Shaheed Ahmad Zakzaky

Shaheed Ahmad Zakzaky Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Shaheed Ahmad Zakzaky, Grocers, Abuja.

Assalamualaikum Ya Shuhadah min Jaishu Ahmad🕊️🥺
15/10/2026

Assalamualaikum Ya Shuhadah min Jaishu Ahmad🕊️🥺

11/10/2026

Official: Jadawalin taron Ahmad week na Bana, tare da taron 'International Youth Conference'.

Muna yi wa matafiya, tare da sauran mahalarta fatan sauka lafiya.


Gayyata Zuwa Gangamin Twitter Domin Ahmad WeekJaishu Shaheed Ahmad Zakzaky, na gabatar muku, tare da gayyatar ku zuwa ga...
08/10/2026

Gayyata Zuwa Gangamin Twitter Domin Ahmad Week

Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky, na gabatar muku, tare da gayyatar ku zuwa gangamin Twitter (Twitter Trend) domin Ahmad Week.

Wannan gangamin an tsara shi ne domin bayyanawa duniya rayuwa, ayyuka tare da tasirin Shaheed Ahmad Zakzaky. A yayin wannan gangamin, za a fitar da bayanai waɗanda s**a kebance ayyuka, nazarce-nazarce tare da tasirin Shaheed Ahmad Zakzaky.

Har wala yau, a ranar gangamin, akwai tattaunawa tsakanin wasu daga cikin waɗanda s**a rayu kuma s**a tasirantu daga Shaheed Ahmad Zakzaky, inda za su yi bayanai akan rayuwarsa.

Wannan gangamin zai kasance ne a rana ta farko daga cikin jerin kwanaki bakwai na Makon Shaheed Ahmad. Muna gayyatar dukkan ƴan uwa domin yin musharaka cikin wannan ibada.

Gangamin zai kasance kamar haka:

Rana: 11th October, Lahadi

Lokaci: 4:00 PM

Taken gangamin:




Sanarwar: Fa'eez Media

TARIHIN RAYUWAR SHAHEED AHMAD ZAKZAKY (H)KASHI NA 08 — SAYYID AHMAD DA TAUSAYINSA GA AL’UMMASayyid Ahmad mutum ne mai ts...
06/10/2026

TARIHIN RAYUWAR SHAHEED AHMAD ZAKZAKY (H)

KASHI NA 08 — SAYYID AHMAD DA TAUSAYINSA GA AL’UMMA

Sayyid Ahmad mutum ne mai tsananin tausayi da hangen nesa. Duk abin da ya shafi al’umma yana matuƙar damunsa.

Ya kasance yana nuna ƙiyayya ga zalunci da azzalumai, tare da nuna tausayi ga waɗanda ake zalunta.

Ya kan bayyana yadda zalunci yake damunsa, har ya ce:

«“Na rasa yadda zan siffanta irin wannan zaluncin, har nakan ji kamar raina zai fita.”»

Haka kuma, Sayyid Ahmad yana matuƙar son yara. Duk inda yake, yara suna son kasancewa kusa da shi saboda kyakkyawar mu’amalarsa da su.

Ya ba da muhimmanci sosai ga tarbiyyar yara da makomarsu. Daga cikin abubuwan da aka samar akwai Daura (IVC), lokutan wasannin yara a wasu bukukuwa, Rundunar Sayyid Abul-Fadal Abbas (AS) da kuma Daura Ilmiyya.

Manufarsa ita ce a ba yara tarbiyya da ilimin da zai taimaka musu wajen zama nagartattun mutane a nan gaba.

Ya kasance yana ganin cewa makomar al’umma tana da alaƙa da tarbiyyar yara tun suna ƙanana.

— Tahir Ibrahim Gwarzo

TARIHIN RAYUWAR SHAHEED AHMAD ZAKZAKY (H)KASHI NA 06 — KARATUN BOKO NA SAYYID AHMADSayyid Ahmad ya yi karatun Primary a ...
05/10/2026

TARIHIN RAYUWAR SHAHEED AHMAD ZAKZAKY (H)

KASHI NA 06 — KARATUN BOKO NA SAYYID AHMAD

Sayyid Ahmad ya yi karatun Primary a Buss International School, da ke kusa da filin koyar da tukin jirgin sama na Aviation a Zariya, daga shekarar 1996 zuwa 2002.

Daga nan ya halarci Thybow International School, Zaria, daga shekarar 2002 zuwa 2004.

A shekarar 2005, ya koma Zaria Academy, inda ya yi karatu har zuwa shekarar 2007.

