25/11/2025
DA DUMI DUMI: Sak**akon ya ta kurawa Yan Bindiga da fallasa Asirinsu Kotun Tarayya ta Yankewa Magajin Ali kwara Hukuncin Zaman gidan yari na Tsawon Shekara 45.
Sai dai Wata ƙungiya mai suna Arewa Youth Ambassadors (AYA) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da kuma hukumomin tsaro da su gaggauta sakin Shehu Musa Aljan, wani jarumi daga Arewa da ya shahara wajen taimaka wa jami’an tsaro yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a yankunan Arewa.
AYA ta bayyana cewa Shehu Musa Aljan ya shafe shekaru yana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro.
Ƙungiyar ta jaddada cewa duk da haɗarin da yake fuskanta, Aljan ya taka rawar gani wajen tarwatsa ƙungiyoyin ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankuna masu fama da tashin hankali.
A watan Disamba 2019, rahoton AYA ya nuna cewa Aljan ya bi sawun wasu ’yan bindiga a hanyar Abuja–Kaduna, inda ya k**a wasu daga cikinsu tare da ceto shanu sama da 1,000 da aka sace a yankin Rijana.
Haka kuma ya kwato mak**ai ciki har da, Bindigogin AK-47, AK-49, da Sauran bindigogi da dama, da kuma Dubunnan harsasai
Rahoton ya kara da cewa ’yan bindigar sun yi ƙoƙarin ba shi Naira Miliyan 2 domin ya barsu su tsallaka gadar Kaduna da shanun, amma ya ƙi amincewa.
Aljan ya sha bayyana adawarsa da tattaunawa da ’yan bindiga, yana mai cewa ba abin yarda ba ne domin ba su da gaskiya ko mutunci
An k**a shi, an gurfanar da shi, daga ƙarshe kuma aka yanke masa hukuncin shekaru 45 a gidan yari.
Me zaku Iya Cewa?