01/10/2025
Fede Valverde ya mayar da martani kan jita-jitar da ake yadawa 🤍🇺🇾
Ɗan wasan Real Madrid, Fede Valverde, ya fitar da sanarwa inda ya karyata jita-jitar da ake yadawa game da rashin jajircewarsa ga kulob.
Valverde ya ce ya karanta wasu labarai da s**a lalata sunansa, inda ya amince cewa ya taɓa yin wasanni marasa kyau, amma ya bayyana cewa yana fuskantar s**a kai tsaye ba tare da boyewa ba.
“Ina jin baƙin ciki sosai, amma ba za a taɓa cewa na ƙi yin wasa ba. Na bayar da komai saboda wannan kulob, har ma na yi wasa ina da rauni ko karyewa ba tare da yin gunaguni ko neman hutu ba,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa da koci, wanda hakan ke ba shi damar nuna wane matsayi yake fi so a fili, amma duk da haka yana nan a shirye ya taka ko ina ake bukata.
“Na bar zuciyata da raina a wannan kulob, kuma zan ci gaba da yin hakan, ko da wani lokaci abin bai isa ba ko kuma ban taka yadda nake so ba,” Valverde ya ƙara da cewa.
A ƙarshe, ɗan wasan ya rantse da mutuncinsa cewa ba zai taɓa daina gwagwarmaya ba, yana mai cewa: “Zan yi yaki har zuwa ƙarshe, in taka duk inda ake bukata.”