12/07/2023
BA DUKKAN SAHABBAI NE ALLAH YAYIWA ALKAWALIN SHIGA AL-JANNAH BA; AKWAI SAHABBAI DA YAWA DA ZASU SHIGA WUTAR JAHANNAMA
IDAN DUK SAHABBAI ‘YAN AL-JANNAH NE; ME YA SA ALLAH ZAI SAUKAR DA SURAR MUNAFUKAI A QUR’ANI?
IDAN MUNAFIKI BAYA ZAMA SAHABI SAI DAI YANA IYA ZAMA TARE DA SAHABBAI, TO MUNAFUNCI A FILI YA KE KO A ZUCIYA? TAYA ZAMU IYA TABBATAR CIKIN SAHABBAI BA MUNAFUKAI?
IDAN SAHABI SHINE WANDA YA HAFB_IMG_1515147094543DU DA ANNABI MUHAMMAD(SAW); YANA MAI IMANI DA SHI, KUMA YA MUTU A KAN MUSULUNCI:
KENAN BA DUK WANDA YA MUSULUNTA A LOKACIN ANNABI(SAW) NE SAHABI BA?
TAYA ZAMU GANE SAHABI; TUNDA LALLE NE YA KASANCE MAI IMANI, ALHALI IMANI A ZUCIYA YAKE?
KENAN MUNA BUKATAR SANIN GAIBI KO WANI WANDA YA SAN GAIBI; KAFIN MU TABBATAR DA SAHABBANCIN KO WANE SAHABI?
YA ZAMU YI DA AYOYIN DA KE TABBATAR DA AKWAI MUNAFUKAI CIKIN SAHABBAI?
KO MASU AKIDAR DUK SAHABBAI ‘YAN AL-JANNAH SUN YARDA DA AKIDAR TAHRIFI (JIRKITA QUR’ANI TAHANYAR RAGI KO KARI)?
KENAN DUK WANDA YACE; DUKKAN SAHABBAI YARDADDU NE KUMA ‘YAN AL-JANNAH NE; TO YA KARYATA AYOYI DA YAWA A QUR’ANI DA INGANTATTUN HADISAI MASU YAWAN GASKE?
KENAN AYOYIN QUR’ANI DA INGANTATTUN HADISAI SUN TABBATAR MANA DA CEWA; BA DUKKAN SAHABBAI NE ALLAH YAYIWA ALKAWALIN SHIGA AL-JANNAH BA; AKWAI SAHABBAI DA YAWA DA ZASU SHIGA WUTAR JAHANNAMA?
Wasu su kan kafa hujja da wasu ayoyin Qur’ani akan cewa Allah yayi al-kawalin Al-Jannah ga dukkan Sahabbai, misali:
Fadin Allah(saw);
ﻟَﺎ ﻳَﺴْﺘَﻮِﻱ ﻣِﻨْﻜُﻢْ ﻣَﻦْ ﺃَﻧْﻔَﻖَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻞِ ﺍﻟْﻔَﺘْﺢِ ﻭَﻗَﺎﺗَﻞَ ﺃُﻭﻟَﺌِﻚَﺃَﻋْﻈَﻢُ ﺩَﺭَﺟَﺔً ﻣِﻦَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺃَﻧْﻔَﻘُﻮﺍ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪُ ﻭَﻗَﺎﺗَﻠُﻮﺍ ﻭَﻛُﻠًّﺎ ﻭَﻋَﺪَﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﺤُﺴْﻨَﻰ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻤَﺎ ﺗَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ ﺧَﺒِﻴﺮٌ.
“Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara, kuma ya yi yaki daga cikinku, baya zama daidai (da wanda bai yi hakan ba). Wadancan sune mafifitan girman daraja, bisa ga wadanda s**a ciyar daga baya kuma su ka yi yaki. Kuma dukansu Allah Ya yi mu su alkawli da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa”.
(ﺍﻟﺤﺪﻳﺪ : 10).
Shin wannan ayar ta nuna Sahabban da s**a yi jihad da infaki kafin fatuhu Makka ma’asumai ne? Idan ba ma’asumai ba ne; to wanda yayi wani aiki irin na ‘yan wuta daga baya (kamar kisan kai; irin yanda Fi’atul-bagiya s**a yi) to shi ma ba shida wani laifi; tunda an yi masa alkawalin Al-jannah?
