AA Kwangeelah

AA Kwangeelah May Every New Chapter be Better than Your last🔥🌚

Ya Kai Ɗan Adam Wa Kake Saɓawa Ne?Wanda Ya Halicceka Daga Wani Ruwa Wulaƙantacce Abin Ƙyama Amma Ya Fifita Ka Akan Dukka...
14/04/2025

Ya Kai Ɗan Adam Wa Kake Saɓawa Ne?

Wanda Ya Halicceka Daga Wani Ruwa Wulaƙantacce Abin Ƙyama Amma Ya Fifita Ka Akan Dukkan Halittunsa?

Wanda Yayi Ka Cikakken Mutum Yayi Maka Ado Na Halitta Da Ni'imomin Da Idan Ka Kalli Kanka A Yanzun Nan Bazaka Iya Ƙidaya Koda Na Jikinka Ba?

Ubangijin Da Yake Kareka Sannan Ya Saukar Maka Arzikinsa Dare Da Rana, Batare Daya Ɗora Maka Harajin Ko Ƙwandala Ba?

Ubangijin Daya Tanadar Maka Aljanna Duk Da Taurin Kai Da Kake Masa, Ga Mala'iku Da Ko Saɓa Masa Bazasu Taɓayi Ba, Su Bai Gina Musu Ba Sai Kai?
Ubangijin Da kafin Ya Halicceka Saida Kayi Alƙawarin Idan Har Kazo Duniya Shi Zaka Bautawa Shi Kadai?

Da Kazo Sai Ka Biyewa Maƙiyinsa Shaiɗan.

Wanda Bakada Maƙiyi Tamkarsa?
Wanda Yayi Silarka Faɗowarka Duniya Gidan Wahala?!

Wanda Yayi Alƙawari Sai Yayi Iya Ƙoƙarin Hanaka Nutsuwa Da Jindaɗi A Duniya Har Ka Mutu?

Wanda Bashi Da Burin Daya Wuce Duk Wuyar Da Kasha A Duniya Idan Ka Mutu Ma Kaci Gaba Da Shan Azabar Wacce Ta ninninka Ta Duniyar Milyoyin Adadi?

Ashe Bazaka Ji Kunya Ba?

Yana Kallon Ka Kake Saɓa Masa?
Ya Umarceka Da Sallah 5 Kacal Kake Tozarta Su?
Ya Hanaka Kusantar Zina Da Dangoginta Kake Zaƙewa Mata Da Kallon Batsa?
Bakasan Yana Ganinka Ba?

Me Zakace A Ranar Da Zai Tsayar Dakai Yana Tambayarka?
Annabi [Saw] Yana Cewa
ما منكم من أحد إلا سيكلمه ربه ليس بينه وبين الله ترجمان
"Ba Ɗaya Daga Cikinku Face Sai Allah Yayi Magana Dashi Babu Typinter Mai Tarjama A Tsakaninsu"😭

Astangafirullah Wa Atubu Ilaihi😭

RASHIN SANI YAFI DARE DUHU....1. Wani Gaye ya haɗu da Ɗan ajinsu shekaru da dama bayan sun kammala makaranta, bai yadda ...
14/04/2025

RASHIN SANI YAFI DARE DUHU....

1. Wani Gaye ya haɗu da Ɗan ajinsu shekaru da dama bayan sun kammala makaranta, bai yadda da abinda idanun shi ya gane mishi ba, domin Abokin shi ya gani cikin makekiyar Benz. Sai ya dawo gida yana jin haushin kanshi, ya ɗauka cewa ya gaza a rayuwa. *Abinda bai saniba shine wannan abokin nashi direba ne lokacin da s**a gamu Ogan shi ne ya aike shi da motar. 🙅

2. Wata Ƴar'uwa taci mutuncin mijinta domin he is not romantic. Ta zarge shi da baya zuwa ya buɗe mota idan ya kaita wajen aiki kamar yadda mijin ƙawarta yake yiwa matar shi idan ya ajiye ta a wajen aiki. *Abinda bata sani ba shine ƙofar motar mijin ƙawar nata baya buɗuwa ta ciki saita waje. Shiyasa mijinta yazama dole sai yazo ya buɗe mata kofar ta waje* 💯

3. Matar wani Ɗan'uwa takai ziyara gidan wata ƙawarta, sai hankalin ta ya tashi yadda taga ƴaƴan ƙawar nata gwanin sha'awa suna wasa, ita kuma ɗanta guda ɗaya tsawon shekaru biyar, amma abinda bata sani ba shine: cikin wannan yaran da tagani guda uku, guda ɗaya ne kaɗai wanda ƙawar ta haifa, shima yana fama da sikila wanda likitocin su, sun tabbatar bazai jimaba nan da watanni zai rasu, sauran 2 kuma kuma adopting dinsu tayi daga gidan marayu 🥹

Sir wisdom DARASIN CIKI SHINE

Ma'aunin mu na rayuwa kowa da nashi daban daban, don haka nemi naka ka auna taka rayuwar. Idan kana kallon mutane kana kwatanta su da kanka, hakan bazai sanya ka zamto maɗaukaki ba, sai dai maƙasƙanci...🙅

Idan da ka san irin lodi dake kan hawainiya, da ba zaka riƙa tunanin menene yasa take sanɗa ba, domin haka kada ka raina abinda kake dashi, yi amfani dashi kaji daɗin rayuwar ka, kafin ta Allah ta kasance ☠️

Mu daina tambayar kawunanmu irin wadannan tambayoyin👇

Sa'annina suna yin aure
Sa'annina suna da yara
Sa'annina suna da aiki mai kyau
Sa'annina suna cin nasara
Sa'annina suna sayan motoci na alfarma
Sa'annina manyan yan siyasa ne a kasa
Sa'annina suna da katafarun gidaje,

Hakane, gaskiya ne! Amma kuma Ɗan'uwa ai abun kunya ne ac

13/04/2025

Wata Rana Annabi Muhammadu (S.A.W) Yana Zaune Cikin Sahabban Sa Sai Yace... Dukkan Ku Zaku Shiga Aljannah Sai Wanda Yaki; Sai Sahabbai Sukace Wazaiki Aljannah Yarasulullah?

Sai Manzon Allah S.A.W Yace Wanda Yabini Zai Shiga Aljannah Wanda Kuma Yasaba Min To Hakika Shi Yaki Aljannah.

ALLAH Tashemu Karkashin Tutarsa Manzon Tsira, ALLAH Yasa Mucika Da Imani, Aameeen.

13/04/2025

Hi Everyone🙌

Address

Kalgwai
Jigawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AA Kwangeelah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category