labaran yau da kuluma

labaran yau da kuluma safin da zaku riqa samun labarann da ke faruwa a sassan duniya

YANZU-YANZU: Shugaban Kasar IRAN Ya Sauka a Doha Babban birnin Qatar don halartar wani taron gaggawa na shugabannin kasa...
15/09/2025

YANZU-YANZU: Shugaban Kasar IRAN Ya Sauka a Doha Babban birnin Qatar don halartar wani taron gaggawa na shugabannin kasashen Musulmi da Larabawa, wanda aka shirya don tattauna harin da Isra’ila ta kai kan Qatar.

Kasashe 50 Zuwa 57 Ake Saran Zasu Halarci Wannan Taron Da Za a Gudanar Yau Litinin. Babban manufarsa ta zuwa taron Shi ne kare matsayin Iran da nuna goyon baya ga Qatar kan wannan harin na Ise-ra-ila.

Da kuma Ankarar da Shugabannin kasashen Musulmai su ɗauki matakai na haɗin kai da kuma tsayawa kai da fata wajen adawa da irin waɗannan hare-hare. Yace lokaci ya yi da magana ba ta wadatar wa, Sai anyi aiki wajen kare hakkokin ƙasashen musulmi.

"Wallahi mu Fulani mun fi Hausawa imani" Inji dan bindiga Malam Isiya yayin sasanci a karamar hukumar FaskariDaga cikin ...
14/09/2025

"Wallahi mu Fulani mun fi Hausawa imani" Inji dan bindiga Malam Isiya yayin sasanci a karamar hukumar Faskari

Daga cikin dalilan da ya fada ya ce, "idan s**a muka yi fada da Hausawa, in s**a k**a mutanenmu kashe su suke yi, mu kuma idan mun k**a dan imani sai mu sako su" Inji Malam Isiya Akwashi Garwa jigon yan bindiga na yankin Bakori

Shugabannin Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi su ne ke neman tayar da rikici a duniya - Firaministan QatarƘarin bayani - ...
12/09/2025

Shugabannin Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi su ne ke neman tayar da rikici a duniya - Firaministan Qatar

Ƙarin bayani - https://bbc.in/42mNjFl

Haɗakar hammayar ADC a Najeriya ta tabbatar da naɗin Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata David Mark a matsa...
02/07/2025

Haɗakar hammayar ADC a Najeriya ta tabbatar da naɗin Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata David Mark a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.

Sanata David Mark, ya bayyana cewa ƙawancen ADC, haɗaka ce da ta shafe watanni ana tattaunawa domin samar da ita.

Ya ambato manyan matslolin tsaron da ke addabar jahohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Borno da Yobe da sauran su, da cewa duk wani da ya damu da halin da ake ciki mai alaƙa da hakan, ya amince da shiga wannan haɗaka tasu.

Ya ce duk waɗanda s**a hallara a taron da zuciya ɗaya s**a amince da dunƙulewar.

Hamshaƙin attajirin kuma ɗaya daga cikin mutum mafi arziki a nahiyar Afrika, ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan ...
28/06/2025

Hamshaƙin attajirin kuma ɗaya daga cikin mutum mafi arziki a nahiyar Afrika, ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da rashin lafiya k**ar yadda ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya shaida wa BBC.

Ya rasu yana da shekaru 94, ya kuma bar matansa da ƴaƴa da jikoki da dama.

Donald Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya ba tare da sharuɗa ba, yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta, yana mai j...
17/06/2025

Donald Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya ba tare da sharuɗa ba, yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta, yana mai jadadda cewa ana neman kure haƙurinsa.

A wani sakon mai tsayi da ya wallafa a shafinsa Social Truth, Mista Trump ya yi gargaɗin cewa kai wa ga jagoran addinin Iran, Ali Khamenei ba abu ne mai wahala ba, amma dai Amurka ba za ta kashe shi ba, a yanzu.

Jawaban shugaban na zuwa ne gabanni tattaunawa da kwamitin tsaro na Amurka.

Ana dai ci gaba da yaɗa jita-jitar cewa Amurka na shirin shiga wannan yaƙi

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya ƙi amincewa da yunƙurin Isra'ila na kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Kham...
17/06/2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya ƙi amincewa da yunƙurin Isra'ila na kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a yaƙin da take yi da Iran, lamarin da kafofin watsa labaran Amurka s**a ruwaito yana cewa "bai dace ba."

Bayan burin da Isra'ila ke da shi na tarwatsa abin da take kira babbar barazanar da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya ke yi ga ƙasarta a matsayin dalilin hare-haren na yanzu, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyanhu, ya ce kawo sauyin gwamnati a Iran ma na cikin burinsu.

Netanyahu ya sha faɗa a baya cewa akwai buƙatar ƴan ƙasar su tashi tsaye wajen ƙwatar ƴancinsu daga jagoran.

A wannan maƙalar, za mu yi nazarin wane ne jagoran addinin, da irin ƙarfin ikonsa a ƙasar, da kuma rawar da iyalansa suke takawa a siyasar ƙasar.

Hotuna daga taron yiwa ƙasa addu'a, wanda Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta shirya yau a a'a filin Arafah.Allah ya kar...
05/06/2025

Hotuna daga taron yiwa ƙasa addu'a, wanda Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta shirya yau a a'a filin Arafah.

Allah ya karba, yasa ayi Hajji Mabrur!!

