11/11/2025
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 1: *Aymanul Faris
*** Chapter 1&2
Shimfiɗa: Barka da wannan lokaci jama'a, mun dawo bakin aiki. Allah yasa yadda muka
fara rubuta littafin nan, mu gama shi lafiya. Fatan zaku bamu haɗin kai, ta hanƴar yin
liking.
***
****
*Ƙauyen Gazwar na ɗaya daga cikin kauyukan dake cikin jahar Mauzil ta birnin
Damashkar. Gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan ƙauye 'yan wata ƙabila ce da ake
kira banu Kuyuru. Allah ya horewa kabilar Babu Kuyuru gawurtattun sadaukai majiya
karfi, da kuma zaratan jarumai masu dakakkiyar zuciya, baiwar iya yaki da sarrafa
takubba. Adadin mutanen wannan ƙabila ba zai wuce dubu uku ba, kuma Allah yayi su
masu tsananin kyawu ne mazansu da matansu.
Ƙauyen Gazwar na bisa wani ɗan karamin tsibiri ne wanda teku da manyan
duwatsu s**a kewaye, basu da wata sana'a da ta wuce noma da kiwo saboda albarkar
ƙasar da suke da. Kuma wani iko na Allah a shekara suna iya noma abinda mutanen
birnin Damashkar zasu ci gaba dayansu har tsahon wata shekarar, bisa wannan dalili ne
ƙabilar Banu Kuyuru suke samun kudin shiga kwarai da gaske. Shugaban kabilar ya
kasance wani sadaukin mutum mai tsananin adalci da ake kira Hasanul Jalwar bn
Kusuful Jalwar.
Shugaba Hasanul Jalwar ya kasance sadaukin sadaukai kuma jarumin jarumai, don
kaf cikin kabilar Banu Kuyuru babu wani sadauki mai karfin damtse k**ar sa. Haka
kuma ya kasance adali mai son al'ummarsa suma kuma suna tsananin kaunarsa saboda
yadda yake kishinsu da son ci gabansu. Hasanul Jalwar yana da matar aure guda daya
jal, wata kyakkyawar mace wacce ake kira da suna Hajriya. Sai da s**a yi aure da
shekaru bakwai sannan Allah ya albarkace su da samun haihuwa, s**a haifo wani
kyakkyawan jariri wanda s**a kira shi da suna, AYMANUL FARISI.
Aymanul Faris kyakkyawan saurayi ne ɗan kimanin shekaru goma sha tara. Yana da
murɗaɗɗen jiki da tarin ƙwanji. Fatar jikinsa fara ce tas, irin farin da ba kowanne farin
mutum keda kalarsa ba, fari mai bayar da haske. Gashin kansa baƙi ne wuluk, kai kace
rina shi akayi. Idanuwansa ma farare ne tamkar farar madara, da wani ɗigon baƙi tamkar
an ɗiga tawada a cikinsu. Tun Aymanul Faris yana ɗan shekara bakwai shugaba Hasanul
Jalwar ya ke bashi horon yaki, tun yana kuka saboda tsananin wahalar da yake sha, har
ya saba. Lokacin da ya kai shekara goma sha tara sai ya zamo ɗaya daga cikin manyan
zaratan dakarun wannan ƙabila, saboda tsananin jarumtakarsa da juriyarsa. Sau uku
Aymanul Faris yana yin gagarumar jarumtaka wacce take girgiza dukkan wani mahaluƙin
da ke zaune a ƙauyen Gazwar.
A karon farko da ya fara nuna jarumtakarsa shine, lokacin da waɗansu dakarun
sumame s**a kawo mamayar bazato izuwa tsibirin Gazwar bisa jiragen ruwa. Da sassafe
ne kafin rana ta fito, kafin kowa ya tashi daga bacci kawai sai aka jiwo kururuwar
mazaje daga can bayan gari, nan fa kowa ya farka a firgice aka fara iface-iface da guje-
guje saboda tsananin razana. Jarumai s**a fara ɗaura ɗamarar yaki suna tunkarar bayan
gari inda suke jiwo wannar kururuwa, mata da kananun yara kuma s**a fara kulle
ƙofofin gidaje suna buya. Saboda wannan shine karo na farko da aka taɓa kawowa
ƙauyen Gazwar mamayar bazato.
Aymanul Faris na kwance a cikin ɗakinsa bisa gado yana ta sharar bacci kawai sai
yaji iface-ifacen jama'a ya soma cika garin, cikin hanzari ya farka a firgice sannan ya
sauƙo daga kan gado, ya zaro takobinsa dake jikin bango, ya ruga da gudu ya nufi kofar
gida. In banda takalminsa da dogon wandon dake jikinsa babu komai a jikinsa.
Tabbas Aymanul Faris ya kasance jarumi mai murɗaɗɗen jiki da tarin kwanji, gashi
dai yaro ne dan shekara goma sha tara, amma jikinsa ya mummurɗe tamkar wani
tsohon sadauki.
Lokacin da Aymanul Faris da sauran mayaƙan ƙabilar banu Kuyuru s**a iso gaɓar
teku sai s**a hango wadansu girɗa-girɗan sadaukai tsaitsaye a cikin manƴa-manƴan
jiragen ruwa, dauke da muggan mak**an yaki suna ta ihu da kururuwa tamkar zasu ci
babu. Kallo daya mutum zai yiwa sadaukan ya razana saboda tsananin girmansu,
faɗinsu da kuma kaurinsu. Idan kuwa mutum yayi arba da waɗannan zabga-zabgan
mak**an dake hannunsu sai ya saki fitsari a wando saboda tsananin razana. Adadin
'yan fashin zai kai dubu biyar kuma gaba dayansu sanƴe suke da baƙaƙen tufafi, sun
rufe fuskokinsu da wani irin ƙyalle mai launin kore, wani garjejen ƙaton mutum ne mai
ƙirar mutanen farko tsaye a gabansu kai da gani kasan shine shugabansu.
Koda waɗannan 'yan fashi s**a ga dakarun su Aymanul Faris 'yan tsiraru sai s**a
fara bushewa da dariyar mugunta, domin sun tabbatar da cewa sai sun sami nasara
akan su. Ba tare da ɓata lokaci ba aka tuko waɗannan jiragen ruwa na ƴan fashin s**a
zo bakin gaba, 'yan fashi s**a sassauka s**a yi jeru laya-layi suna masujiran umarni.
Garjejen mutumin nan ya ratso ta tsakiyarsu sannan yazo ya tsaya a gabansu, ya
kurawa Aymanul Faris idanu tamkar mai yin nazarin wani abu. Daga bisani kuma ya
kyalkyale da dariya ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Tabbas ku kanku kun san cewa sai
munyi nasara akanku, mene ne dalilin da yasa zaku wahalar da kanku, ku fito domin
gwabza yaki damu alhalin kun san cewa baza kuyi nasara ba?" Aymanul Faris ya daka