MAZAN JIYA

MAZAN JIYA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MAZAN JIYA, Grocers, Giade Local Government, .

Alhaji Musa Ɗan Kwairo — Gwarzon Mawakin Gargajiya na HausaAn haifi Alhaji Musa Ɗan Kwairo a garin Bakura, Jihar Zamfara...
17/04/2026

Alhaji Musa Ɗan Kwairo — Gwarzon Mawakin Gargajiya na Hausa

An haifi Alhaji Musa Ɗan Kwairo a garin Bakura, Jihar Zamfara, a farkon shekarun 1909. Tun yana ƙarami ya nuna baiwar fasaha da ƙaunar kiɗan gargajiya, abin da ya kai shi zama ɗaya daga cikin fitattun mawakan Hausa a tarihi.

Musa Ɗan Kwairo ya taka muhimmiyar rawa wajen adanawa da yaɗa al’adun Arewa ta hanyar kiɗa. Wakokinsa sun haɗa sauti mai armashi da hikima, suna taɓo batutuwa kamar sarauta, jarumta, soyayya, haɗin kai da kuma darussa na rayuwa.

Ya yi amfani da kayan kiɗan gargajiya kamar kotso, tare da salon rerawa mai ɗauke da labari da jan hankali. Wannan ya sa wakokinsa s**a zama abin so ga al’umma daga kowane ɓangare.

Daga cikin fitattun wakokinsa akwai:
Mai Dubun Nasara, Yan Arewa, Sarkin Daura, Noma Babar Sana’a, Ahmadu Bello Sardauna, Ado Bayero da sauransu.

Musa Ɗan Kwairo ya samu girmamawa da lambobin yabo da dama saboda gudunmawarsa ga al’adu da kiɗan Hausa.

Ya rasu a ranar 3 ga Satumba, 1991, amma tarihinsa da wakokinsa na ci gaba da rayuwa a zukatan mutane har yau.

Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa. 🤲

17/04/2026
Fadar Shugaban Kasa: ADC Ce Zata Karbi Mulki a 2027, Inji OyegunTsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Chief John Odigie...
16/04/2026

Fadar Shugaban Kasa: ADC Ce Zata Karbi Mulki a 2027, Inji Oyegun

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Chief John Odigie-Oyegun, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC (African Democratic Congress) tana shirya kanta ne domin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma karbe iko da fadar shugaban kasa ta A*o Rock a babban zaben shekarar 2027.
Oyegun ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a babban taron kasa na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa kan shirin da jam’iyyar ADC take da shi na karbar ragamar mulki a matakin tarayya.
“Mun shirya tsaf domin karbe fadar A*o Rock, kuma hakan ba zai zama tamkar yadda aka saba ba,” in ji Oyegun.
“Ina so kowa ya sani, domin suna ta zarginmu cewa 'John, ai kana daya daga cikinsu' (wato yana cikin tafiyar gwamnati mai ci).”
Tsohon gwamnan jihar Edo ya koka kan yadda Najeriya take da dumbin arzikin kasa amma kuma yan kasar ke fuskantar matsanancin hali.
Ya bayyana wannan yanayi a matsayin gazawar shugabanci da aka samu tsawon shekaru.

Allah ya jikan Aliyu Namangi... Ashe Shima ya hango irin wannan yanayi, ya kuma yi wa'azi ta sigar Waka.. Allah yayi man...
16/04/2026

Allah ya jikan Aliyu Namangi... Ashe Shima ya hango irin wannan yanayi, ya kuma yi wa'azi ta sigar Waka.. Allah yayi mana magani

