20/04/2026
Wani abun mamaki da takaici shi ne yadda ake samun mutane masu farin gemu, wadanda ya kamata a ce su ne jagorori wajen bada shawara ga matasa, amma sai ga shi sun zama silar zubar da jini da raba mutane da dukiya da kwanciyar hankali.
Ganin mutum da irin wadannan muggan makamai yana nuna cewa makiyin al'umma ba shi da takamaiman shekaru. Wannan tsoho ya zubar da kima da mutuncin da Allah ya ba shi na tsufa, ya zabi ya zama tsinanne a idon duniya.
Yada hotunan irin wadannan bata-gari yana da matukar alfanu ga tsaronmu.
Mutane da dama na iya sanin sa a wani gari ko unguwa amma ba su san abin da yake aikatawa ba. Yada hoton zai sa a san ainihin waye shi da kuma wadanda suke ta'asar tare.
Yana nuna wa sauran masu niyyar aikata hakan cewa, komai daren dadewa, hannun hukuma zai kai gare su kuma za a kunyata su a idon duniya.
Yana fadakar da al'umma cewa kada a amince wa mutum kawai saboda ganin gemunsa ko tsufansa; tsaro yana bukatar sa ido akan kowa.
Ba zamu fasa dora hotunan duk wanda ya shigo hannu ba. Matukar ba su daina ta'addanci ba, mu ma ba zamu daina yada fuskokin su don duniya ta shaida mummunar ta'asar su ba.
Tambayata a gare ku Shin kuna ganin akwai bukatar kara kaimi wajen bincikar ko akwai wasu masu boyewa a karkashin inuwar dattawa a unguwanninmu?
Idan har akwai kuma baqine matukar baku yadda da su ba to ku tashe su a unguwar ku idan haya suke, Idan kuma siyan Gidan sukayi to ku sayi gida ku tashe su a unguwar ku wannan shine kawai.