Me ya sa wadanda ke kafa hujja da wannan ayar ba su kawo farkon ayar? Saboda farkon ayar yana nuna yanda wasu Sahabbai s**a ki tallafawa Musulunci da dukiyoyinsu? kamar yanda Allah ya ke cewa:
وَمَا لَكُمْ أَلَّا تُنفِقُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَاثُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ لَا يَسْتَوِي مِنكُم مَّنْ أَنفَقَ مِن قَبْلِ الْفَتْحِ وَقَاتَلَ ۚ أُولَٰئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً مِّنَ الَّذِينَ أَنفَقُوا مِن بَعْدُ وَقَاتَلُوا ۚ وَكُلًّا وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَىٰ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
“Me ya sa baku ciyar da dukiyarku wajen dauka kalmar Allah? Allah ne majibincin Sammai da kassai….”
Kenan akwai wasu Sahabbai masu yiwa Allah rowa da kin ciyar da dukiyar su wajen daukaka addinin Musulunci?
Shin ba ku kula da Fadin Allah cewa; ﻣِﻨْﻜُﻢ (daga cikinku) ba; a ayar? Kenan ya nuna ba dukkan Sahabban da s**a musulunta kafin Fatahu Makka; ayar take magana akan su ba? wadansu ne daga ciki? Idan dukkan Sahabban da s**a muasulunta kafin Fatahu Makka ayar take magana; to me ya sa aka kawo ‘Tab’idiyya’?
Idan har dukkan Sahabban da s**a musulunta kafin Fatahu Makka sun yi infaki da jihadi me ya sa Allah zai ce;
ﻫَﺎ ﺃَﻧْﺘُﻢْﻫَﺆُﻟَﺎﺀِ ﺗُﺪْﻋَﻮْﻥَ ﻟِﺘُﻨْﻔِﻘُﻮﺍ ﻓِﻲ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟﻠَّﻪِﻓَﻤِﻨْﻜُﻢْ ﻣَﻦْ ﻳَﺒْﺨَﻞُ ﻭَﻣَﻦْ ﻳَﺒْﺨَﻞْ ﻓَﺈِﻧَّﻤَﺎ ﻳَﺒْﺨَﻞُ ﻋَﻦْ ﻧَﻔْﺴِﻪِ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻐَﻨِﻲُّ ﻭَﺃَﻧْﺘُﻢُ ﺍﻟْﻔُﻘَﺮَﺍﺀ.
“Ga kunan (ku Sahabbai), kune ake kiranku ku yi infaki amma wasunku suna rowa…”.
(Suratu Muhammad(saw); ayata 38).
Idan har wannan ayar tana nuna duk Sahabin da yayi jihadi da infaki kafin fatahu Makka dan Al-Jannah ne; me ya sa Allah zai ce;
ﻭَﺇِﻥْ ﺗَﺘَﻮَﻟَّﻮْﺍ ﻳَﺴْﺘَﺒْﺪِﻝْ ﻗَﻮْﻣًﺎ ﻏَﻴْﺮَﻛُﻢْ ﺛُﻢَّ ﻟَﺎﻳَﻜُﻮﻧُﻮﺍ ﺃَﻣْﺜَﺎﻟَﻜُﻢ.
“Idan (ku Sahabbai) kun juya baya (kun canza ayuka masu kyau da munana) (Allah) zai canza wasu mutane da ban; ba irinku ba, kuma ba zasu zama tamkar ku ba”.
(Suratu Muhammad(saw); ayata 38).
Kenan wannan ayar tana nuna ko da sahabi yayi jihadi da infaki; idan har ya canza daga baya; to Allah zai canza masa sakamako?
Cewa ayar tana nuna Abubakar, Umar, Usman… ‘yan Al-Jannah ne; Saboda sun yi infaki (ciyarwa) kafin bude Makka. Ba wata ruyawa da ta inganta da ta nuna Abubakar, Umar, Usman… Sun yi infaki kafin Fatahu Makka.
