MAI-naira nig.limited

MAI-naira nig.limited Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MAI-naira nig.limited, Grocers, No 131 Dorayi emir Road kano by zage behind murtala muhammaed special hospital, Dorayi Babba.

15/01/2026
Na gabatar da sabuwar hular Kwankwasiyya mai tambarin beran dinka.
23/09/2025

Na gabatar da sabuwar hular Kwankwasiyya mai tambarin beran dinka.

14/08/2025

Oribebe

Akwai kayan bokanci na sayarwa harda yar budurwar aljana idan akwai Mai buƙataBokan dayake aiki dasune yakoma yin ADAIDA...
14/08/2025

Akwai kayan bokanci na sayarwa harda yar budurwar aljana idan akwai Mai buƙata
Bokan dayake aiki dasune yakoma yin ADAIDAITA SAHU
😂😂😂😂

14/08/2025

Dan uban ƴan Kwankwasiyyar gobe Juma'a zan taho da tawaga ta mu kwana a Shanono, idan Abba da mataimakinsa ko jagora sun isa mu haɗu a Shanono gobe Juma'a can zan kwana zamu tafka rashin mutunci ga duk wanda ya yi yunƙurin ƙwace mana zaɓe, saboda dole sai mun ci zaɓen nan koda tsiya koda tsiya-tsiya, ranar zaɓe kada Allah ya kiyaye, ƴan jam'iya ku zagi uban kowa ku ke da sama—Abdullahi Abbas Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.

A taron FEC na jiya, Shugaba Tinubu ya sake bada approvals din aiki a Lagos na gyaran gadoji guda biyu, Third Mainland B...
14/08/2025

A taron FEC na jiya, Shugaba Tinubu ya sake bada approvals din aiki a Lagos na gyaran gadoji guda biyu, Third Mainland Bridge akan kudi N3.6Trillion, da kuma gyaran gadar Carter ita kuma akan kudi N360Billion, idan ka hada su jimilla ya k**a kusan N4Trillion. Idan ka tara wannan tiriliyoyin akan lissafin N7Trillion da nai a baya na aiyukan da aka kai jihar Lagos, kenan a cikin shekaru biyun gwamnatin Tinubu an tura kudi a kalla N11Trillion. Wato TIRILIYAN GOMA SHA DAYA KENAN!

A sanda nai rubutin farko, an samu yan arewa da suke cikin gwamnatin Tinubu sun min raddi kala kala, cewa Tinubu na aiki a Arewa. Sun lissafo min aiyukan da kusan karashen na gwamnatin Buhari ne, a matsayin aiyukan Tinubu a Arewa, ciki harda titin Kano zuwa Hadejia, wanda ni hanyar gida na ce, kuma na san kiris ne ya rage, a karasa shi lokacin Gwamnati Buhari, amma dan rinto, an hada a cikin jeran aiyukan arewa da Tinubu yayi.

Tambaya ta ga yan Arewa dake cikin gwamnatin Tinubu shine, da karashen aikin Buhari da ake rinto da shi, da kuma aiyukan da ake daure mu da igiyar zato cewa za ayi su nan gaba, shin jimmillar su gaba daya a jihohin Arewa 19, kudin su ya kai N11Trillion? Idan kun ce ya kai, toh dan Allah ku lissafo min su.

Wato dan kana cikin gwamnati ba lasisi bane na ka kyale a cuci al'ummar ka. Idan ka ga ba daidai ba, toh ko ba za ka iya magana ba, ya k**ata ka kauda kai, ka kyale wanda za su iya su yi domin a gyara, wani zubin gwamnati sai da s**a.

Ba na mantawa lokacin Obasanjo, da sahalewar yan Arewan da ke cikin mulki, aka saka hannu a dokar 13% derivation, wanda hakan ta sa har yau, ake kwashe kaso sha uku, na ribar arzikin man kasa, ana bawa jihohin da suke da arzikin mai. Ban ce kar a basu ba, amma kowa ya san duk duniya ba inda ake bada kaso 13% sai a Najeriya.

Idan ba muyi wa tufkar hanci ba tun yanzu, ban san ya zata kasance ba Idan Tinubu ya zarce har tsahon shekara 8 yana mulki. Ba mamaki idan dan Arewa zai je Lagos sai yayi Visa! Ko mu hadu mu taka musu birki, ko su take mu har illa masha Allah!

Salihu Tanko Yakasai
Dawisun Kanawa
August 14, 2025.

14/08/2025

Sakon Dansarki ga yan kwankwasiyya
Mai zaku ce?

Address

No 131 Dorayi Emir Road Kano By Zage Behind Murtala Muhammaed Special Hospital
Dorayi Babba

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MAI-naira nig.limited posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category