PRESS MEDIA ISA

PRESS MEDIA ISA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from PRESS MEDIA ISA, Grocers, Fodiya Yar'makafi Isa, Isa.

12/11/2025

*GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!!*

*ƳAN UWA MUSULMI ALMAJIRAN SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) NA HALKAR TASHAR RAGGAYE DAKE DA'IRAR ISA TA JAHAR SAKKWATO*

*SUNA FARIN CIKIN GAYYATAR AL'UMMAR MUSULMI ZUWA WAJEN GAGARUMIN MAULUDIN MANZON ALLAH (S) WANDA ZAI GUDANA*

*MAI JAWABI MALAM ABUBAKAR NUHU T/ MAFARA (MALAM ABBAH)*

*MAWAKI MALAM AMMAR MUHAMMAD (DAN TINKA) ZARIA*

*KAMAR HAKA*

*RANAR LARABA 12 NOV 2025*
*WURIN SARDAUNA PRIMARY SCHOOL ISA*
*LOKACI 4:30 NA YAMMA DA KUMA KARFE 08:00 NA DARE*

*ALLAH BADA IKON ZUWA ILAHEY*

Yunƙurin haɗin Kan Malaman addinin Musulunci, Prof. Ibraheem Maqari da tawagarshi sun ziyarci Jagora Shaikh Ibraheem Zak...
02/11/2025

Yunƙurin haɗin Kan Malaman addinin Musulunci, Prof. Ibraheem Maqari da tawagarshi sun ziyarci Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yau Lahadi 11 ga Jimadal Ula 1447 (2/11/2025), a gidansa dake Abuja.

Bayan gabatar da jawabai da shawarwari akan muhimmancin haɗin kai da kusantar juna tsakanin malaman addini, Jagora (H) ya ƙarfafi wannan ƙoƙari sannan yayi fatan alkhairi da samun nasara.


— Sayyid Ibraheem Zakzaky Office


02/11/2025

22/10/2025

FAƊAKARWA

Bismillahir Rahamanir Raheem.

A 'yan kwanakin nan, wasu da muke kyautata zaton 'yan uwa ne, kuma masu kyakkyawar nufi, suna amfani da fasahar' Artificial intelligence (AI)' suna ƙirƙiran hotuna iri daban-daban, suna yaɗawa a kafafen sadarwa.

Hotunan na ɗauke da wasu alamomin Harka Islamiyya, k**ar hoton Jagora (H) a cikin wasu gurare, irin su dakin gwaje-gwaje, ko dakin yaƙi, ko filin daga da sauransu. Ko kuma su kirkiri hoton wasu mutane su saka musu kayan soja, suna tirenin a wani waje, tare da sanya musu Logo din Harisawa. Ko kuma canzawa hoton Jagora (H) fasali, zuwa wani abu mai k**a da wargi da wasa, tare da sanya Logo din Ofishin Jagora a jikin hoton, sai ya zama k**ar Ofis din ne ya fitar da hoton a haka.

Lallai wadannan ayyukan ba abu ne kyakkyawa ba, ba kuma sunansa cigaba ba, abu ne wanda yake da illa, k**a daga rashin wayewa, da mayar da Jagora (H) ko Harka Islamiyya a matsayin wasa da wargi a idon duniya, zuwa baiwa maƙiya iri daban-daban kafar cutar da Harka ta fuskoki daban-daban yanzu ko nan gaba.

Bisa haka, muna kira ga 'yan uwa da suke yin irin wannan, su bari. Waɗanda s**a yi a baya, su goge a shafukansu. Har ya zama in an ga wani ya cigaba ƙirƙira ko yaɗa irin waɗannan zanen, an san cewa da wata mummunar manufa yake yin hakan a nan gaba, kuma 'yan uwa ba za su biye masa ba.

Muna fatan Matasan Harka Islamiyya, - ma'abota basira da sadaukarwa - za su duƙufa wajen binciken hanyoyin samar da cigaba na haƙiƙa ga tafarkin gwagwarmaya, ba tare da shagaltuwa da abubuwan da s**a fi k**a da wasa ba.

H-Central.
— Hurrasul Harakatil Islamiyya
29/4/1447 / 22/10/2025

Wani bangare na Hurras, Imam Hassan Al-mujtaba A,S Sokoto Zone, Isa Unit. a muzaharar mauludin ma'aiki saww wadda yan'uw...
03/10/2025

Wani bangare na Hurras, Imam Hassan Al-mujtaba A,S Sokoto Zone, Isa Unit. a muzaharar mauludin ma'aiki saww wadda yan'uwa musulmi almajiran sayyid Ibrahim Yaqub zakzaky (H) na garin Isa dake jahar sokoto s**a gudanar a ranar asabar din da ta gabata 27__ 09__ 2025 alhamdulillah Hurras sun isar da sakon JAGORA (H) kuma sun jaddada bai'a ga Allamah (H) akan gwagwarmayar yunkurin tabbatar addinin musulunci har zuwa ga nasara ko shahada.

_Shamsu Aliyu Shamaki Isa




27__ 09__ 2025

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un Ko yau mahara sun kashe mana Haris kuma dan Tamsiliyya Mal. Hamisu Makuwana, da shi ...
24/08/2025

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un

Ko yau mahara sun kashe mana Haris kuma dan Tamsiliyya Mal. Hamisu Makuwana, da shi munkayi Tattakin bana a yankin Funtua, A wannan satin sau uku kenan 'yan Ta'adda suna kisa da daukar mutane masu yawa a wannan babban gari dake kusa da shiga Sabon birnin gobir.

