17/04/2026
SALATIN ANNABI…..
-Manzon Allah SAW ya ce: "Ku yawaita salati a gareni a daren Juma'a da ranar Juma'a, wanda yayi salati daya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi.
-Kuma ma wani qarin daraja da daukaka shine, duk wanda ya lizimci yawaita salati ga Manzon Allah damuwanshi da bakinciki za su gushe, farin ciki da kwanciyar hankali za su kusance shi.
-Yana daga cikin mafi soyuwan mutane ya kasance mai biyayya gare shi, kuma son Annabi wajibi ne a kan kowane Musulmi mai tauhidi. Kuma yana daga cikin son sa (S A W) yi masa salati da yi masa haƙiƙanin biyayya.
-Kuma yana daga cikin haƙiƙanin yi wa Annabi (S A W) salati to ya zama kana koyi da Manzon Allah a cikin komai.
-Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; “Marowaci shi ne wanda aka ambace ni yaji amma bai yi mini salati ba.
-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce, Allah yana da waɗansu Mala’iku a bayan qasa, suna isar mini da sallama daga al’ummata.
-Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa”.
‘Yan uwa masu Albarka muna gayyatarku zuwa ga taska wadda rahamar ta ba ta qarewa, taska wadda babu asara da tabewa acikinta, taska wadda take bude kofofin alkairi take kuma kulle kofofin sharri, taskar da duk wanda ya k**a sai ya tsira duniya da lahira, domin acikinta akwai gyaran zuciya idan zuciya ta gyaru jiki da aiki zasu tsarkaka, wanan taska ita ce koyi da Manzon Allah da yawaita yi masa salati acikin halin farin ciki da halin damuwa. Hakika Allah baya kunyatar da wanda yake koyi da Annabi kuma yake masa salati.
اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ. اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.