Asma'u Abdullai.

Asma'u Abdullai. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Asma'u Abdullai., Grocers, Toro, Bauchi.

Amincin Allah ya tabbata a gareku Abokai na, barkan mu da safiyar jumma'a💐
22/05/2026

Amincin Allah ya tabbata a gareku Abokai na, barkan mu da safiyar jumma'a💐

Daga cikin manyan ni’imomin rayuwa akwai lafiya.Mutum baya gane darajar lafiya sai lokacin da ciwo ya kwantar da shi. Ka...
21/05/2026

Daga cikin manyan ni’imomin rayuwa akwai lafiya.
Mutum baya gane darajar lafiya sai lokacin da ciwo ya kwantar da shi. Ka gode wa Allah a kowace safiya. 🤲

Ni’imar samun iyaye nagari tana daga cikin arzikin duniya.

Ka kyautata musu tun suna raye, domin ranar da s**a tafi hawaye baya dawo da lokaci.
Kwanciyar hankali ta fi dukiya daraja.

Mutane da yawa suna da kuɗi amma babu farin ciki a zuciya.

Aboki na gari ni’ima ne.
Domin yana tunasar da kai Allah lokacin da ka manta, kuma yana tsayawa tare da kai lokacin ƙunci.

Duk ranar da ka wayi gari kana numfashi, to Allah ya sake baka wata dama.

Kada ka ɓata ta cikin saɓo da cutarwa.
Ni’imar sutura da abinci abu ne da ya kamata mu riƙa godewa Allah akai.

Wasu suna kwana da yunwa alhali kai kana cikin walwala.

Ilimi ni’ima ce mai ɗaukaka mutum.
Da ilimi ne mutum ke gane gaskiya da ƙarya.
Zaman lafiya a ƙasa ni’ima ce babba.

Idan babu tsaro, babu walwala, babu cigaba.
Ka daina kallon abin da baka da shi kawai.

Ka tuna akwai mutane da yawa suna mafarkin irin rayuwar da kake ciki yanzu.
Babbar ni’ima ita ce shiriya.

Domin dukiyar duniya tana ƙarewa, amma shiriya tana kai mutum Aljannah. 🤍.

Alhamdulillah: ko Gobe ayi sallah. 🥱
20/05/2026

Alhamdulillah: ko Gobe ayi sallah. 🥱

✨ MUHIMMANCIN ADDU’O’I A RAYUWAR MU ✨Rayuwa ba ta tafiya da ƙarfi ko dabara kaɗai… tana tafiya ne da tsari, tarbiyya, da...
19/05/2026

✨ MUHIMMANCIN ADDU’O’I A RAYUWAR MU ✨
Rayuwa ba ta tafiya da ƙarfi ko dabara kaɗai… tana tafiya ne da tsari, tarbiyya, da addu’a. Mutum mai tsari a rayuwa yana samun nutsuwa, kuma mai kyakkyawar tarbiyya yana samun daraja a idon jama’a. Amma duk wannan ba ya cika sai da addu’a.
Adddu’a ita ce sirrin nasara. Ita ce hanyar da bawa ke magana da Ubangijinsa cikin ladabi da tawali’u. Duk wanda ya saba da addu’a, to yana gina rayuwarsa ne a hankali, yana gyara zuciyarsa, yana kuma samun shiriya a dukkan al’amuransa.

Ya Allah, Ka gyara mana zukatanmu, Ka sanya mu cikin masu tsari a rayuwarmu, masu gaskiya a maganarmu, masu tsoronKa a dukkan al’amuranmu.
Ya Allah, Ka tsarkake mana zuciyarmu daga hassada da ƙiyayya, Ka cika ta da soyayya da rahama. Ka sa mu zama abin koyi ga al’umma, Ka ba mu tarbiyya mai kyau da hali nagari.
Ya Allah, Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, Ka kare mu daga ɓata, Ka ba mu ikon yin abin da Ya dace a kowanne lokaci. Ka sanya rayuwarmu ta zama mai albarka, Ka kuma sa mu mutu muna cikin imani.
Ya Allah, duk wanda ya karanta wannan rubutu, Ka sauƙaƙa masa damuwarsa, Ka buɗe masa ƙofofin alheri, Ka cika masa burinsa na alheri, Ka azurta shi da farin ciki da kwanciyar hankali.
Amin Ya Rabbal Alamin 🤍

Assalamu Alaikum barkan mu da safiyar jumma'a Yan uwana, Ina Yi Muku fatan Alheri.
15/05/2026

Assalamu Alaikum barkan mu da safiyar jumma'a Yan uwana, Ina Yi Muku fatan Alheri.

