16/01/2026
DUK NAMIJIN DA ZAIZO MIKI DA DAYA DAGA CIKIN WAƊANNAN HALAYEN TO MAYAUDARI NE
'Yar uwa, bude kunnanki da kyau. Zuciya tana da saukin yarda, amma hankali shine garkuwa.
Idan saurayi yana nuna miki wadannan halayen guda 5, to ki Gudu, kada ki tsaya jin "Ba haka nake nufi ba."
1. Mai Tsananin Gaggawa:
Kun hadu sati daya amma har ya fara maganar "Ke ce matata", "Zan gina miki duniya", "Ba zan iya rayuwa babu ke ba."
Maganar GaskiyaNamijin gaske yana daukar lokaci yana nazari kafin ya furta kalmar Aure. Mai gaggawa yana so ya rude ki ne ya samu abin da yake so ya gudu.
2. Mai Tsoron Zuwa Gida:
Kuna shekara kuna waya, amma da zaran kin ce: "Yaushe zaka zo gida a ganka?" sai ya fara bada uzuri.
"Ban shirya bane", "Akwai matsaloli a office", "Kiyi hakuri tukunna."
Maganar Gaskiya Wanda yake son ki da gaske, ba zai ji tsoron ganin Iyayenki ba. Wanda yake boyewa, wani abu yake nema daban.
3. Mai Neman Hujjar Soyayya:
Idan ya ce miki: "Idan kina sona ai zaki bani kanki" ko "Ki turo min hotonki na sirri don in tabbatar da amana."
Maganar Gaskiya Wannan shine babban Mayaudari. Soyayya mai daraja tana kare mutunci ne, bata cinye shi. Wanda yake son jikinki, ba zuciyarki yake so ba.
4. Mai Kiran Dare Kawai:
Da rana baya nemanki, baya son a ganku tare a fili. Sai dare ya yi tsakar dare sannan wayarsa take shigowa, yana maganganun shauki.
A Gaskiya, A "Reserve" yake ajiye ki. Akwai wacce yake baiwa lokacinsa na rana (Real girlfriend), ke kuma ta dauke kewar dare ce.
5. Mai Boye Wayarsa:
Idan yana tare da ke, wayarsa tana kife. Idan kira ya shigo, sai ya tashi ya koma gefe. Baya barin ki taba wayarsa ko da wasa.
Maganar Gaskiya Sirrin da yake boyewa, shine cewa ba ke kadai bace a rayuwarsa.
'Yar uwa, kada ki bari Kadarar Aure ta sa ki fada hannun Barawon Zuciya.
Namijin da yake son ki da gaske, zai Girmama ki, zai Kare ki, kuma zai Nemi hanyar Gidanku ba tare da kin tilasta shi ba.
Ya Allah, duk 'yar uwar mu da take hannun Mayaudari bata sani ba...
Ya Allah Ka bude idonta, Ka raba ta da shi, Ka canza mata da Nagari.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️