DMM Hausa

DMM Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from DMM Hausa, Grocers, Abuja, Kano.

ACF TA ZAƁI DR. GONI FARUK UMAR DA WASU DOMIN KWAMITIN ASUSUN TALLAFIƘungiyar tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta zaɓi...
19/04/2026

ACF TA ZAƁI DR. GONI FARUK UMAR DA WASU DOMIN KWAMITIN ASUSUN TALLAFI

Ƙungiyar tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta zaɓi shugaban reshenta na Jihar Kano, Dr. Goni Faruk Umar, tare da wasu fitattun ‘yan Najeriya domin su zama mambobin Kwamitin Gudanar da Asusun Tallafi.

Rahoton KANO FOCUS ya bayyana cewa kwamitin, wanda ya ƙunshi manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar, zai kula da tafiyar da harkokin asusun tallafin na ƙungiyar.
A cewar jerin sunayen da ACF ta fitar, tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai ritaya, Mohammed D. Abubakar, shi ne Shugaban kwamitin, yayin da tsohon Gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong, zai kasance Mataimakin Shugaba.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Amina Dantata, Kashim Ibrahim Imam, Suleiman Adamu, Tijjani Bande, Aliyu Idi Hong, da Yerima Lawal Ngama.
Haka kuma akwai fitattun lauyoyi irin su Dakas I. Dakas da Joe-Kyari Gadzama, tare da wasu daga ɓangaren gwamnati da masu zaman kansu. Ƙungiyar ta naɗa Usman Kukasheka a matsayin Sakataren kwamitin, yayin da Maimuna Yaya Abubakar za ta zama Mataimakiyar Sakatare.

Ana sa ran wannan kwamitin zai taka muhimmiyar rawa wajen tara kuɗaɗe da kuma tabbatar da gaskiya da ingantaccen tsarin gudanar da su, domin tallafa wa ayyuka da manufofin dogon lokaci na ACF.
Shigar da Dr. Goni Faruk Umar tare da sauran manyan mutane na nuna ƙoƙarin ƙungiyar wajen amfani da gogewa da ƙwarewa iri-iri domin ƙarfafa tsarin tafiyarta.

Nasiru Yusuf Ibrahim, ANIPR
Sakataren Yaɗa Labarai na II.

ACF NOMINATES DR GONI FARUK UMAR, OTHERS TO ENDOWMENT FUND COMMITTEEThe Arewa Consultative Forum (ACF) has nominated the...
19/04/2026

ACF NOMINATES DR GONI FARUK UMAR, OTHERS TO ENDOWMENT FUND COMMITTEE

The Arewa Consultative Forum (ACF) has nominated the Chairman of its Kano State chapter, Dr Goni Faruk Umar, alongside several prominent Nigerians to serve on its Endowment Fund Management Committee.

According to KANO FOCUS, the committee comprising distinguished figures from across the country is expected to oversee the management and administration of the forum’s endowment fund.

Based on the list released by the forum, retired Inspector General of Police, Mohammed D. Abubakar, will serve as Chairman of the committee, while former Plateau State Governor, Simon Lalong, has been appointed as Vice Chairman.

Other notable members of the committee include Amina Dantata, Kashim Ibrahim Imam, Suleiman Adamu, Tijjani Bande, Aliyu Idi Hong, and Yerima Lawal Ngama.
The list also features prominent legal practitioners such as Dakas I. Dakas and Joe-Kyari Gadzama, along with other members drawn from both the public and private sectors.
The forum appointed Usman Kukasheka as Secretary of the committee, while Maimuna Yaya Abubakar will serve as Assistant Secretary.

The Endowment Fund Management Committee is expected to play a key role in mobilising resources and ensuring transparent management of funds to support the activities and long-term objectives of the ACF.

The inclusion of Dr Goni Faruk Umar and other eminent personalities underscores the forum’s commitment to leveraging diverse experience and expertise to strengthen its institutional capacity.

Nasiru Yusuf Ibrahim, ANIPR
Publicity Secretary II

FG STRENGTHENS ROLE OF TRADITIONAL INSTITUTIONS IN SECURITY AND GOVERNANCEThe Federal Government, under the leadership o...
19/04/2026

FG STRENGTHENS ROLE OF TRADITIONAL INSTITUTIONS IN SECURITY AND GOVERNANCE

The Federal Government, under the leadership of Bola Ahmed Tinubu, has adopted a strategic approach to addressing Nigeria’s socio-economic and security challenges by deepening collaboration with traditional institutions across the country.

