26/08/2026
KRISMETI VS MAULIDI
(Babu wani bambanci tsakaninsu, Ga dalilaina kamar haka)
1- Annabi Isa (A.s) bai ce ayi masa krismeti ba
Haka nan Annabi Muhammad (s.a.w) bai ce ayi masa bukin Maulidi ba.
2-Ashe kenan kirkirar Krismeti akayi kamar yadda shima Maulidin kirkirarsa aka yi.
3- Ana cakuɗa maza da mata a bukin krismeti, Haka nan ana ana cakuɗa mata da maza a bukin Maulidi
4- Ana hura balom-balom a filin krismeti ana bawa yara suna rikewa kamar yadda shima a Maulidi ana yin hakan.
5- Ana kiɗe-kiɗe a Bukin krismeti kamar yadda ana kiɗe-kiɗe a bukin Maulidi
6- Ana rawa da cashewa a bikin Krismeti kamar yadda ake cashewa sosai a bukin maulidi.
7- Ana baiwa Annabi Isa matsayin Allah a bikin Krismeti hakanan ana baiwa Annabi da shehunnai matsayin Allah a bukin Maulidi.
8-Ana anko a bikin krismeti kamar yadda ake anko a bukin maulidi.
9- Ana kawo ƙissoshin karya a bukin krismeti kamar yadda ake kawo ƙissoshin karerayi a bikin Maulidi
10- Ana manna fostocin yesu kamar yadda ake marna fostocin Shehu inyass a Bukin maulidi
"تلك عشرة كاملة"
Ya Allah ka tsare mana imaninmu ka tabbatar damu akan sunnar Ma'aiki (s.a.w)
Ameeen
by sunna sak