Ayar tana nuna cewa lalle wanda aka yiwa al-kawalin husna (Al-Jannah) a ayar sun yi jihadi, kuma sun kashe kafirai a jihadi. Kenan ayar ba akan su Abubakar, Umar, Usman… take magana ba, saboda ba wata ruyawa da inganta da ta nuna Abubakar, Umar ko Usman sun taba kashe wani kafuri a fagen daga, ba ruwaya ingantatta da ta nuna sun taba yin mubaraza, gwarzantaka ko jarunta a fagen yaki. Hasalima ruwayoyi ingantattu da littattafan Ahlus-Sunnah; sun nakalto yanda s**a ari takalmin kare a filin yakin Uhud, Khaibar, Hunai…
Shin ko ba ku san cewa ranar yakin Uhud; Abubakar, Umar, Usman… Sun gudu daga faken yaki?
Ko ba ku karanta hadisur-Raya (Hadisin bada tuta ga Imam Ali a Yakin khaibar) ba? Me ya sa aka tura Abubakar da Umar s**a gudo?
Me ya sa a yakin Ahzab Abubakar, Umar, Usman.. basu tari sadaukin kafirai Amr bin Abduwud ba? Me ya sa Imam Ali(as) ne kadai ya nuna jarubta a ranar?
Me ya sa a yakin Hunain Abubakar, Umar, Usman… S**a ranta a na kare?
Imam Malik a Muwatta, ya tabbatar mana da cewa, Annabi(saw) ya ki yiwa Abubakar bushara da Al-Jannah, saboda ya san zai canza bayan wafatinsa(saw). Ga matanin ruwayar:
ﻭَﺣَﺪَّﺛَﻨِﻲ ﻋَﻦْ ﻣَﺎﻟِﻚٍ، ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﺍﻟﻨَّﻀْﺮِ، ﻣَﻮْﻟَﻰ ﻋُﻤَﺮَ ﺑْﻦِ ﻋُﺒَﻴْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺃَﻧَّﻪُ ﺑَﻠَﻐَﻪُ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ(ص) ﻗَﺎﻝَ ﻟِﺸُﻬَﺪَﺍﺀِ ﺃُﺣُﺪٍ “ﻫَﺆُﻻَﺀِ ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢْ”. ﻓَﻘَﺎﻝَ ﺃَﺑُﻮ ﺑَﻜْﺮٍ ﺍﻟﺼِّﺪِّﻳﻖُ ﺃَﻟَﺴْﻨَﺎ ﻳَﺎ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺑِﺈِﺧْﻮَﺍﻧِﻬِﻢْ ﺃَﺳْﻠَﻤْﻨَﺎ ﻛَﻤَﺎ ﺃَﺳْﻠَﻤُﻮﺍ ﻭَﺟَﺎﻫَﺪْﻧَﺎ ﻛَﻤَﺎ ﺟَﺎﻫَﺪُﻭﺍ . ﻓَﻘَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ(ص) “ﺑَﻠَﻰ ﻭَﻟَﻜِﻦْ ﻻَ ﺃَﺩْﺭِﻱ ﻣَﺎ ﺗُﺤْﺪِﺛُﻮﻥَ ﺑَﻌْﺪِﻱ” . ﻓَﺒَﻜَﻰ ﺃَﺑُﻮ ﺑَﻜْﺮٍ ﺛُﻢَّ ﺑَﻜَﻰ ﺛُﻢَّ ﻗَﺎﻝَ ﺃَﺋِﻨَّﺎ ﻟَﻜَﺎﺋِﻨُﻮﻥَ ﺑَﻌْﺪَﻙَ”.
(Muwatta Malik, Littafin Jihadi: 21, Hadisi na 993).
Idan ayar ta nuna an yiwa Abubakar… al-kawalin Al-Jannah, me ya sa Annabi(saw) bai yimasa busharar ba? Me ya sa Annabi(saw) zai ce; “Ban san abinda zaku aikata bayana ba”? Kenan hakan yana nuna Annabi(saw) ya san zasu aikata wani abu a bayansa? Ko kun fi Annabi(saw) sanin Qur’ani?
Idan har ayar tana nuna an yiwa Umar alkawalin Al-Jannah; ME YA SA UMAR YA GAGARA SAMUN NUTSUWA; YAYI TA BIN HUZAIFA AKAN YA GAYAMASA YANA CIKIN MUNAFUKAI KO BAYA CIKI?
Me Ya sa Umar Ya Takura A Gayamasa Yana Cikin Munafukai Ko Baya Ciki?