The Senior Special Assistant to the President on Chieftaincy Matters, Alh. Abbas Tijjani Hashim (Sarkin Sudan of Kano), made this known while addressing development partners in line with the President’s directive.

He explained that the initiative is focused on leveraging grassroots intelligence through traditional rulers to strengthen Nigeria’s security architecture. According to him, traditional institutions remain critical stakeholders in community-based intelligence gathering and conflict resolution.

The strategy also aims to promote development through data-driven asset management, while expanding and redefining the roles of traditional rulers within the modern governance framework.

Discussions at the meeting highlighted the importance of organizing enlightenment forums for traditional leaders and updating their responsibilities to align with current realities and national priorities.

Alh. Abbas Tijjani Hashim reaffirmed the Federal Government’s commitment to working closely with traditional rulers at all levels to enhance national security, unity, and sustainable development.

TARIHIN SHARIF IMAM MUHAMMAD BIN ABDULKARIM ALMAGHILI
09/04/2026

TARIHIN SHARIF IMAM MUHAMMAD BIN ABDULKARIM ALMAGHILI

BIN ABDULKARIM ALMAGHILI

TINUBU’S HERITAGE IN ACTION: SSA ON CHIEFTAINCY AFFAIRS UNVEILS NEW CULTURAL MONITORING SYSTEMThe Senior Special Assista...
01/04/2026

TINUBU’S HERITAGE IN ACTION: SSA ON CHIEFTAINCY AFFAIRS UNVEILS NEW CULTURAL MONITORING SYSTEM

The Senior Special Assistant to the President on Chieftaincy Affairs, Abbas Tijjani Hashim, has announced the establishment of a monitoring and evaluation system aimed at promoting Nigeria’s cultural heritage and supporting government initiatives at the grassroots level.

Alhaji Abbas Tijjani Hashim, who also holds the traditional title of Sarkin Sudan of Kano, disclosed this during a meeting with key traditional titleholders, including the newly turbaned Sarkin Yamma of Bwari, Alhassan Musa Baba Chukuri, and the Dangaladiman Kwangwami, Lauwali Ibrahim.

According to the SSA, the initiative aligns with the vision of Bola Ahmed Tinubu to strengthen traditional institutions and ensure that cultural values contribute meaningfully to national development. He explained that the system will help track and evaluate the impact of cultural and community-based programs across the country. During the meeting, discussions focused on the role of traditional leadership in preserving cultural identity, promoting unity, and enhancing civic engagement among citizens.

The participants emphasized the importance of collaboration between government and traditional institutions in fostering sustainable development. Alhaji Abbas Tijjani Hashim also called on traditional rulers nationwide to remain vigilant and proactive in maintaining peace and security within their domains. He stressed that traditional leaders play a critical role in ensuring stability at the grassroots level.

The development is seen as part of ongoing efforts by the Tinubu administration to integrate cultural heritage into governance and strengthen community based structures across Nigeria.

I'SHIELD TEAM PAID A COURTESY VISIT TO THE NDLEA STRATEGIC COMMAND, KANO STATE. 10th March. 2026.Comrade Muzammil Sani s...
11/03/2026

I'SHIELD TEAM PAID A COURTESY VISIT TO THE NDLEA STRATEGIC COMMAND, KANO STATE. 10th March. 2026.

Comrade Muzammil Sani said the purpose of the visit was to formally introduce the organisation to the new Commander, CN Lawal Yahaya, and to present our key focus areas, which include Substance Use Prevention, Human Rights, Healthcare, Education, Youth Development, and Conflict Resolution. The visit also aimed to explore possible avenues for partnership and collaboration with the agency.

In his remarks, the Commander warmly welcomed our team and expressed his delight over the visit. He further shed light on the mandate of the agency, particularly in the areas of drug law enforcement, substance use prevention in schools and communities, public enlightenment, and alternative livelihood initiatives for individuals involved in illicit drug activities.

In reference to our areas of operation, the Command reiterated its readiness to work hand in hand with I'SHIELD in order to rid the state of the scourge of drug abuse and related social vices.