12/05/2026

💞💞💞

barkan ku da Rana abokai, ubangiji Allah ya haɗa fuskokin mu acikin gidan Al-jannah 🤲
12/05/2026

barkan ku da Rana abokai,

ubangiji Allah ya haɗa fuskokin mu acikin gidan Al-jannah 🤲

YAWAN ZARGI YANA LALATA ZAMAN TAKEWAZaman takewa yana buƙatar soyayya, amana, fahimtar juna, da kwanciyar hankali. Duk i...
08/05/2026

YAWAN ZARGI YANA LALATA ZAMAN TAKEWA

Zaman takewa yana buƙatar soyayya, amana, fahimtar juna, da kwanciyar hankali. Duk inda waɗannan abubuwa suke, gida ko alaƙa tana samun daɗi da ɗorewa. Amma akwai wani abu da yake shiga a hankali ya rushe zaman takewa ba tare da an lura ba, shi ne yawan zargi.

Zargi yana farawa ne da ƙaramin tunani mara tushe. Mutum ya fara ɗaukar zato a matsayin gaskiya, sai ya gina fushi da damuwa a kai. Daga nan sai ya fara kallon abokin zama da ido na shakku, duk abin da ya yi sai ya fassara shi da mummunar manufa.

A tsakanin ma’aurata ko masoya, yawan zargi yana kashe amana. Idan mace ko namiji kullum yana cikin bincike, tambayoyi marasa iyaka, da zaton cin amana ba tare da hujja ba, zuciyar ɗayan za ta gaji. Domin babu wanda yake jin daɗin rayuwa a inda ake kallonsa kamar mai laifi a kowane lokaci.

Haka kuma, zargi yana haifar da yawan faɗa da rashin natsuwa. Abin da bai kamata ya zama matsala ba, sai ya zama babban rikici. Kalma kaɗan ta rikide zuwa sabani, saboda an riga an cika zuciya da shakku.

Yawan zargi kuma yana iya sa mutum ya rasa gaskiyar da yake da ita. Wani lokaci mutum yana zargin wanda bai yi laifi ba, har ya sa shi jin takaici ko gajiya. Daga ƙarshe sai kyakkyawar alaƙa ta lalace saboda abin da bai taɓa faruwa ba.

Maganin wannan matsala shi ne gaskiya da tattaunawa. Idan akwai abin da ya dame ka, ka yi magana cikin natsuwa maimakon gina zato a zuciya. Haka kuma a koya yarda da juna, domin amana ita ce tubalin zaman lafiya.

A ƙarshe, duk wanda yake son zaman takewa mai daɗi, ya guji yawan zargi. Domin inda zargi ya yi yawa, farin ciki yana raguwa, soyayya tana sanyi, zuciya kuma tana gajiya.

Rayuwa ta fi daɗi idan aka gina ta a kan yarda, ba a kan zato ba.
copied ✍️

Allahumma salli wa sallim ala nabiyina Muhammad (ﷺ)🫀❤️‍🩹🌷🩵
08/05/2026

Allahumma salli wa sallim ala nabiyina Muhammad (ﷺ)🫀❤️‍🩹🌷🩵

Assalamu alaikum: Alhamdulillah yanzu kam na samu lafiya, Nagode da Addu'o'inku, ubangiji Allah ya sakawa kowa da Al-kha...
07/05/2026

Assalamu alaikum:
Alhamdulillah yanzu kam na samu lafiya, Nagode da Addu'o'inku, ubangiji Allah ya sakawa kowa da Al-khairi, ya kuma haɗa fuskokin mu acikin gidan Al-jannah 🤲

ina bukatar addu'ar ku abokai
06/05/2026

ina bukatar addu'ar ku abokai

Address

Toro
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Asma'u Abdullai. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category