Shin Bai Yarda Da Alkawalin Al-jannar bane?
ME YA SA UMAR DAN KHADDAB BAI JE JANA’IZAR ABOKINSA; ABUBAKAR BA? An Tambayi Umar Me Ya sa Baka je Jana’izar Abubakar ba? Sai Umar Yace Saboda Huzaifa Bai je Ba.
Huzaifatul Yamani Shine Wanda Ya san Munafukai, Kuma Duk Wanda Huzaifa Bai je Jana’izar Sa Ba To Munafiki Ne.
Shin Ko Kunsan Cewa Amr Bin Ass Ne Yayi Sallah Ga Abubakar kuwa? Shin Kunsan Waye Amr kuwa? To ku duba; Al-isti’ab na Ibn Abdulbar Juz’i Na 1 Shafi Na 228. Siratul Halbiya Juz’i Na 3 Shafi Na 143. Al-fitna Bainas-Sahaba Shafi Na 80… Ku ganewa idonku.
Fadin Allah(swt):
ﻭَﺍﻟﺴَّﺎﺑِﻘُﻮﻥَ ﺍﻷَﻭَّﻟُﻮﻥَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﻬَﺎﺟِﺮِﻳﻦَ ﻭَﺍﻷَﻧْﺼَﺎﺭِ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﻫُﻢْ ﺑِﺈِﺣْﺴَﺎﻥٍ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻬُﻢْ ﻭَﺭَﺿُﻮﺍ ﻋَﻨْﻪُ ﻭَﺃَﻋَﺪَّ ﻟَﻬُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﺗَﺠْﺮِﻱ ﺗَﺤْﺘَﻬَﺎ ﺍﻷَﻧْﻬَﺎﺭُ ﺧَﺎﻟِﺪِﻳﻦَ ﻓِﻴﻬَﺎ ﺃَﺑَﺪًﺍ ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟْﻔَﻮْﺯُ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢُ.
“Kuma wadanda fara (shiga Musulunci) daga Muhajirin da Ansar da wadanda s**a biyo bayan su da kyautatawa, Allah Ya yarda da su; su ma sun yarda da Shi, kuma Ya yi masu tattalin gidan Al-janna; koramu suna gudana a karkashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma”.
(Q : 9 : 100).
Saboda Allah tabbatar da ba dukkan Sahabbai ne “Sabikunal-auwalun” ba; bayan wannan ayar sai Allah ya ce;
وَمِمَّن حَولَكُم مِنَ الأَعرابِ مُنافِقونَ ۖ وَمِن أَهلِ المَدينَةِ ۖ مَرَدوا عَلَى النِّفاقِ لا تَعلَمُهُم ۖ نَحنُ نَعلَمُهُم ۚ سَنُعَذِّبُهُم مَرَّتَينِ ثُمَّ يُرَدّونَ إِلىٰ عَذابٍ عَظيمٍ.
“Kuma daga cikin wadanda ke tare da ku (Sahabbai); daga Larabawa akwai munafukai, haka kuma daga cikin mutanen Madina (akwai munafukai), sun kware a cikin munafunci, kai ba ka san su ba, mu ne muka san su, da sannu za mu yi musu azaba sau biyu, sannan kuma mu mayar da su zuwa ga azaba mai girma”.
(Q: 9 : 101).
Sannan kuma, Me harafin ﻣِﻦَ yake nufi a harshen Larabci? Me ya sa Allah ya ce “daga cikin muhajirun da Ansar” (ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﻬَﺎﺟِﺮِﻳﻦَ ﻭَﺍﻷَﻧْﺼَﺎﺭِ) kenan ba dukkan Sahabbai Muhajirun da Ansar ake nufi ayar ba?
Ya zaku yi da Sahabbai muhajirun da Ansar da suke cikin Fi’atul-bagiya, ‘Yan Jamal…? Ko kun koma ‘yan Qur’aniyyun ne baku yarda da Hadisai ba?