Hukumomin Saudiyya sun yi nanata cewa sun ɗauki matakai domin rage wa mahajjata wahalhalu na zafin rana a Hajjin bana ya...
05/06/2025

Hukumomin Saudiyya sun yi nanata cewa sun ɗauki matakai domin rage wa mahajjata wahalhalu na zafin rana a Hajjin bana yayin da ake tsammanin zafin zai ci gaba da ƙaruwa.

A shekarar da gabata, mutum 1,300 ne s**a mutu yayin aikin akasari saboda zafin mai tsanani a birnin Makkah.

An shuka dubban binshiyoyi da kuma kakkafa ɗaruruwan na'urorin sanyaya wuri domin rage ɗumin da aka yi hasashen zai kai 44C a ma'auni.

Sun kuma hana yara 'yan ƙasa da shekara 12 yin aikin ibadar. Kazalika, sun jibga tara da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka k**a yana yunƙurin shiga Makkah ba tare da cikakken izini ba.

Zuwa ranar Lahadi, hukumomi sun ce sun hana mutane fiye da 269,000 shiga birnin na Makkah, wanda shi ne mafi tsarki a addinin Musulunci.

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) sun yi barazanar tsunduma ya...
05/06/2025

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) sun yi barazanar tsunduma yajin aiki saboda abin da s**a ce rashin biya musu buƙatunsu.

Kamfanin na AEDC na samar wa Abuja babban birnin Najeriya wuta, da kuma jihohin Nasarawa da Kogi da Neja masu maƙwabtaka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata wasiƙa da ƙungiyoyin ma'aikatan biyu s**a aike wa mahukuntan kamfanin domin sanar da su aniyarsu, suna masu cewa "yajin aikin zai iya farawa a kowane lokaci".

"Ku tuna cewa mun ƙulla yarjejeniya da ku a ranar 27 ga watan Satumban 2024 domin jingine yajin aiki game da rikicin kasuwanci da s**a shafi ma'aikata," k**ar yadda jaridar ta ambato wasiƙar na bayyanawa.

"Muna tunasar da ku matsalar ƙin biyan fanshonmu da aka cire mana tsawon wata 16, da ƙin fara biyanmu sabon mafi ƙarancin albashi, da ƙin ƙara wa ma'aikata matsayi tsawon shekara 10, da ƙin tabbatar da ma'aikata na wucin gadi a matsayin cikakku."

Dalilan da ke janyo rashin tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya

Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki?

Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa):A irin wannan ranar ce ( 9 ga wat...
05/06/2025

Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa):

A irin wannan ranar ce ( 9 ga watan Zul-Hijjah ) SHEKARA ta goma bayan Hijira a Dutsen Arafat (ranar Arfa kenan) Annabi Muhammad S.A.W ya yi wata huduba mai ratsa zuciya.

Fiyayyen Halitta (S.A.W) Ya fara da cewa:

“Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a wannan wuri a yau.

1⃣

Ya ku mutane k**ar yadda ku ka ri'ki wannan wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa mutane kayan da s**a ba ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku.

2⃣

Ku tuna fa, hakika Allah zai yi sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin
da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi. Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.

3⃣

Ya ku jama'a hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma su ma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su,
Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci zina.

4⃣

Ya ku jama'a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah (SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka. Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi.

5⃣

Ku sani fa, kowane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da aikata kyawawan ayyukka.

6⃣

Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban Ubangijinku, domin sak**ak

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kakka...
29/05/2025

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kakkausar murya, yana mai cewa cikin shekara biyu kacal, gwamnatin ta nuna gazawa, kuma gwamnati ce wadda ba ta tare da jama'a sannan maras jin tausayin talakawa fiye da kowacce gwamnati tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana cewa jam'iyyar adawa ba za ta yi shiru ba yayin da halin rayuwa ke ƙara tsananta ga ‘yan kasa tare da yawaitar almubazzaranci daga bangaren gwamnati.

Atiku ya ce babu wata gwamnati da ta taɓa jefa al’umma cikin irin wannan ƙunci ba tare da la’akari da gaskiya da rikon amana da jagoranci nagari ba.

“Wannan gwamnati ta Tinubu ba wai kawai ta ƙara talauci a fadin ƙasar ba ne, har ma ta kafa sabbin tarihi wajen almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a.”

Ya ƙara da cewa a daidai lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, jami’an gwamnati suna rayuwa cikin walwala da amincewa da kasafin kuɗi da ke amfana kawai ga attajirai yayin da talakawa ke ci gaba da shan wahala.

“Abin taƙaici ne yadda Najeriya ba wai kawai ta kasance ƙasa da ke fama da matsanacin talauci a duniya ba, yanzu haka ta zama ƙasar da ke da yawan yara masu fama da rashin abinci fiye da kowacce ƙasa a Afirka, hatta fiye da Sudan — ƙasar da ke fama da yaƙi.” in ji Atiku.

Ya ce bisa rahoton Global Hunger Index na 2024, Najeriya na daga cikin ƙasashen da s**a fi fama da yunwa da rashin abinci, inda take matsayi na 18 a duniya.

Ya ƙara da cewa duk wani tsarin gwamnati da aka ɗauka a ƙarƙashin wannan mulki ya fi cutar da talakawa fiye da komai, yayin da masu kuɗi ke ci gaba da morewa.

Atiku ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yawan bashin da gwamnatin ke ci gaba da karɓa.

"A lokacin da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, jimillar bashin ƙasar ya tsaya kan naira tiriliyan 49. Amma cikin shekaru biyu kacal da fara mulki, ya karu zuwa tiriliyan 144 yayin da kuma ake shirin karɓar

Address

Katsina Funtua
Funtua
100001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when labaran yau da kuluma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category