YAU NE RANAR MATA TA DUNIYA 2026Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata ta Duniya ta shekarar 2026, masu ruwa da tsaki sun y...
08/03/2026

YAU NE RANAR MATA TA DUNIYA 2026

Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata ta Duniya ta shekarar 2026, masu ruwa da tsaki sun yi kira da a kara bai wa mata dama da karfafa su, musamman mata masu buƙata ta musamman, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa da kuma gina al’umma mai karfi.

Ana gudanar da wannan biki a duk shekara a ranar 8 ga Maris, kuma a bana ya zo ne da taken “Ba da Domin Samu: Karfafa Mata Domin Samar da Duniya Mafi Alheri,” wanda ke jaddada muhimmancin hadin kai, zuba jari, da kuma kuduri wajen bunkasa hakkoki da damar mata da ‘yan mata.

Da take magana a yayin tunawa da ranar, wata Jarumar Addini da Al’adu a Jihar Kano, Bilkisu Ado Zango, ta bayyana cewa bai wa mata dama ya kamata a dauke shi a matsayin jari wanda zai ninka anfani ga al’umma, ba wai asarar albarkatu ba.

A cewarta, idan mutane, kungiyoyi da al’ummomi s**a yi niyyar tallafa wa mata, hakan yana haifar da damammaki da ke karfafa iyalai, al’ummomi da kuma ci gaban kasa baki daya.

Ta bayyana cewa taken “Ba da Domin Samu” yana nuna muhimmancin musayar anfani a tsakanin al’umma, tana mai cewa kasashen da ke fifita daidaito tsakanin maza da mata da kuma hada kowa a cikin al’umma suna samun karin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Ta kara da cewa bikin na shekara-shekara yana zama wata dama ta kara kaimi wajen magance matsalolin tsari da son zuciya da mata ke fuskanta a rayuwarsu ta kashin kai da kuma ta aiki.

Zango ta lura cewa mata na taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma da kuma tafiyar da ci gaba. Sai dai ta jaddada cewa mata masu nakasa s**an fuskanci karin kalubale na zamantakewa da na tsari, ciki har da wariya da kuma karancin damar samun anfani, wanda ke bukatar tsare-tsare da matakai na musamman daga gwamnati da al’umma.

Ta ce shirye-shirye irin su Faith and Cultural Champions for Healthy Women and Girls Project an tsara su ne domin magance wasu daga cikin wadannan kalubale ta hanyar wayar da kai kan harkokin lafiya da kuma inganta dabi’u masu kyau a cikin al’umma da za su anfani ‘yan mata da matasa mata.

Wannan shiri da Cibiyar Sadarwa da Tasirin Zamantakewa (CCSI) ke aiwatarwa tare da jagorancin Advisory Faith and Cultural Champions, yana da burin inganta lafiyar ‘yan mata matasa da mata kanana, ciki har da masu nakasa, a jihohin Kano da Kaduna.

A cewarta, shirin yana hada shugabannin addini da na al’adu masu daraja a cikin al’umma a matsayin Individual Faith and Cultural Champions, domin yada sakonni da dabi’u masu kyau da za su karfafa lafiyar ‘yan mata da matasa mata. Shirin yana mai da hankali kan wayar da kai kan muhimman batutuwan lafiya kamar kulawar mata masu juna biyu (antenatal care), haihuwa a cibiyoyin lafiya, da kuma tsara tazara tsakanin haihuwa.
Ta kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da shirin a kananan hukumomi shida na Jihar Kano, wato Kano Municipal, Bunkure, Makoda, Dawakin Tofa, Takai da Madobi, inda ake gudanar da wayar da kai da kuma hada kan al’umma.

Zango ta kara bayyana cewa wani muhimmin bangare na shirin shi ne shigar da mutane masu nakasa a matsayin jakadu ko shugabanni a cikin al’ummominsu. Ta ce shirin na kokarin kawar da shinge, yakar kyama da nuna wariya, tare da tabbatar da cewa masu nakasa suna da damar da ta yi daidai wajen shiga harkokin ci gaban al’umma da kuma yanke shawara kan batutuwan lafiya.

Ta bayyana cewa Ranar Mata ta Duniya tana bayar da muhimmiyar dama domin kara bayyana muryoyin mata masu nakasa, wadanda da dama daga cikinsu har yanzu suna fama da wariya da kuma ware su a cikin al’umma.