Idan ma kun koma ‘yan Qur’aniyyun ya zaku yi da fadin Allah(saw):
ﻭَﻣِﻤَّﻦْ ﺣَﻮْﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺄَﻋْﺮَﺍﺏِ ﻣُﻨَﺎﻓِﻘُﻮﻥَ ﻭَﻣِﻦْ ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﻤَﺪِﻳﻨَﺔِ ﻣَﺮَﺩُﻭﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻨِّﻔَﺎﻕِ ﻟَﺎ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻬُﻢْ ﻧَﺤْﻦُ ﻧَﻌْﻠَﻤُﻬُﻢْ ﺳَﻨُﻌَﺬِّﺑُﻬُﻢْ ﻣَﺮَّﺗَﻴْﻦِ ﺛُﻢَّ ﻳُﺮَﺩُّﻭﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﻋَﺬَﺍﺏٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ.
Su waye ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﻤَﺪِﻳﻨَﺔِ? Shin akwai bambanci da tsakanin ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﻤَﺪِﻳﻨَﺔِ da ﺍﻷَﻧْﺼَﺎﺭِ a istilahin lokacin Annabi(saw)?
Idan ﺍﻷَﻧْﺼَﺎﺭِ sune ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﻤَﺪِﻳﻨَﺔِ to kenan hakan kara tabbatar ba dukkan Sahabbai ne Allah yake nufi a ayar:
ﻭَﺍﻟﺴَّﺎﺑِﻘُﻮﻥَ ﺍﻷَﻭَّﻟُﻮﻥَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﻬَﺎﺟِﺮِﻳﻦَ ﻭَﺍﻷَﻧْﺼَﺎﺭِ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﻫُﻢْ ﺑِﺈِﺣْﺴَﺎﻥٍ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻬُﻢْ ﻭَﺭَﺿُﻮﺍ ﻋَﻨْﻪُ ﻭَﺃَﻋَﺪَّ ﻟَﻬُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﺗَﺠْﺮِﻱ ﺗَﺤْﺘَﻬَﺎ ﺍﻷَﻧْﻬَﺎﺭُ ﺧَﺎﻟِﺪِﻳﻦَ ﻓِﻴﻬَﺎ ﺃَﺑَﺪًﺍ ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟْﻔَﻮْﺯُ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢُ.
Kenan ba dukkan Sahabbai ne masu imani na gaskiya ba? Shin su Munafukan Sahabbai ne? Kada ku manta fa; duk mai kin Imam Ali(as), to munafiki ne, inji Annabi(saw).
Kuma Annabi(saw) ya tabbatar mana akwai munafikai a cikin Sahabbai, kamar yanda yazo a wannan ruwayar:
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻭﻛﻴﻊ، ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺳﻔﻴﺎﻥ، ﻋﻦ ﺳﻠﻤﺔ، ﻋﻦ ﻋﻴﺎﺽ ﺑﻦ ﻋﻴﺎﺽ، ﻋﻦﺃﺑﻴﻪ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﻗﺎﻝ: ﺧﻄﺒﻨﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ﺹ) ﺧﻄﺒﺔ ﻓﺤﻤﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺃﺛﻨﻰ ﻋﻠﻴﻪ، ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﺇﻥ ﻓﻴﻜﻢ ﻣﻨﺎﻓﻘﻴﻦ ﻓﻤﻦ ﺳﻤﻴﺖ ﻓﻠﻴﻘﻢ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﻗﻢ ﻳﺎ ﻓﻼﻥ ﻗﻢ ﻳﺎ ﻓﻼﻥ ﻗﻢ ﻳﺎ ﻓﻼﻥ ﺣﺘﻰ ﺳﻤﻰ ﺳﺘﺔ ﻭﺛﻼﺛﻴﻦ ﺭﺟﻼً ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﺇﻥ ﻓﻴﻜﻢ ﺃﻭ ﻣﻨﻜﻢ ﻓﺈﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ، ﻗﺎﻝ: ﻓﻤﺮ ﻋﻤﺮ ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻞ ﻣﻤﻦ ﺳﻤﻰ ﻣﻘﻨﻊ ﻗﺪ ﻛﺎﻥ ﻳﻌﺮﻓﻪ ﻗﺎﻝ: ﻣﺎ ﻟﻚ ﻗﺎﻝ: ﻓﺤﺪﺛﻪ ﺑﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝﺍﻟﻠﻪ(ﺹ) ﻓﻘﺎﻝ: ﺑﻌﺪﺍً ﻟﻚ ﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻴﻮﻡ.
