16/07/2026
DANGANE DA IRAN.....
Rahotanni sun ce hare-haren Amurka kan Iran sun ci gaba da aukuwa ba tare da tsayawa ba fiye da awa guda, musamman ta wuraren Bandar Abbas, Ahvaz, Tsibirin Qeshm da Bushehr.
An ce hare-haren sun fi mayar da hankali kan muhimman ababen more rayuwa, musamman hanyoyin sadarwa da layukan wutar lantarki, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a yankuna da dama tare da kawo cikas ga ayyukan wasu asibitoci.
A cewar rahotannin, mutane bakwai sun jikkata, ciki har da mutum uku daga iyali guda da s**a samu raunuka marasa tsanani, da kuma wasu jami'an tsaro. A Tsibirin Qeshm kaɗai, an ce an ji fashewa takwas, wasu daga cikinsu sun afku a yankunan da fararen hula ke zaune. Har yanzu ba a san ko wane wurare ne aka nufa kai tsaye ba, ko kuma fararen hula ne s**a faɗa cikin harin.
Rahotannin sun nuna cewa Amurka na ƙara faɗaɗa hare-harenta, kuma ana kallon lamarin a matsayin babban sauyi na yaƙin da aka shiga. A gefe guda, an ce jami'an tsaron Iran sun shiga cikin shirin ko-ta-kwana domin tunkarar duk wata barazana.
Ana kuma ganin cewa manufar hare-haren ita ce raunana muhimman ababen more rayuwa kafin duk wani yiwuwar farmakin ƙasa, kamar yadda s**ai a Gaza da Kudancin Lebanon, da taimakon larabawan Dubai, Kuwait, Bahrain, Qatar ake gudanar da waɗannan hare haren.
Baya ga haka, rahotanni sun ce hare-haren sun bazu zuwa wasu yankunan kudancin Iran. An ce jiragen yaƙin Amurka sun kai hari kan Filin Jirgin Sama na Iranshahr, inda mazauna yankin s**a ba da rahoton jin ƙarar fashewa uku masu ƙarfi, tare da bayyana harin a matsayin mai tsanani saboda ƙarar fashe fashe.
Haka kuma, an ce hare-haren saman Amurka sun lalata wata gada da ke Kahourestan a Bandar Abbas. Rahotanni sun kuma ce an sake kai hari a Bampur da Iranshahr, yayin da sansanonin jiragen sama da filayen jiragen sama a sassan Sistan da Baluchestan su ma s**a fuskanci hare-hare.
Kazalika, kafafen yaɗa labaran Iran sun ba da rahoton cewa an samu fashewa 11 a kusa da ƙauyen Mesen da ke Tsibirin Qeshm