03/05/2026
Rayuwa tana da gaskiya guda ɗaya: Kai kaɗai ne za ka iya samo wa kanka mafita.
Duk wanda ka gani ya zama wani abin koyi a yau, ba haka kawai ya tashi ya samu ba.
Ya sha gwagwarmaya, ya yi tunani mai zurfi, ya yi aiki tukuru, ya hana idanunsa barci, ya ɗaura wa jikinsa wahala domin cimma burinsa.
Wasu ma sun shiga haɗari da kasada domin su kubuta daga tsananin wahalar rayuwa.
Kada ka zauna kana jiran wani ya canza maka rayuwa.
Tashi ka fara daga inda kake, da abin da kake da shi.
Domin mafi girman canji yana farawa ne daga ranar da ka yanke shawarar cewa:
"Ba zan ci gaba da zama haka ba."