Voice of Gama

Voice of Gama Zaman lfy shine burinmu

Aminu Abdullahi Warkal ya sabunta mubaya'arsa ga Madugun Kwankwasiyya Engr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.A baya dai Warkal ...
23/02/2026

Aminu Abdullahi Warkal ya sabunta mubaya'arsa ga Madugun Kwankwasiyya Engr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

A baya dai Warkal ya yi wasti da tafiyar Kwankwasiyya ya shiga jam'iyyar APC, wanda ake zargin ya bar NNPP din ne sakamakon ba a biya masa wasu bukatunsa a Gwamnatin Kano da yake ikirarin sun kafa ba.

Kafin wannan lokacin dai Aminu Warkal shi ne shugaban kungiyar Kwankwasiyya Tiktokers, kafin wasu shugabannin kungiyar su tsige shi.

Dawowarsa Kwankwasiyya kuma a lokacin da wasu ke ganin tsarin na cikin tsaka mai wuya, ya dauki hankalin al'umma da dama.

Me ku ke tunanin ya sanya Aminu Abdullahi Warkar yin mi'ara koma baya?

20/08/2025

A ƙarasa mana wannan karin maganar...

20/08/2025

Wane gari kataba zuwa haryanzu kana kewarsa??

20/08/2025

Zabi sonka

Sponsored Da ɗumi-ɗumi: Ogan Ɓoye ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai a Ƙaramar Hukumar Nassarawa.Mai Girma Shugaban Karamar...
06/01/2025

Sponsored

Da ɗumi-ɗumi: Ogan Ɓoye ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai a Ƙaramar Hukumar Nassarawa.

Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa Hon. Amb Yusuf Imam Ogan Boye,Ya Nada Mukamai Da Zaiyi Aiki Tare Da su Don Tafiyar Da, Shugabancin Karamar Hukumar Nassarawa. Inda Mukaman Ya Hada Fanni Daban Daban Kamar Haka.

1-Jamil Da Attahir :Prin Personal Sectary (PPS)

2-Rabilu Muhammad Gama: Personal Asst Documentation

3-Kabiru Ishaq Hannafi: Personal Asst Domestic Affairs

4-Ahmad Hussaini Nuhu: Personal Asst Special Duties

5-Hassan Shehu Adam :Special Asst Media I

6-Comrd Muhd Habib: Special Asst Media II

7-Habibu Adamu Abubakar:Personal Asst Decumentation To The Vice Chairman

8-Ahmad Aminu Sunusi:Personal Domestic.

9-Kamal Muhammad Adam:Personal Asst Decumetation To Sectary.

10-Farouq Garba:Personal Asst Domestic To Sectary.

11-Jamilu Sa,idu :Cheif Details Affairs I

12-Salisu Garba :Cheif Details
Affairs II

13-Shamsu Yahaya Abdullahi:Special Asst Photographic

14-Halima Abubakr :Women Affairs

15-Auwalu Abdullahi :Cheif Protocol

16-Khadija İdris:D.G Humanitarian

17- Abdul,Aziz Badamasi :D.G Digital Economic Resources Moblization

18-Sharif Nazir Hassan :D.G Land Physical Planning.

19-Sunusi Abdullahi Ya,u:D.G İnternal Affairs

20-Barrister Umar Shehu Kawaji:Local Government Legal Council

21-Hon.Dalha Yusuf Babban Gawo:D.G Development Strategy

22-Dr.Garba Miko Dakata :D.G Political Affairs

23-Hon .Sani Jibrin SK: D.G Corporate

24- Usman M.K Giginyu: D.G Work.

Inda Munakaman Ya Kara Hadawa Da Masu Dauko Masa Rahoto, Da special Assistant.Kamar Haka.

25- Jazuly Isah Fashion:D.G Market

26- Muhd Yusuf Hamza :Excutive Asst Empowerment

27-Hon.Jasohua Gawuna :Executive Asst Tribe .

28- Yusuf Hassan Gote: Ext Asst On Groups $Association.

29-Abdullahi Dauda :Ext Asst On Slaughter Houses

30- mustagha Muhd Adam:Ext Asst On Project And Monitoring.

31-Sabo A Abdullahi :Special Asst On Yankaba Market.

32-Hon.Muhd Hussain:Special Asst On T

Gwamnatin Buhari ce ke da alhakin matsalar da ake fama da ita a Najeriya--Fadar shugaban kasaGwamnatin Najeriya ta ɗoraw...
22/06/2024

Gwamnatin Buhari ce ke da alhakin matsalar da ake fama da ita a Najeriya-

-Fadar shugaban kasa

Gwamnatin Najeriya ta ɗorawa tsohuwar gwamnatin da ta gabata alhakin tashin hankali da kuma mastin tattalin arziki da ƴan ƙasar ke fama da shi.

Mai baiwa shugaban ƙasar shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa ya zamarwa tsohuwar gwamnati dole ta ɗauki alhakin halin da ƴan Najeriya ke ciki a yanzu.

Bayo Onanuga na mayar da martani ne kan wata maƙala da jaridar New York times da ake wallafawa a Amurka ta fitar, da ke nuna irin yadda gwamnati mai ci ke yiwa ƴan Najeriya matsar gyaɗa.

Ya ce rahoton babu komai a ciki illa kaidi na kafofin yaɗa labaran ƙetare, sai dai kuma abin takaici shine yadda s**a kasa yin bayani kan yanayin da gwamnati mai ci ta karɓi ƙasar a hannun gwmanitin Buhari da ta gabata.

