15/04/2026
Atiku: Idan aka zaɓe ni, zan mayar da mulkin karɓa-karɓa cikin kundin tsarin mulki
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce zai nemi yin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa tsarin mulkin karɓa-karɓa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Da yake magana a ranar Laraba yayin wata hira a shirin Prime Time na tashar Arise Television, Abubakar ya ce yana goyon bayan tsarin raba mulki (zoning), yana mai cewa idan aka sanya shi a kundin tsarin mulki zai samar da tsari mafi adalci da kuma kwanciyar hankali wajen karɓa-karɓar mulki.
“Idan na zama shugaban ƙasa, ko da gyara guda ɗaya ne kawai zan iya yi, zan yi aiki domin hakan,” in ji shi.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa Peoples Democratic Party (PDP) ita ce kaɗai jam’iyyar siyasa da ke da tsarin raba mulki a rubuce cikin kundin tsarin mulkinta
fatan nasara babanmu Limami nagarchechchen jagora wan da shikadai ne xe iya karawa da makiyan talakawan Nigeria
wato gamnatyn APC akasar Nan yakuma mumatawa jam Iyar ADC baya Dan tin karar axxalumar gomnaty a Nigeria
yakuma kamaya muhada Kai don ganin atiku abubakar (waxirin Adamawa) yasamu nasara a 2027 in Allah yakai mu
atiku yanada kyakykyawan manufa domin chigaban Nigeria da Al ummah ta