Allah ya sauwaka

MUN CIKA WATAN SAFAR 1447 Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ اللهم صل على...
24/08/2025

MUN CIKA WATAN SAFAR 1447

Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ

اللهم صل على محمد وعلى آل محمد🌹🌹

Ana sanar da al'umma cewa yau Lahadi watan Safar ya cika kwana talatin (30) cur. Don haka gobe Litinin za ta zama 1 ga watan Rabi'ul Awwal 1447. In sha Allah.

Muna taya al'ummar Musulmi murnar zagayowar watan haihuwar Manzon Rahama (SAWA). Allah Ta'ala Ya sa a yi bukukuwa lafiya.

Alah ya ba mu sa'a.

Wassalam






29/Safar/1447
24/08/2025

DUBAN WATAبِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ اللهم صل على محمد وعلى آل محمد🌹 Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky...
23/08/2025

DUBAN WATA

بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ

اللهم صل على محمد وعلى آل محمد🌹

Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).

Ana biɗar ƴan'uwa Musulmi da su fara duba jinjirin watan Rabi'ul Awwal daga yau Asabat 29 ga watan Safar, 1447.

Za a iya sanar da labarin ganin watan ta waɗannan lambobi:

07064194054
09036186572
08035686569

Wassalam






29 Safar 1447
23/08/2025

SANARWA! SHEKARAR 1446 TA KAMMALA بسم الله الرحمن الرحيماللهم صل على محمد وال محمد وعجل فرجهم. Ana sanar da ƴan'uwa cewa...
26/06/2025

SANARWA!

SHEKARAR 1446 TA KAMMALA

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد وال محمد وعجل فرجهم.

Ana sanar da ƴan'uwa cewa yau Alhamis 29 ga Zhul Hijjah shekarar 1446 ta kawo ƙarshe don ta cika kwana 355 daidai. Don haka gobe Juma'a za ta zama 1 ga watan Al-Muharram 1447.

Kada a manta da ayyukan ƙarshen shekera a yau da kuma ayyukan sabuwar shekara gobe. Akwai salloli da addu'o'i ma'thurai na waɗannan ranakun. A duba cikin مفاتيح الجنان da sauran littafan addu'o'i.

Kamar yadda aka saba za a shiga zaman jajen tunawa da shahadar Abi Abdillah (AS) daga gobe ke nan, in sha Allah.

السلام على الحسين المظلوم الشهيد 🙏






29/ZulHijja/1446
26/06/2025

MUN CIKA WATAN ZHUL QA'DAH 1446: Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ اللهم...
28/05/2025

MUN CIKA WATAN ZHUL QA'DAH 1446:

Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ

اللهم صل على محمد وعلى آل محمد🌹🌹

Ana sanar da al'umma cewa yau Laraba watan Zhul Qa'adah ya cika kwana talatin (30) cur. Don haka gobe Alhamis za ta zama 1 ga watan Zhul Hijjah 1446. In sha Allah.

Kada a manta da ayyukan kwanuka goma na wannan wata wadda Allah Ta'ala ya kira su layalul ashar (ليال العشر) a Suratul Fajr. Da kuma ladubban layya don tunawa da sadaukarwar Annabi Ibrahim (AS).

Allah ya ba mu sa'a.
Wassalam






30/Zulqada/1446
28/06/2025

12/03/2025

... “IN KA WAYI GARI KANA MAI AZUMI.."

Jinka yai Azumi, gani ka yai Azumi, shu'urinka yai Azumi, fatarka tai Azumi, kai duk gaɓobinka sui Azumi. Ma'ana Azumin waɗan nan gaɓobi, daga barin haramomi, kai harda makaruhai.
Mene ne Azumi? Azumi shine kamewa, me ake kame kamewa? Shine barin abu k**ar yadda yazo a Suratu Maryam ya nuna suna azumin magana, mu ba kawai bamu azumin magana bane anma hanamu, an hanamu Azumin magana, wato su yakan zamo in mutum yana azumi ya zamo baya magana sam-sam.
Amma mu ya zama bakin gwargwado bakinka ya zamo ka kame shi baka magana sai abin da yake shine mai kyau, imma kana zikirine, ko karatun Alkur'ani ko addu'a, ko kana faɗin magana mai kyau kokuma kai shiru. Kar ka faɗi haram banda zage-zage banda giba kaga bakinka yayi azumi kenan, ba ciki kawai ba, ba'a sa mashi abinci ba.

To azumi magana ya zama ka kame bakinka daga faɗan haram dama duk abinda yake makaruhi ne, kai ko abinda bai da amfani, koda magana zaka yi ya zamo kayi Economism ɗin kalmomi ka (ka taƙaita kalmomin ka) ka zazzaɓo kalmomin da s**a zama lazim koda zaka bada abu kace ayi kaza sai ka faɗi kalmomin da zasu wadatar. Banda zaunawa Aita firace firace da surutai, koda ko na halas ne ballan tana ma daga nan za'a faɗama na makaruhi, ƙilama a faɗama haram Alal misali giba haramun ne.

_Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin da yake karanto wasiyyar Imam Ja'afar As-Sadeeq (A.S) a Husainiyyah Baqiyatullah Zaria._


WhatsApp Channel 📱
https://whatsapp.com/channel/0029Vb2obG1EQIakxZ27Tg35

Address

Fodiya Yar'makafi Isa
Isa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when PRESS MEDIA ISA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category