09/08/2025
Babu wanda ya ke da kokwanto kan cewa makarantu, asibitoci, ruwan famfo, lantarki da kamfanin sadarwa na gwamnati duka ba su da kyau a Najeriya. Daga Kansila na mazaɓa zuwa shugaban ƙasa; daga leburori zuwa Ɗangote; daga kan malamin Firamare zuwa Farfesa a Jami'a, duk wanda ya samu dama a cikin waɗannan ba ya yadda ya je asibitin gwamnati, ko ya kai yaransa makarantar gwamnati, ko ya ke maleji da ruwan famfo da lantarkin da gwamnati ta ke rabawa. Borehole da solar a ke amfani da su a duk gidajen masu wannan iko; makarantu masu zaman kansu da asibitocin ƴan kasuwa a ke aika yara. Akwai misalai barkatai, k**a daga kan tsohon shugaban ƙasa da ya rasu a London Clinic cikin watan da ya gabata zuwa ƙasa.
Ba sabon abu ba ne a je asibiti babu Likita, ko babu gadon da za a kwantar da mara lafiya, ko babu sirinjin da za a yi allura zuwa duk wani abun buƙata, k**ar yanda Hajiya A'isha Buhari ta taɓa shiga asibitin Villa kuma ta tarar babu sirinji da ruwan allurar Malaria, duk da cewa a lokacin an fitar da kusan billion 30 don gyaran wannan asibitin na Villa. Kamar haka, kullum talakawa suke mutuwa kafin a kai su asibitin, ko in an samu sun je a kan lokaci, amma ƙarancin ma'aikata, ko sakaci, ko rashin kayan aiki ko kuma cuwa-cuwar ƙananan ma'aikata ta kashe su!
Wannan ya sa ni ban ga wani abun tayar da jijiyar wuya ba in an ce akwai sakaci a cikin rasuwar marigayi Sadiq Gentle. Allah ya gafarta masa! Siyasa ta kan hana mu ganin gaskiya, ko kuma ta sa mu faɗi ba daidai ba. Misali, lokacin da Dan Bello (Allah ya gafarta wa mahaifinsa) ya ɗauko hotuna da videos na makarantun da s**a lalace, kai tsaye wasu s**a shiga s**arsa da cewa WAI SHI BA YA TAƁA YABAWA GWAMNATI KAWAI SABODA ADAWA. Ba adawa ba ce. Da haka a ke gyarawa gwamnati aikinta, kuma yarda da haka ya sa mai girma Gwamna ya kai ziyara makarantun nan take, kuma kai tsaye ya fara aiki! In ya zama kullum yabo kawai muka iya, to babu ranar da za a gyara ɓarnar da idon gwamnati bai kai kanta ba, ko cuwa-cuwar ɓatagarin ma'aikatan gwamnati.
Gare ku waɗanda ke kewaye da gwamnati, ku ji tsoron Allah a cikin aikin da kuke yi. Hakane akwai yabon gwamnati, kwarzanta ayyukan gwamnati da fito da kyawawan ayyukanta don yaɗa manufa ta siyasa. Amma kuma ba kodayaushe ne mai s**ar gwamnati ya ke zama ɗan adawa ba. Bal ma masoya sun fi yawa a cikinsu. Kyawun tsarin Dimukuraɗiyya shine bayar da damar s**an ayyukan gwamnati ga wanda bai gamsu ba. Kuma ma, wanda duk ya ce maka ka gyara, Wallahi ba maƙiyi ba ne, koda kuwa daga tsagin ƴan adawa ya ke. Abinda ya yi sunansa taimako. Gyara kayanka ba zai taɓa zama sauke mu raba ba.
Copied from Sir Mubarak Ibrahim Lawan
Hafiz A Haruna