Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka

Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka, Grocers, Bauchi.

‎Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya kaddamar da aikin gina kasuwanni na zamani a Chikin Garin Bau...
18/02/2026

‎Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya kaddamar da aikin gina kasuwanni na zamani a Chikin Garin Bauchi.

‎A yayin jawabin kaddamarwar, Gwamna Mohammed ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin sa na bunkasa harkokin kasuwanci, karfafa kananan 'yan kasuwa, da kuma habaka tattalin arziki a jihar.

‎Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa na dagewa wajen sauya tsarin birane, samar da ayyukan yi, da kuma kirkirar yanayi mai sauki ga kananan da matsakaitan masana’antu.

‎Ya kara da cewa, kasuwannin da za a gina za su kasance masu kyau a tsarin gine-gine, cikakke da dukkan abubuwan more rayuwa da s**a dace, tare da tsaro, saukin shiga, da jin dadin masu saye da masu sayarwa.

‎Kasuwannin da aka tsara gina sun hada da:

‎* Kasuwar Fanteka
‎* Kasuwar Gwari
‎* Kasuwar Furnitures
‎* Sabuwar Kasuwar Wunti
‎* Kasuwar Hatsi da Magunguna

‎Shuwagani Kasuwani Sasai daban daban Sun samu Halarta Wanda Shugaban Hadakan Yan Kasuwa da Masu Sana'ar Hanu Hon. Abdullah Caps ya jagoran cesu.

SANARWA TA MUSAMMAN KADDAMAR DA SABBIN KASUWANNI ZAMANI GUDA BIYAR. A KARAMAR HUKUMAR BAUCHI Gobe Laraba, 18/02/2026, Ma...
17/02/2026

SANARWA TA MUSAMMAN KADDAMAR DA SABBIN KASUWANNI ZAMANI GUDA BIYAR. A KARAMAR HUKUMAR BAUCHI

Gobe Laraba, 18/02/2026, Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi), zai kaddamar da sabuwar kasuwa ta zamani da ta kunshi muhimman sassa kamar haka:

1 Sabuwar Kasuwan ’Yan Gwari

2 Kasuwan ’Yan Bola Jari

3 Kasuwan ’Yan Furniture

4 Kasuwar New Wunti Market

5 Masu Maganin Gargajiya da ’Yan Shinkafa

Za a gudanar da gagarumin taron ne a Filin New Market, kan sabuwar hanyar Ibrahim Bako Tirwun, a birnin Bauchi.

Lokaci: Karfe 10:00 na safe.

Sanarwa daga Shugaban Gamayyar Kungiyoyin ’Yan Kasuwa na Kasa reshen Jihar Bauchi, Alh. Abdallah Caps.

Shugaban Hadakan Yan Kasuwa Na Jiha da Na Karamar Hukuma sun Halarce Rantsar da Shugabanni Yan Kasuwa Na Dr. Sulaiman Ad...
10/02/2026

Shugaban Hadakan Yan Kasuwa Na Jiha da Na Karamar Hukuma sun Halarce Rantsar da Shugabanni Yan Kasuwa Na Dr. Sulaiman Adamu Market dake Central Market Bauchi.

Shugaban Hadakan ‘Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu na Jihar Bauchi, Hon. Abdullahi Caps, tare da Shugaban Hadakan ‘Yan Kasuwa na Karamar Hukumar Bauchi, Hon. Adamu Yahaya, sun halarci taro Shaida bikin rantsar da shugabannin ‘yan kasuwa na Kasuwar Dr. Sulaiman Adamu.

‎Bikin rantsarwar ya gudana cikin kwanciyar hankali da nasara, inda aka rantsar da sabbin shugabannin kasuwar Dr. Sulaiman Adamu a gaban manyan baki da ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban. Hakan ya nuna karfin hadin kai da jajircewar ‘yan kasuwa wajen tafiyar da harkokin kasuwanci bisa doka da gaskiya.