Ya ce dukannin kafofin yaɗa labarai dama ƴan kasar na nunawa gwamnati yatsa kan yadda ta cire tallafin mai, sai dai an kasa gane irin asarar da ƙasar ta shafe sama da shekaru 20 tana tafkawa a ɓangaren bada tallafin man fetur ɗin kuma ba’a samun sakamako mai kyau.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Yi Gwanjon Jiragen Uku Na Shugaban Ƙasa Domin Rage Kashe Kuɗaɗen Kasa Wajen...
22/06/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Yi Gwanjon Jiragen Uku Na Shugaban Ƙasa Domin Rage Kashe Kuɗaɗen Kasa Wajen Gyaran Su

A ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi don rage yawaitar kashe kuɗaɗen Najeriya wajen tafiye-tafiye da gyaran jirage, shugaban zai yi gwanjon jirage uku daga jiragen da aka ware dan jigilar shuwagabanni da sanya kuɗaɗen a wuraren da zasu amfanar da ƙasar.

In ba a manta ba, a watannin baya Shugaba Tinubu ya sanya dokar da zata rage adadin yawan ƴan rakiya da zasu dinga tafiye-tafiye tare da shuwagabanni a ƙasar domin rage yawaitar kuɗaɗen da ake fitar wa a matsayin alawus.

Matakin ya kawo saiti ga tsarin tafiye-tafiye da kuma rage kaso mai yawa na kudaden ds gwamnati ke kashewa a baya.

22/06/2024

Kungiyoyin ma’aikatan jami'o'in kasar nan sun bawa gwamnatin tarayya
wa’adin mako biyu domin biyan albashin mambobinsu na wata hudu.

Gwamnan jihar Ogun ya raba wa ‘yan majalisar dokokin jihar filayen
noma a wani bangare na kokarin tabbatar da samar da abinci da
tallafawa shirin farfado da noma na gwamnatin tarayya.

Akalla dillalan kwaya 1,344 a Jihar Katsina ne s**a shiga hannun
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta ƙasa a shekarar
da ta gabata

KETARE.
Shugaba Putin ya ce Koriya ta Kudu za ta tabka mummunan kuskure
idan ta samarwa Ukraine da makamai.

Da Dumi-DumiBabbar kotun tarayya a Kano ta yi hukuncin soke nadin da aka yi wa Muhammad Sunusi na biyu, amma kuma ta ce ...
22/06/2024

Da Dumi-Dumi
Babbar kotun tarayya a Kano ta yi hukuncin soke nadin da aka yi wa Muhammad Sunusi na biyu, amma kuma ta ce hakan ba yana nufin soke dokar da majalisar dokokin jihar ta yi ba.

Alkalin kotun Justice Abdullahi Liman ya ce hukuncin da ya yanke a baya na dakatar da cire sarakunan Kano biyar na nan daram.


Ya kuke kallon wannan Hukuncin?

Shugaba Tinubu ya kawo Ali Nuhu Gwamnatin sa ne domin Bunkasa tattalin arzikin Kasa ta Hanyar Al'adu ~Minista bagudu.Min...
22/06/2024

Shugaba Tinubu ya kawo Ali Nuhu Gwamnatin sa ne domin Bunkasa tattalin arzikin Kasa ta Hanyar Al'adu ~Minista bagudu.

Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki Sen Abubakar Atiku Bagudu ya nemi tallafi daga kungiyoyin kasa da kasa da masu ruwa da tsaki ga Hukumar Fina-Finai ta Najeriya domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da Manajan Darakta/Babban Darakta, Dakta Ali Nuhu da manyan jami’an hukumar s**a kai masa ziyarar ban girma a ma’aikatar, ranar Alhamis, a Abuja.

Abubakar Bagudu ya yi nuni da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi niyyar kafa ma’aikatar al’adu da tattalin arziki domin ya fahimci cewa wasu kungiyoyin Al'ada da ayyuka na taimakawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.

Don haka ya yi kira ga Darakta Janar na Hukumar NFC da ya samar wa matasa damammaki masu ma’ana don cin gajiyar sana’ar. Bagudu ya kuma shawarci kamfanin da ya nemi hadin gwiwa da KOICA na Koriya ta Kudu, Japan da kuma ofishin jakadancin Faransa, don ciyar da masana'antar kasar gaba.

Ministan ya kira Dr. Ali Nuhu, wani Babban Jagora a cikin gwamnati don yin amfani da kwarewarsa wajen isar da sakwanni masu inganci na Renewed Hope da aiwatar da juriyar ‘yan Najeriya wadanda kullum suke aiki don rayuwa mai ma’ana.

Da yake jawabi, Darakta Janar na NFC, ya ce makasudin kara girman kasafin kudin kamfanin, domin samun damar cimma ayyukan da aka sanya a gaba. Ya kuma yi nuni da cewa, karin kasafin kudin zai baiwa Hukumar damar kula da ofisoshin hulda da jama’a, da inganta wurin zama na dindindin, da inganta ma’aikatan da ake da su da kuma daukar ma’aikatan da s**a tsufa.

Al’ummar Yankin Ja’en da ke Kano na ci gaba da neman dauki sakamakon yadda fadan daba ya ki ci ya ki cinyewa.Ko a Jumu’a...
22/06/2024

Al’ummar Yankin Ja’en da ke Kano na ci gaba da neman dauki sakamakon yadda fadan daba ya ki ci ya ki cinyewa.

Ko a Jumu’ar nan an samu rahoton samun asarar rayuka a yankin.

Address

Gama D Mangoro Shata
Kano
HIINAGDYSOSAIALLAHYABARZUNCI

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Voice of Gama posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category