13/04/2025
UBANGIJI MAKIYAYINA NE.
Ubangiji makiyayina ne,
Ba zan rasa kome ba.
Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,
Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.
Yana ba ni sabon ƙarfi.
Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.
Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,
Gama kana tare da ni!
Sandanka na makiyayi da kerenka
Suna kiyaye lafiyata.
Ka shirya mini liyafa Inda maƙiyana duk za su iya ganina, Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,
Ka cika tanduna fal da mai.
Hakika, alherinka da ƙaunarka
Za su kasance tare da ni muddin raina.
Haikalinka zai zama gidana har abada.
NINE SIA
NA GASKANTA