Kalaman Hikima

Kalaman Hikima Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kalaman Hikima, Contact Us through Our Chennel On YouTube/Kalaman Hikima, Jigawa.

KADA KA YI FUSHI DA KOMAIBa duk abin da mutane suke yi ba ne ya kamata ka ɗauka da zafi. Wasu maganganun idan ka yi shir...
16/05/2026

KADA KA YI FUSHI DA KOMAI

Ba duk abin da mutane suke yi ba ne ya kamata ka ɗauka da zafi. Wasu maganganun idan ka yi shiru ka wuce, sun fi alheri fiye da ka tsaya yin fushi ko rigima a kai.

Ka sani, yin abu cikin hankali da haƙuri suna ceton mutum daga nadama.

Mutum mai saurin fushi yana yawan yin kuskure, a wasu lokutan yana rasa mutunci, haka kuma yakan lalata dangantaka.

Amma mai nutsuwa, wato mutumin da ba ya saurin fushi… ko bayan an bata masa rai zuciyarsa tana samun salama.

Wani lokaci yin shiru shi ne mafi girman nasara.

Allah Ya datar da mu.

MAI HAƘURI SHI KE DA NASARAMutane da yawa suna son nasara… amma ba kowa ne yake son haƙurin da ake bi kafin a same ta ba...
16/05/2026

MAI HAƘURI SHI KE DA NASARA

Mutane da yawa suna son nasara… amma ba kowa ne yake son haƙurin da ake bi kafin a same ta ba.

Ka tuna cewa itace ko tairo ba ya girma a rana ɗaya. Haka ma rayuwa take. Wasu lokuta:
> Za ka yi ƙoƙari ba tare da ganin sakamako nan take ba.
> Sannan za ka iya shan wahala kafin lokacin sauƙi ya zo.
> Sannan kuma sai jira tsawon lokaci kafin burinka ya cika.

Amma idan ka ci gaba da haƙuri tare da ƙoƙari… lokacinka zai yi.

Mai haƙuri baya rasa rabonsa.
Allah Ya datar da mu

ABOKAI IRI UKU NE1- Abokin Hira2- Abokin Shawarar3- Abokin Sirri1- Abokin hira — domin nishadi da tattaunawa.2- Abokin s...
15/05/2026

ABOKAI IRI UKU NE

1- Abokin Hira
2- Abokin Shawarar
3- Abokin Sirri

1- Abokin hira — domin nishadi da tattaunawa.
2- Abokin shawara — wanda yake taimaka maka da tunani mai kyau idan ka rikice.
3- Abokin sirri — wanda ka yarda da shi wajen ɓoye damuwarka da sirrinka.

Ba kowane aboki ne ya kamata ka ba dukkan sirrinka ba.

Matsalar mutane da yawa a wannan zamani ita ce: suna haɗa matsayin abokai wuri guda. Wannan ya sa ake samun:

> Cin amana,
> Yawan sabani,
> Da nadama.

Ka san matsayin kowa a rayuwarka… kuma ka mu’amalance su da hikima. Ba kowa ne ya kamata ya san komai game da rayuwarka ba.

Allah Ya datar da mu.

KA DAINA JIRAN CIKAKKEN LOKACI Mutane da yawa suna da manyan burika… amma suna jiran “lokaci mai kyau” kafin su fara. Ga...
14/05/2026

KA DAINA JIRAN CIKAKKEN LOKACI

Mutane da yawa suna da manyan burika… amma suna jiran “lokaci mai kyau” kafin su fara.

Gaskiya ita ce: Babu cikakken lokaci a rayuwa. Ka fara da abin da kake da shi yanzu.

Ƙaramin mataki yau… ya fi babban buri da ba a fara ba. Kada tsoron kuskure ya hana ka tafiya. Domin ko manyan masu nasara… sun fara ne ba tare da komai cikakke ba.

Nasara tana son masu ƙoƙari, ba masu jira kawai ba.

Allah Ya datar da mu.

KADA KA RAINA KANKAMutane da yawa sun kasa cimma burinsu ba don ba su da baiwa ba… sai don sun yarda da maganganun mutan...
13/05/2026

KADA KA RAINA KANKA

Mutane da yawa sun kasa cimma burinsu ba don ba su da baiwa ba… sai don sun yarda da maganganun mutane fiye da yadda s**a yarda da kansu.

Ka tuna:
Duk babban mutum da kake gani yau, ya fara ne da ƙaramin mataki.

Kada ka tsaya saboda:
> Mutane suna maka dariya,
> Ko Saboda Mutane suna ƙin ka,
> Ko kuma ka taɓa faduwa.

Kada ka bari maganganun mutane su kashe maka burinka. Abin da kake gani ƙarami a jikinka yau… shi ne zai iya zama babban nasararka gobe.

Ka yarda da kanka. Ka ci gaba da ƙoƙari. Ka daina kwatanta rayuwarka da ta wasu.

Rayuwa ba ta tambayar sau nawa ka fadi… Tana kallon sau nawa ka tashi ka ci gaba.

Ka daina jiran lokacin da komai zai yi kyau kafin ka fara. Fara da abin da kake da shi yanzu.

Wata rana mutanen da s**a raina ka… su ne za su riƙa yaba nasararka.

Allah Ya datar da mu.

02/05/2026

Alkhairi Dawwama Yake....

29/04/2026

Kyakkyawan Zance, Kyauta, Gafara......

28/04/2026

Idaniyarmu Tana Kallon Zahiriyya Ne Kawai...

26/04/2026

Ka Dauki Darasi Daga Jiyanka...

25/04/2026

Duk Wanda Ya Ji Kan Wani....

24/04/2026

Kada Ka Shiga Cikin Damuwa.....

Address

Contact Us Through Our Chennel On YouTube/Kalaman Hikima
Jigawa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kalaman Hikima posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share