⭕️Ya ilahal-Arshi gamu,
Yara Har Tsoffin cikimmu,
Duk Takaici ya Ishe Mu,
Ga ana faman kashe Mu,
Ba'a girmama tamu Rayuwa ba.
😭😭😭
⭕️Yau Arewa Maza da Mata,
Kuntatarmu tana yawaita,
Ga Musifu sun tsawaita,
Ga Shi kowa ya Kawaita,
Ba mu San Manufar Ubangiji ba!
😭😭😭
⭕️Mun zamo Guiwa a sare,
Kowanemmu Ido a zare,
Ko ana so ne mu k'are?
Namu Tarihi a share,
Tamkar ba'a yi mu Yan Adam ba!
😭😭😭
⭕️Rabbi ga Kukammu mun Kai,
Tunda ba me jimmu sai Kai,
Me isar Daukar matakai,
Zul-jalali ka ba mu jin-kai,
Kai ne Gatammu ba Mutum ba!
😭😭😭

~Aliyu Namangi
Kamar yau ne yake wannan waqe😭

Marigayi Sarkin Kano Alhaji (Dr) Ado Bayero.Allah ya kyautata kwanciya.Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa kurak...
15/04/2026

Marigayi Sarkin Kano Alhaji (Dr) Ado Bayero.
Allah ya kyautata kwanciya.

Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa kurakuransa, ya sa Aljannah ce makomarsa. Amin.

Muma Innamu Ajalin Yazo Allah Yasa Mucika
Da kyau Da Imani 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Yaune ranar Harshen uwa ta duniya. Wace kalma ce tafi saukin fada a yarenku??
15/04/2026

Yaune ranar Harshen uwa ta duniya. Wace kalma ce tafi saukin fada a yarenku??

An ɗauka wannan hoton cikin shekarar 1989 a Arewacin Kasar nan, Hoton yana Nuni da Yadda ake Auna Nauyin Nono Bayan An t...
15/04/2026

An ɗauka wannan hoton cikin shekarar 1989 a Arewacin Kasar nan, Hoton yana Nuni da Yadda ake Auna Nauyin Nono Bayan An tatso shi, Kuna Iya Lura Da wata Mata Zaune Rike da Abun Rubuta tana Rubutu adadin Nauyi kilo da Nono yayi.

Wai shin, har Yanzu kuwa, a kan auna nauyin nono, bayan an tatse shi, sannan a rubuta nauyinsa kafin a kai kasuwa.👇

Anyi Amfani da fasahar Zamani wajen gyara hoton Ku Duba comments section 👇

Alhaji Dr. Abubakar Imam shahararren marubucin kasar hausa kenan marubucin littafin 'MAGANA JARI CE'. Wanda ya taimaka w...
15/04/2026

Alhaji Dr. Abubakar Imam shahararren marubucin kasar hausa kenan marubucin littafin 'MAGANA JARI CE'. Wanda ya taimaka wajen samar da jaridar Hausa ta farko a duniya mai suna 'Gaskiya ta fi kwabo' a shekarar 1939.

Shi ne editan farko na wannan jaridar. Ya bada kyakkyawar gudummawa wajen yada al'adun hausawa tare yada shi kansa yaren ta hanyar yin rubuce rubuce masu yawa.

Fata Allah ya yi masa rahama.

Fadar Sarkin Bauchi Cikin Shekarar 1964 Kamar yadda Eric Chicago ya sanar damu. Ai Kun tuna sunan waɗannan motocin ko?Ba...
15/04/2026

Fadar Sarkin Bauchi Cikin Shekarar 1964 Kamar yadda Eric Chicago ya sanar damu. Ai Kun tuna sunan waɗannan motocin ko?

Barka da Dare

An ɗauki wannan hoto jim kaɗan bayan karɓar 'yancin Kan Nigeria, 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960.
15/04/2026

An ɗauki wannan hoto jim kaɗan bayan karɓar 'yancin Kan Nigeria, 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960.

Firaminista Tafawa Balewa yayin ziyarar sojan ƙasar nan da aka girke a Congo, ranar 12 ga watan Satumba na shekarar 1963...
15/04/2026

Firaminista Tafawa Balewa yayin ziyarar sojan ƙasar nan da aka girke a Congo, ranar 12 ga watan Satumba na shekarar 1963.

Address

Giade Local Government

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MAZAN JIYA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Grocery Store?

Share