Daga nan ya koma Holemark, inda aka yi masa double promotion, ya tsallaka tuuwa SS2 maimakon SS1.

Ya kammala karatun Secondary School a shekarar 2009.

Bayan kammala Secondary School, bai samu damar ci gaba da karatu nan take ba sai shekarar 2011. A wannan lokacin, ya yi amfani da damar wajen gudanar da bincike da kara zurfafa iliminsa, tare da taimaka wa mahaifinsa a ayyukan yau da kullum.

Ya kuma samu darussa daga malamai kamar Malam Kabiru Abbas, Malam Kabiru Ado da Malam Ibrahim Physics, wadanda s**a ba da gagarumar gudummuwa wajen ci gaban karatu

_ Tahir Ibrahim Gwarzo

Labarin gwagwarmaya mai ɗorewa “ Sayyid Hassan Nasrallah ya tafi, amma arzikin da ya kafa ta tsaya daram. Labarin Hizbul...
05/10/2026

Labarin gwagwarmaya mai ɗorewa

“ Sayyid Hassan Nasrallah ya tafi, amma arzikin da ya kafa ta tsaya daram. Labarin Hizbullah na Lebanon labari ne mai ɗorewa... wannan wata babban arziki ne ga Lebanon da ma sauran kasashe. ”

—Shahid Imam Sayyid Ali Khamene'i — 23/09/2025

Yau Lahadi kwana Bakwai ya yi saura kafin fara babban taron Ahmad week na wannan shekara, tare da taron 'International Y...
04/10/2026

Yau Lahadi kwana Bakwai ya yi saura kafin fara babban taron Ahmad week na wannan shekara, tare da taron 'International Youth Conference'



Jasaz Ta Shirya Youth International Conference Karo Na FarkoJaishu Shaheed Ahmad Zakzaky ta shirya taron matasa mai suna...
01/10/2026

Jasaz Ta Shirya Youth International Conference Karo Na Farko

Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky ta shirya taron matasa mai suna 'Youth International Conference' kashi na farko. Kamar yadda sanarwar ta gabata a shafin Fa'eez Media, wannan taro ne da aka shirya domin duba i zuwa rayuwar matasa.

Taron zai tabo janibobi daban-daban da suke da alaƙa da rayuwar matasa. Masana daga ɓangarori da wurare daban-daban za su yi baje kolin bahasoshi tare da musayar tunanuka da nazurra a kan maudu'ai da s**a shafi rayuwar matasa.

Har wala yau, taron zai haɗa matasa daga sassa da kuma ƙasashe daban-daban. Ana sa ran wannan taron zai zama babbar mahadar da ke haɗa matasa domin yin duba da nazari gas rayuwa da kuma makomarsu. Shafin Fa'eez TV zai kasance ɗaya daga cikin kafafen da za ku iya riskar wannan gagarumin taro. Ku kasance tare da mu.

— Fa'eez TV

Shaheed Ahmad Zakzaky (H) 🫡
21/09/2026

Shaheed Ahmad Zakzaky (H) 🫡

بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ"مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْ...
15/09/2026

بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ

"مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبْدِيلًا"

Cikin alhini da juyayi muke miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga Sahibul Asr (Ajjalallah Farajahu Sharif), da jagoran mu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).

Na Rashin; Marhum Muhammad Abdullahi

Yau Talata: 15/09/2026. Yayi dai dai da kwana uku na rasuwar: Marhum Muhammad Abdullahi

Marhum ya kasance jajirtaccen ɗan uwa mai sallamawa da jajircewa, kuma hazikin matashi mai himma wajen kula da addini, sannan ya kasance cikakken ma'aikaci a cikin matasa na rundunar Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky (JASAZ) a Zone ɗin Mukhtar Assakafy, kuma mai bada gudunmawa da himma wajen sauke nauyin da ke kansa.

Ya rasu a ranar Lahadi. 13/09/2026, sakamakon accident da ya ritsa dashi akan hanyar dawowa Muzahara a garin Wurno zuwa Achida wanda anan ya cimma wa'adin sa.

Muna ƙara miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyaye, abokai da ƴan uwansa, Allah ya girmama matsayin sa ya karɓi uzurinsa, ya sadashi da Shahidan Muslumci.

Muna roƙon ƴan uwa da su sanya shi cikin addu'oin su tare da barar Fatiha daya, da Salatin Annabi goma sadaukarwa zuwa ga ruhin sa.

KULLU NA AHMAD YA ABA AHMAD

JASAZ Shuhada Department.
15/09/2026.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shaheed Ahmad Zakzaky posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category