‎A jawabinsu, shugabannin Hadakan ‘Yan Kasuwa na Jiha da na Karamar Hukumar Bauchi sun taya sabbin shugabannin kasuwar murna, tare da jan hankalinsu da su rike amanar da aka dora musu, su tabbatar da adalci, hadin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan kasuwa. Haka kuma sun bukaci ‘yan kasuwar Dr. Sulaiman Adamu da su bai wa shugabanninsu cikakken hadin kai domin samun cigaba mai dorewa.

Sadiq Baba ✍️
10/February/2026.

‎An Rantsar da ’Yan Kasuwa na Sabuwar Kasuwa (Tudun Alkali Railway Road)‎‎An rantsar da shugabanni yan kasuwa na Sabuwar...
08/02/2026

‎An Rantsar da ’Yan Kasuwa na Sabuwar Kasuwa (Tudun Alkali Railway Road)

‎An rantsar da shugabanni yan kasuwa na Sabuwar Kasuwa da ke (Tudun Alkali Railway Road), an Gudanar da biki Rantsuwan Wanda ya samu halartar manyan shugabanni na kungiyoyin ’yan kasuwa.

‎Taron rantsarwar ya samu halartar Shugaban Haɗaƙan ’Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu na Jihar Bauchi, Hon. Abdallah Caps, tare da takwaransa na Karamar Hukumar Bauchi, Hon. Adamu Yahaya, inda s**a nuna goyon baya da farin ciki kan nasarar rantsar da sabbin shugabannin kasuwar.

‎Shugabannin sun jaddada muhimmancin haɗin kai, gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da harkokin kasuwa, tare da kira ga sabbin shugabannin da su yi aiki domin cigaban kasuwar da walwalar ’yan kasuwa baki ɗaya.

‎Sadiq Baba✍️.
08/February/2026.

Shugaban Gamaiyan Kungiyar ’Yan Kasuwa Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwa (Chiroma)Shugaban Gamaiyan Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu...
20/01/2026

Shugaban Gamaiyan Kungiyar ’Yan Kasuwa Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwa (Chiroma)

Shugaban Gamaiyan Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu ta Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Hon. Abdullah Caps, ya jagoranci mambobin ƙungiyar domin mika ta’aziyyar rasuwa ga iyalan marigayi Malam Yakubu (Chiroma).

Ziyarar ta’aziyyar ta gudana ne domin jajanta wa iyalan marigayin bisa wannan babban rashi da s**a yi, tare da addu’ar Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma bai wa iyalansa da al’umma gaba ɗaya haƙurin jure wannan jarrabawa.

Hon. Caps ya bayyana marigayi Malam Yakubu (Chiroma) a matsayin mutum nagari wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban al’umma, musamman a fagen kasuwanci da zaman lafiya. Ya kuma yi kira ga mambobin ƙungiyar da jama’a da su ci gaba da yin addu’a ga mamatan Musulmi a ko da yaushe.

SADIQ BABA ✍️.
20/January/2026.

20/01/2026
Ƙungiyar Haɗakar Yan Kasuwa ta Ƙaramar Hukumar Bauchi ta Kai Ziyarar ga Shugaban Jam’iyyar PDP.Ƙungiyar Haɗakar Yan Kasu...
15/01/2026

Ƙungiyar Haɗakar Yan Kasuwa ta Ƙaramar Hukumar Bauchi ta Kai Ziyarar ga Shugaban Jam’iyyar PDP.

Ƙungiyar Haɗakar Yan Kasuwa da Masu Sana’o’in Hannu ta Ƙaramar Hukumar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin shugabanta Hon. Adamu Yahaya, ta kai ziyarar ga Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙaramar Hukumar Bauchi, Hon. Durbin Inki.

Shugaban ƙungiyar ya jagoranci mambobin ƙungiyar ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar, inda s**a gana da shugaban jam’iyyar domin tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi cigaban kasuwanci, haɗin kai, da kuma bunƙasar tattalin arzikin al’umma.

Ziyarar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna da fatan ƙara haɗin gwiwa tsakanin ’yan kasuwa da jam’iyyar domin ci gaban Ƙaramar Hukumar Bauchi baki ɗaya.

SADIQ BABA ✍️
15/January/2025.

14/01/2026

Traders And Artisan Multipurpose Cooperative Union (HADAKA)🤝.

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category