27/10/2023
FRI/27/OCT/2023
CIKIN YANAYIN JIMAMI DA NUNA ALHINI NAKE MIKA SA'KON TA'AZIYYA GA AL'UMMAR GARIN MARU AMADADIN HON. MOUKHTAR MUHAMMAD LUGGA , BISA GA HARIN DA YAN BINDIGA S**A KAI GARIN A DAREN JIYA. 😭😭😭
Ina Amfani da wannan Dama cikin Yanayin Jimami da Tausayawa ga Al'ummar Garin Maru A madadin Mai Girma Shugaban Ma'aikata a Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara Kuma Shugaban Jam'iyyar PDP Hon. Mouktar Lugga MON. (Wambam Maru) , bisa ga kisan Gilla da Akayiwa Mutanen Garin A Daren Jiya Sanadiyar Harin Da Yan ta'adda S**a Kai Garin, Allah Ubangiji Yagafartamasu Yayi Rahama gareshi, Allah Ubangiji Yabawa 'Yan uwa, da Abokan Arzi'ki Juriya da Hakuri na Rashi, Allah ya iyakace Abun.
Daga karshe; Zamu cigaba da Kira ga Gwamnati Dakuma Hukumomin tsaro Dasu tashi tsaye wajen Daukar kwakkwaran Mataki na Ganin sun Dakile matsalar Datake tunkarar Al'ummar Jahar zamfara musamman a Garin Maru na yawaitar Kai Hare-haren Yan BINDIGA, Gwamnati, Hukumomi, 'kungiyoyi, Da Dukkanin Al'umma Hakine a Kawunan Ku na Ganin Antashi tsaye Domin Ya'kar wannan Yawan Kai Hare-haren Yan BINDIGA a Kauyukanmu Datake kokarin Mamaye Sauran Garuruwa.
Allah Ubangiji Yagafartamasa, Dama Sauran Al'umma Baki Daya Allah ya kawo Muna Aminci a jaharmu da Kasa Baki Daya.
✍️✍️✍️
✍️✍️✍️