka kaddara mana.

03/10/2025

Ga wasu code masu muhimmanci da zasu amfaneku:

1. *663 # Duba number waya ta MTN.

2. * #62 # Dubawa ko ana bibiyarka (Call Forwarding).

3. #31 # Cire private number.

4. *31 # Saka private number.

5. *305 # Dubawa da cire active services saboda satar kudin MTN.

6. * #06 # Duba IMEI na waya.

7. * #0* # Yin Restore na karamar waya.

8. *996 # Dora NIN a layi, duba layinkan dake connecting da NIN, da generating VNIN.

9. # #27 # Cire (Call Forwarding).

10. *121*6 # Duba wanda kafi kira a Airtel

11. **21*Number # Dora (Call Forwarding).

13. *346 # Duba NIN number.

14. *565*0 # Duba BVN Number.

15. *123*7*4 # Blocking layinka da aka sace ko faduwa kafin welcome back na MTN.

17. *312*65*4 # Sayen 2GB MTN Data a ₦500

Lura da wannan:

Wadannan code da suke a ƙasa sunada matuƙar muhimmanci, saboda zasuyi amfani a lokacin da aka sace ma wayarka koka yadda ta. Saboda idan baka rufe account ɗinka ba, wanda ya sace wayar zai iya sace maka kuɗi a account ta hanyar amfani da layinka.

1. Zenith: *966*911 #

2. Sterling Bank: *822*911 #

3. FCMB: *329*911 #

4. FirstBank: *894*911 #

5. Fidelity Bank: *770*911 #

6. Access Bank: *901*911 #

7. UBA: *919*911 #

8. Stanbic bank: *909*29 #

9. Keystone: *7111*911 #

10. Polaris Bank: *833*13*phone number #

11 Opay: *955*131 #

12 Moniepoint: *5573*911 #

ALLAH yatsaremu, wayoyinmu da Asusunmu na BANKI

゚
.

01/10/2025

YìN ZìNA ĎA BÙDURWA ĶAFIN AUŔE
Ki daure ki karanta har karshe zaki samu ilimin rayuwa:

SADUWA KAFIN AYI AURE

Yana kula da al amuranki
Yana kiranki a kodayaushe
Shi mai yawan nemanki ne
Kodayaushe cikin yi miki alkawarin baxantaba iya rabuwa dake ba
Yayi alkawarin kasan cewa tare dake a kowanne irin yanayi
Shi mutum ne nagari
Yayi miki alkawarin aure

INDA MATSALAR TAKE

Ya nemi da ki bashi kanki yayi zina dake
Kin tsorata da lafuzansa
Kin tsaya jinkiri kafin ki amince da bukatarsa

Amma daga baya sai kika amince domin kina gudun bacin ransa
Kinyi tunanin shi mutum ne nagari
Kinyi tunanin zai cika alkawarin da yayi miki

Ya ganki tsirara haihuwar uwarki
Yayi zina dake
Kin bashi abu mafi daraja da kima da k**e alfahari dashi
Shikuma yakasance cikin gagarumin farinciki

KIN BASHI KANKI KAFIN AURE

Sai yafara neman karin yin zina dake dake akai akai
Kin amince ya cigaba da kwanciya dake sau ba adadi
Sai kika fara ganin bakon sauyi daga gareshi

Ya fara nuna miki rashin kulawa kamar yadda yakeyi miki a baya
Yafara daukar zafi da yi miki fada akan dan kankanin laifi

Yafara jifanki da munanan kalmomi aduk lokacin da kuka samu sabani
Yafara ganinki a matsayin yar takura a gareshi

Hhhmm

KINSAN DALILIN FARUWAR HAKAN?

TO ZO KIJI

Saboda baki da wani abu na musamman da zaki bashi yaji kin birgeshi
Saboda baki da abinda zaiji yana dokinki
Saboda yana ganin kinyi arha sosai a gareshi

HABA YAR UWA ME K**E TUNANI NE A BAYA?

Kina tsammanin zai cigaba da yin tattalinki ne alhalin baki da wani abu da zaki birgeshi dashi?
Kina tsammanin zai ga darajarki ne bayan kin zamo mace mafi arha a gurinsa?

Kina tsammanin ya cigaba da kasan cewa tare dake bayan ya kwanta dake yayi zina dake
To dame kuma k**e so ki kara birgeshi?

Da me kuma zakiyi alfahari a matsayinki na ya mace a idanunsa ?
Zai kara gaba ne ya barki ya cigaba da bibiyar sauran mata,

Allah yasa mudace Allah ya hadaku da masoya na gaskiya ba mazinata ba

Allah yataimakemu yasa mudace da Alherinsa

📢

01/10/2025

*Tambaya Zuwa Ga Maza...*

Ba na goyon bayan mace ta tara samari, wallahi ko kaÉ—an...
Amma yallabai, waccan yarinyar da kake yawan kira da “sweetheart”, “baby”, ko “future wife” aurenta kake so kayi?
Wani shiri kake da shi akanta?
Kana da niyyar kare rayuwarka da ita, ko kuwa lokacinta kake kashewa don jin daÉ—in kanka?

Idan amsoshinka sune "Eh" to shin ta sani? Ka bata tabbaci da kwanciyar hankali kuwa?
Mata ba mu da buƙata mai yawa, so da tabbaci muke nema.
Amma idan muka rasa waÉ—annan biyu, komai na iya faruwa.

Ya kamata ku gane cewa rayuwar mace tana da takaitaccen lokaci a idon al’umma.
Kai namiji zaka iya jinkirta aure har shekara 40, kuma babu mai tambaya sai dai su ce “Lokacin ka ne baiyi ba” ko “Bai da lafiya ne.”
Amma mace fa? Tun da ga lokacin da ta kai shekara 20 ake fara kallonta da kallo biyu.
Ta ki aure? Hmm, me ke damunta? Rawan ido ne? Ko girman kai?

Idan ta haura shekara 30, an fara lakaba mata sunaye:
“Ƴar rainin hankali,” “bata da tarbiyya,” “mai yawan ta zubar,” har ma a ce “ƴar iska”.
Amma wai iskanci da wa take yi?
Da kanta take yi?
Ko da namijin da ya yaudareta da kalmomin "Zan aure ki," alhali cikin zuciyarsa ya san ba haka yake ba?

Wannan mugunta ce.
Ka san ba zaka aureta ba, amma baka janyewa, kuma baka barin wanda zai aure ta ya matso.
Sai ta ƙone da kai, ta ƙone da rayuwa gaba ɗaya.

Wallahi, idan kai kana cikin masu halin nan ka ji tsoron Allah, ka tuba.
Ka tuna fa: ita Ć´ar mutane ce.
Yayar wani ce.
Kanwar wani ce.
Uwar wani ce.
Kuma kai ma wata rana za ka haifi Ć´a mace.
Yaya zaka ji idan aka yi wa Ć´arka irin haka?

Ukty!

Ki ji tsoron Allah, ki rike mutuncinki.
Ke Ć´ace, halittar da Allah ya girmama.
Ya kiyaye ki daga haihuwa zuwa aure, kuma idan babu miji, to akwai yayu, Ć´aĆ´a, ko kanne da zasu tsaya miki.
Kar ki zubar da kanki sabida kalmar "Ina sonki zan aure ki"sai ki rasa komai.

In shaidan ya rinjaye ki sau É—aya, kada ki barshi ya maimaita.
Na farko kuskure ne.
Na biyu ganganci ne.
Na uku kuwa son zuciya ne.

Address

Dutsen Alhaji Bwari F C T Abuja
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when M yusuf posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category