“Abi Mas’ud ya ce; …Manzan Allah(saw) ya yi mana khuduba, ya yi godiya ga Allah tare da yabo a gare shi, sannan ya ce: Lallai daga cikinku (Sahabbai) akwai munafikai! duk wanda na kira sunan shi ya mike tsaye!, sai ya ce: kai wane tashi! kai wane tashi! kai wane mike!, har sai da Manzan Allah(saw) ya tayar da mutum 36, sannan ya sake cewa: har yanzu daga cikinku akwai munafikai, ku ji tsoron Allah! (alamun basu kenan ba) mai ruwayar ya ce: sai Umar ya hadu da daya daga cikin wadanda Manzan Allah(saw) ya ce su tashi, ya rufe kansa amma Umar din ya gane shi, sai ya ce da shi: me ya same ka? sai ya ba shi labarin abin da ya faru da su a Masallaci, sai Umar ya ce da shi: Tir da kai! Allah ya nisantar da kai daga rahamarsa”.
(Musnadu Ahmad: Hadisi mai lamba: 21317. Dala’ilun-Nubuwwa na Baihaqi: Hadisi mai lamba: 2030. Al-bidaya wan nihaya na Ibnu kasir: j 5, s 33).
Wannan Hadisi ya tabbatar mana da akwai munafikai da yawa a cikin Sahabbai, kuma ba sukenan wadanda Annabi(saw) tayar ba. Idan suke nan me ya sa Annabi(saw) bayan ya gama taryar da 36; sai kuma ya cewa da Sahabbai kuji tsoron Allah? Sannan me ya sa Umar ya ke da alaka da Munafiki? Da alama lokacin da Annabi(saw) ya tayar da munafikan Umar baya nan? Kenan Umar bai fiye zama tare da Annabi(saw) ba?
Ingantattun Hadisai sun tabbatar mana akwai Sahabban da zasu shiga wutar Jahannamah:
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﻮﻟﻴﺪ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺷﻌﺒﺔ ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﺍﻟﻤﻐﻴﺮﺓ ﺑﻦ ﺍﻟﻨﻌﻤﺎﻥ ﻗﺎﻝ ﺳﻤﻌﺖ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﻋﻦ ﺇﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ(ﺭ) ﻗﺎﻝ ﺧﻄﺐ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ﺹ) ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻧﻜﻢ ﻣﺤﺸﻮﺭﻭﻥ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﻔﺎﺓ ﻋﺮﺍﺓ ﻏﺮﻻ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: “ﻛﻤﺎ ﺑﺪﺃﻧﺎ ﺃﻭﻝ ﺧﻠﻖ ﻧﻌﻴﺪﻩ ﻭﻋﺪﺍ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺇﻧﺎ ﻛﻨﺎ ﻓﺎﻋﻠﻴﻦ” ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮ ﺍﻵﻳﺔ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﺃﻻ ﻭﺇﻥ ﺃﻭﻝ ﺍﻟﺨﻼﺋﻖ ﻳﻜﺴﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ. ﺃﻻ ﻭﺇﻧﻪ ﻳﺠﺎﺀ ﺑﺮﺟﺎﻝ ﻣﻦ ﺃﻣﺘﻲ ﻓﻴﺆﺧﺬ ﺑﻬﻢ ﺫﺍﺕ ﺍﻟﺸﻤﺎﻝ ﻓﺄﻗﻮﻝ ﻳﺎ ﺭﺏ ﺃصحبي! ﻓﻴﻘﺎﻝ ﺇﻧﻚ ﻻ ﺗﺪﺭﻱ ﻣﺎ ﺃﺣﺪﺛﻮﺍ ﺑﻌﺪﻙ ﻓﺄﻗﻮﻝ ﻛﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ “ﻭﻛﻨﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺷﻬﻴﺪﺍ ﻣﺎ ﺩﻣﺖ ﻓﻴﻬﻢ ﻓﻠﻤﺎ ﺗﻮﻓﻴﺘﻨﻲ ﻛﻨﺖ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺮﻗﻴﺐ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﺷﻬﻴﺪ” ﻓﻴﻘﺎﻝ ﺇﻥ ﻫﺆﻻﺀ ﻟﻢ ﻳﺰﺍﻟﻮﺍ ﻣﺮﺗﺪﻳﻦ ﻋﻠﻰ ﺃﻋﻘﺎﺑﻬﻢ ﻣﻨﺬ ﻓﺎﺭﻗﺘﻬﻢ.