A cewarta, al’umma mai hada kowa dole ne ta fahimci cewa mata na fuskantar kalubale ta hanyoyi daban-daban, gwargwadon yanayi kamar nakasa, al’ada, shekaru, da kuma asalin zamantakewa.

Don haka Zango ta yi kira ga gwamnatoci, shugabannin al’umma, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki da su inganta manufofin da s**a hada kowa, su karfafa tsarin tallafin al’umma ga mata da ‘yan mata, tare da kalubalantar munanan ra’ayoyi da al’adun da ke takaita damar mata wajen ba da gudummawa ga ci gaban kasa.
Ta jaddada cewa hada kowa cikin al’umma bai kamata a dauke shi a matsayin sadaka ba, sai dai a matsayin muhimmin ginshiki na daidaito da adalci.

Ta ce:
“Karfafa mata masu nakasa na nufin gane hakkokinsu, kara karfin muryoyinsu, da samar musu da damammakin da za su bunkasa rayuwarsu.”Ta kara da cewa hadin gwiwar kowa na da matukar muhimmanci wajen gina al’umma mai hada kowa da kuma adalci.

A karshe, ta bukaci al’ummomi da su yi anfani da wannan rana ta Ranar Mata ta Duniya wajen sabunta kudurinsu na tabbatar da cewa ba a bar wata mace ko yarinya a baya ba a kokarin samar da ci gaba da inganta rayuwar al’umma.

Da Dumi Dumi: Shugaba Tinubu ya dakatar da tsarin biyan kuɗi ba tare da tsabar kuɗi ba na FAAN Laraba, 4 Maris 2026, Shu...
04/03/2026

Da Dumi Dumi: Shugaba Tinubu ya dakatar da tsarin biyan kuɗi ba tare da tsabar kuɗi ba na FAAN Laraba, 4 Maris 2026,


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da tsarin biyan kuɗin haraji ba tare da tsabar kuɗi ba (cashless) da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (Federal Airports Authority of Nigeria – FAAN) ta ƙaddamar a manyan filayen jiragen sama a faɗin ƙasar nan.

A ranar 1 ga Maris, 2026, hukumar ta hana karɓar tsabar kuɗi a ƙofofin biyan kuɗin shiga (toll gates), inda ta tilasta wa direbobi amfani da katin shiga da aka riga aka biya (prepaid access cards) ko hanyoyin biyan kuɗi ta lantarki.

Sai dai lamarin ya rikice, inda fasinjoji da direbobi s**a makale na sa’o’i sakamakon ruɗani da cunkoson ababen hawa mai tsanani da ya biyo bayan fara aiwatar da tsarin.
Wannan ya jawo ƙorafi daga matafiya da s**a bayyana takaicinsu kan rasa jirage da kuma jinkirin ɗaukar su daga filin jirgin sama.
Da yake ganawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ranar Laraba, Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce Shugaban Ƙasa ya amince da dakatar da tsarin.

Ya ce Shugaban Ƙasa ya nuna damuwa kan wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta, inda ya umarci Ma’aikatar da ta koma nazari tare da sake tsara tsarin yadda ya kamata.
Har ila yau, ya bayyana cewa waɗanda s**a riga s**a sayi katinan za su iya ci gaba da amfani da su, tare da ba da damar biyan kuɗi da tsabar kuɗi, har sai Ma’aikatar da hukumomin da abin ya shafa sun fitar da sabon tsari na gaba.

Daga wakilin Daily Trust Baba Martins

SHUGABAN NAHCON, FARFESA ABDULLAHI SALEH, YA YI MURABUS BISA SHAWARAR KANSAFarfesa Abdullahi Saleh ya yi murabus daga mu...
09/02/2026

SHUGABAN NAHCON, FARFESA ABDULLAHI SALEH, YA YI MURABUS BISA SHAWARAR KANSA

Farfesa Abdullahi Saleh ya yi murabus daga muƙaminsa na Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Majiyoyi na kusa da shi sun bayyana cewa wannan mataki da ya ɗauka shawara ce ta kansa gaba ɗaya, wadda ta samo asali ne domin kare da kuma tabbatar da ci gaba mai kyau a ayyukan hukumar ba tare da tangarda ba.

Majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun tabbatar da cewa Farfesa Saleh ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne bayan dogon nazari da tunani mai zurfi, inda s**a jaddada cewa ba kwamitin gudanarwar NAHCON ne ya matsa masa ba, kuma ba wani matsin lamba daga waje da ya tilasta masa yin hakan.

A cewar majiyoyin, tsohon shugaban ya zaɓi ya janye kansa daga wannan matsayi ne da yardar ransa, yana ganin cewa hakan shi ne mafi alheri ga ci gaban da muradun hukumar a wannan lokaci.

Sun ƙara da cewa shawarar Farfesa Saleh ta samo asali ne daga burinsa na ganin NAHCON ta ci gaba da maida hankali kacokan kan ayyukanta na doka, musamman a daidai lokacin da shirye-shiryen aikin Hajjin da ke tafe ke ƙara ɗaukar zafi.

Yayin da ake cikin muhimman matakan tsare-tsare da haɗin gwiwar ayyuka, majiyoyin sun bayyana cewa Farfesan ya ga dacewar yin murabus a matsayin mataki na alhaki, domin kauce wa duk wani abu da zai iya jawo hankalin jama’a ko kawo cikas ga cikar manufar hukumar.

Duk da sauka daga muƙaminsa, an bayyana cewa Farfesa Saleh ya jaddada ƙudirin sa na ci gaba da mara wa tsarin gudanar da aikin Hajji na Nijeriya baya, tare da nuna cikakken goyon baya ga nasarar sa.

Rahotanni sun nuna cewa ya yi alƙawarin ci gaba da aiki tare da hukumomin da s**a dace domin tabbatar da sauyin shugabanci cikin kwanciyar hankali, da kuma dorewar zaman lafiya da daidaito a cikin NAHCON.
Haka kuma, majiyoyin sun bayyana cewa ana ɗaukar matakai domin tabbatar da ci gaba da shugabanci ba tare da tsaiko ba, yayin da masu ruwa da tsaki ke jiran sanarwar hukuma game da wanda zai riƙe muƙamin rikon kwarya ko na dindindin a hukumar.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) na taka muhimmiyar rawa wajen tsara, sa ido da kuma haɗa ayyukan Hajji da Umrah ga Alhazan Nijeriya. Saboda haka, tabbatar da kwanciyar hankali a shugabanci abu ne mai matuƙar muhimmanci, musamman a daidai lokacin da ƙasar ke shirin tunkarar kakar aikin Hajji mai zuwa.

Press Release, KSHCCODE OF CONDUCT BUREAU TAKES SENSITIZATION DRIVE TO KSHC, STRENGTHENS CULTURE OF INTEGRITY AND ACCOUN...
05/02/2026

Press Release, KSHC

CODE OF CONDUCT BUREAU TAKES SENSITIZATION DRIVE TO KSHC, STRENGTHENS CULTURE OF INTEGRITY AND ACCOUNTABILITY

The Code of Conduct Bureau (CCB) has carried out a sensitization and enlightenment visit to the Kano State Housing Corporation (KSHC) as part of its sustained efforts to promote ethical conduct, transparency, and accountability among public servants. The visit was designed to deepen awareness and understanding of the Code of Conduct for Public Officers and to strengthen compliance with constitutional and statutory obligations in the public service
The sensitization exercise focused on educating staff of the Corporation on the mandate, roles, and core activities of the Code of Conduct Bureau, with particular emphasis on the proper completion, submission, and verification of Assets Declaration Forms as required by law. Officials of the Bureau provided comprehensive explanations on categories of public officers mandated to declare assets, the timelines for declaration—upon assumption of office, periodically as prescribed, and at the end of service—as well as the legal consequences of non-compliance, late submission, or false declaration.

Speaking during the session, the Head of the Code of Conduct Bureau, Hajiya Larai Ibrahim, represented by Mohd Ibrahim Khalifa, stressed that the Bureau’s mandate is not to witch-hunt public officers but to guide, enlighten, and support them in upholding integrity, probity, and adherence to the rule of law in the discharge of their official responsibilities. He explained that asset declaration is a constitutional requirement intended to promote transparency, deter corrupt practises, and strengthen public confidence in government institutions.

Participants were further taken through an in-depth and practical session by the Legal Officer of the Bureau, Barrister Atika Abdullahi Idris, who presented a step-by-step guide on how to correctly complete the Assets Declaration Forms. She highlighted common mistakes often made by public officers, outlined best practices to ensure accuracy, and explained the procedures for submission, verification, and record-keeping.

