26/10/2025
Kalaman Sani Shinkafi ga Matawalle cike suke da hassada da bakin ciki.
Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta jihar Zamfara ta bayyana cewa kalaman da Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya yi kan Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr. Bello Muhammad Matawalle (MON), sun samo asali ne daga hassada da jin zafi da bakin ciki saboda rasa tasiri a siyasar jihar.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce ta damu da irin yadda Shinkafi ke fitowa da maganganu marasa kan gado, inda take siffanta shi a matsayin mutum ma ci amana, hassada da neman suna ta kowace hanya. Kungiyar ta ce duk da irin taimakon da Matawalle ya yi masa a baya, yanzu kuma ba abin da zai saka masa da shi sai s**a da kazafi.
Kungiyar ta bayyana cewa kafin Matawalle ya zama gwamna a 2019, Dr Shinkafi ba shi da wani tasiri a siyasa, domin ko a mazaba bai taɓa lashe zaɓe ba, Matawalle ne ya ɗaga shi ya ba shi dama da mukamai, amma daga baya sai ya zama ma ci amana da neman kawo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar.
A cewar kungiyar, maganganun Dr Shinkafi na baya-bayan nan kan Matawalle tamkar ihu ne na ɗan siyasar da ya rasa jama’a, domin yanzu babu wanda ke tare da shi, hatta wadanda s**a taɓa ruɗuwa da shi sun bar shi. Haka kuma tarihinsa na tsalle daga jam’iyya zuwa jam’iyya domin neman kuɗi da suna, ya tabbatar da cewa babu ainihin akida, nagarta a siyasarsa.
Kungiyar ta matasan APCn ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga Dr. Bello Muhammad Matawalle, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma minista a ma'aikatar tsaron Nijeriya a halin yanzu ya nuna nagarta, kishin ƙasa da aminci ga jam’iyya.
Hakazalika, kungiyar ta kuma gargadi Dr Shinkafi da ya daina amfani da ƙarya da farfaganda don neman kulawa, tana mai cewa lokacinsa a siyasa ya ƙare. Sannan kuma kungiyar ba za ta lamunci irin waɗannan maganganu ba, kuma jam’iyyar ta APC a jihar Zamfara tana nan haɗe ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da Dr. Bello Matawalle.
Daga karshe, kungiyar ta kara da cewa, babu irin maganganu, bakin ciki daga wasu ‘yan siyasa da s**a gaza da za su hana jam’iyyar samun cikakkiyar nasara a zaɓen 2027.