16/07/2025
Akwai Darasi A Mutuwãr Buhari Wanda Sai Mai Haɲkali Ne Kaɗai Zai Gane, Cewar Dogonbauchi
Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa na gyara a Najeriya amma an fi ƙarfinsa. (Cabals) sun zagaye shi, azzalumai marasa gaskiya su s**a yi mulkin Najeriya".
Kwamishiniya a hukumar ƙidaya ta ƙasa reshen Jihar Kaduna, Hajiya Sa’adatu Garba Dogonbauchi, ta bayyana takaicinta kan yada wasu suke murna da mutuwar Buhari, a cewarta, "Na yi baƙin cikin yadda mutanenmu ƴan Arewa, Hausawa, musulmai ake ta kaɗe-kaɗe da murna, ko ma me Janar Muhammadu Buhari ya yi bai kamata a saka masa da irin wannan ba". In ji ta.
Dogonbauchi wadda ta bayyana haka ta cikin wata tattaunawarta da Dokin Ƙarfe TV, ta ci gaba da da cewa "Ku tuna cewa Janar Muhammadu Buhari bai satar muku kuɗi ba, ya mutu ba shi da Rijiyar mai, ya mutu gidansa ƙwaya biyu ne rak! Daga Daura sai Kaduna, har ya mutu ba shi da gida a Abuja. Janar Muhammadu Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa na gyara a Najeriya amma an fi ƙarfinsa. (Cabals) sun zagaye shi, azzalumai marasa gaskiya su s**a yi mulkin Najeriya". In ji ta.
A cewar Hajiya Sa’a, "Ya kamata mu sani ɗan’adam tara yake bai cika goma ba. Kuskuren Janar Buhari shi ne da ya ɗauki amana ya ba wa maciya amana saboda kullum suna zuwa masa da fuskar muminai. Ya so ya yi gyara a Najeriya amma maciya amana azzalumai sun bebaye shi. Ga yanayi na rashin lafiya da ya same shi". A cewarta.
Daga nan ta ci gaba da cewa, "Ina jan hankalin ƴan’uwa ƴan Arewa da ƴan Najeriya gaba ɗaya, da mu sani cewa inda Janar Muhammadu Buhari ya je duk ɗinmu za mu je". In ji Dogonbauchi.
Hajiya Sa’a, ta kuma yi kira ga muƙarraban gwamnatin Tinubu da su kiyaye masa amanar da ya ba su domin gudun irin abin da ya faru da Buhari a wannan lokaci. Haka kuma, ta ƙara da yin kira ga ƴan Najeriya da su zamto masu sanya shugabanni cikin addu’a.
Daga ƙarshe kuma, ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalai da ƴan’uwan marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari tare da fatan Allah Ya ji ƙansa Ya gafarta masa. "Buhari Uba ne kuma gwarzo ne da ya bar ɗumbin tarihi". A cewarta.
Me zaku iya cewa?
Dan Allah ku ringa taya mu da sharing zuwa groups.
Sanarwa domin samun ingantattun labarai kuyi following na
ALPU Hausa
AGIBASA-Hausa
ALIB Hausa
Madubin Bauchi
Madubin Arewa
Nigeria Hausa
Madubin-Arewa-TV
ANNUR-Hausa
Madubin Arewa TV
Wakiliyar-Arewa
BDC Hausa
Wakiliyata
AGIBASA-Hausa