The session was highly interactive, providing staff of KSHC the opportunity to ask questions and seek clarifications on grey areas related to asset declaration and ethical obligations. These concerns were clearly and satisfactorily addressed by officials of the Bureau, thereby enhancing participants’ understanding and confidence in complying with the requirements

Officials of the Code of Conduct Bureau explained that the visit forms part of its ongoing nationwide sensitization campaign aimed at deepening awareness of ethical standards, promoting accountability, and entrenching a culture of integrity across public sector institutions at all levels of government.
In his remarks, the Managing Director of the Kano State Housing Corporation, Alh. Abdullahi Rabiu, represented by the Deputy Managing Director, Engr. Isyaku Umar Kwa, expressed appreciation to the Code of Conduct Bureau for the timely and impactful sensitization visit. He described the engagement as a welcome development that would further enhance compliance, professionalism, and ethical standards within the Corporation.

He assured the CCB delegation of the management’s firm commitment to ensuring that all staff of the Corporation fully comply with the provisions of the Code of Conduct for Public Officers and other relevant regulations guiding public service operations. Alh. Abdullahi Rabiu further reiterated that the Kano State Housing Corporation remains steadfast in its commitment to the principles of transparency, accountability, and good governance, as championed by the administration of His Excellency, Engr. Abba Kabir Yusuf, the Executive Governor of Kano State. He urged staff to take the sensitization exercise seriously and to apply the knowledge gained in the effective and ethical discharge of their daily duties.

Signed:
Ismail Garba Gwammaja, ANIPR
Director, Public Enlightenment
Kano State Housing Corporation (KSHC)

Congratulations!!!Invitation for the Induction Ceremony
05/02/2026

Congratulations!!!
Invitation for the
Induction Ceremony

NSCDC TA DORA AIKIN TSARO A KAN SHIGA GA KOWA DA KOWA DOMIN INGANTA TSARO, HAKA KUMA TA KADDAMAR DA MANUFAR JINSI TA BIY...
03/02/2026

NSCDC TA DORA AIKIN TSARO A KAN SHIGA GA KOWA DA KOWA DOMIN INGANTA TSARO, HAKA KUMA TA KADDAMAR DA MANUFAR JINSI TA BIYU WATO (GENDER POLICY II)

Hukumar Tsaron Farar Hula ta Nijeriya (NSCDC) ta kaddamar da Manufar Jinsi ta Biyu (Gender Policy II), inda ta dora tsarin isar da tsaro a kan shiga kowa da kowa, tare da sake jaddada kudurinta na kwarewa da aiki mai mayar da hankali ga jama’a.

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar da aka gudanar a Abuja, Babban Kwamandan Hukumar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, MNI, OFR, ya bayyana cewa shirin shiga ga kowa da kowa nada mutitqar muhimmin cin gaske don gina hukuma mai ƙarfi, inganci kuma abin amincewa domi samun nasarar aikin.

Ya kara da cewa wannan manufa ta dace da kyawawan ka’idojin duniya da kuma manufofin tsaron kasa. Farfesa Audi, wanda ya wakilci Ministan Harkokin Mr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce manufar za ta ƙarfafa ƙarfin hukuma, ta inganta ingancin ayyuka, tare da jagorantar ma’aikata su aiwatar da aikinsu cikin mutunci,l da kulawa da girmama haƙƙin ɗan Adam.

Taron, wanda UKFIDO da SPRING s**a tallafa, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, abokan hulɗar ci gaba da ƙungiyoyin farar hula.

Masu jawabi daban daban sun jaddada cewa tsaro mai haɗa kowa da kowa na ƙara gaskiya da ɗaukar alhaki, kare masu rauni, tare da ƙara amincewar jama’a. An Kaddamar da Manufar Jinsi ta Biyu ta nuna ƙudurin NSCDC na bin UNSCR 1325, kuma ta zama muhimmin mataki a ƙoƙarin hukumar na daidaita shiga kowa da kowa, adalci da kwarewa a dukkan ayyukanta.

ACC Babawale Afolabi, ANIPR
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kasa
Hukumar Tsaron Farar Hula ta Nijeriya

Address

Abuja
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DMM Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category