“…Manzan Allah(saw) ya yi khuduba ya ce:” ya ku mutane lallai za’a tashe ku a gaban Allah ba takalmi da sutura, ba kaciya, sannan ya karanto fadar Allah(swt): “kamar yanda muka fari halitta haka za mu maida ta, Alkawali ne a kanmu kuma lallai mu masu aikatawa ne”. Sannan ya ce: farkon wanda za’a fara yiwa sutura a ranar Al-kiyama shine Annabi Ibrahim(as). Kuma lallai za’a zo da wasu mazaje daga Al’ummata, sai a bi ta hanyar wuta da su, sai in ce ya rabbi ai wadannan Sahabbaina ne fa! sai a ce da ni ai ba ka san abin da s**a aikata ba a bayanka, sun canza bayan wafatinka. sai in fada kamar yadda Annabi Isa(as) ya fada: “Ni mai shaida ne a kansu matukar ina a cikinsu, amma a lokacinda ka karbi raina to kai ne ka fi kusanci dasu, kuma kai mai shaida ne a kan komai.
(Sahihul Buhari, hadisi mai lamba 6528, da 609, da 4259. Sahihu Muslim, hadisi mai lamba 368, da 4253. Musnadu Ahmad, hadisi mai lamba 7652. Sunan na Ibnu Maja, hadisi mai lamba 3048. Mustadrak na Hakim, hadisi mai lamba 6958).
Sahabi Barra’u bin Azib ya tabbatar da Sahabbai da yawa sun canza (ta hanyar canza wasiyar Annabi(saw) bayan wafatinsa(saw):
ﺣﺪﺛﻨﻲ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺇﺷﻜﺎﺏ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻓﻀﻴﻞ ﻋﻦ ﺍﻟﻌﻼﺀ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﺴﻴﺐ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻗﺎﻝ ﻟﻘﻴﺖ ﺍﻟﺒﺮﺍﺀ ﺑﻦ ﻋﺎﺯﺏ ﻓﻘﻠﺖ ﻃﻮﺑﻰ ﻟﻚ ﺻﺤﺒﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ (ﺹ) ﻭﺑﺎﻳﻌﺘﻪ ﺗﺤﺖ ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎ ﺍﺑﻦ ﺃﺧﻲ ﺇﻧﻚ ﻻ ﺗﺪﺭﻱ ﻣﺎ ﺃﺣﺪﺛﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ.
“Al-Musayyib ya ce na hadu da Barra’u Bin Azib. Sai na ce; ku (Sahabbai) kun dace, kun zauna da Annabi(saw) kuma kun yi masa mubaya’a a karkashin bishiya. Sai Barra’u yayi ajeyar zuciya ya ce; ai baka san abinda mukayi ba a bayan (wafatin Annabi(saw) ba ne!”.
(ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻐﺎﺯﻱ، ﺑﺎﺏ ﻏﺰﻭﺓ ﺍﻟﺤﺪﻳﺒﻴﺔ).
Kenan Sahabbai da yawa; har da wadanda s**a yiwa Annabi Muhammad(saw) mubaya’a a karkashin bishiya (bi’atur-ridwan) sun canza; bayan wafatin Annabi(saw)?
Saboda haka, duk wanda yace kacokaf din Sahabbai yardaddun Allah ne, to ya karyata ayoyin Qur’ani da ingantattun hadisai. Haka ma duk wanda yace; kacokaf dinsu mutanen banza ne, shima ya karyata ayoyin Qur’ani da ingantattun hadisai.
A takaice, wadannan ayoyin da ake kafa hujjar alkawarin Al-Jannah ga dukkan Sahabbai da su; sun sauka ne akan Imam Ali(as) da Sahhaban da s**a lizimce shi; domin shine ruwayoyi ingantattu s**a tabbatar da yayi infaki, yayi jihadi; har ya kashe kaso mai yawa a mafi yawan yakokan da Annabi(saw) yayi, kuma ya rigya dukkan Sahabbai imani, doriya akan cewa; Annabi(saw) ya tabbatar mana da cewa; duk Sahabin da bai son Imam Ali(as) munafiki ne.