Tarjamar Alƙur'ani Mai girma da harshen Hausa

Tarjamar Alƙur'ani Mai girma da harshen Hausa Kano

🌹💖 DUK WANDA YA BI MANZO (ﷺ), TO HAƘIƘA YA BI ALLAH… 💖🌹Ya ɗan uwana, Kar ka ƙosa, Ka karanta har zuwa ƙarshe: “Da zuciya...
15/04/2026

🌹💖 DUK WANDA YA BI MANZO (ﷺ), TO HAƘIƘA YA BI ALLAH… 💖🌹

Ya ɗan uwana, Kar ka ƙosa, Ka karanta har zuwa ƙarshe: “Da zuciya mai nuna soyayya da ƙauna da kuma shauƙi...”
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
1.
Soyayyar Annabi Muhammad (ﷺ) ita ce ginshiƙin cikar imani; domin imani ba ya kammala sai an fifita shi sama da kowa.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
2.
Ƙaunarsa (ﷺ) ba magana ce kawai ba; tana tabbata ne ta hanyar bin sunnarsa da aikata abin da ya koyar da zuciya ɗaya da ikhlasi.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
3.
Duk wanda ya san darajar Annabi (ﷺ), zuciyarsa ba za ta iya rayuwa cikin salama ba tare da ƙaunarsa ba.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
4.
Soyayyarsa (ﷺ) hanya ce zuwa samun yardar Allah, domin biyayya gare shi ita ce biyayya ga Ubangiji.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
5.
Nazari mai zurfi a kan rayuwar Annabi (ﷺ), fahimtar Sīrarsa, da zurfafa bincike a Hadisansa yana gina ƙauna bisa ilimi da hujja; wannan ita ce ƙauna ta gaskiya wacce ke tabbata a zuciya har abada.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
6.
Salati a gare shi (ﷺ) yana tsarkake zuciya, yana buɗe ƙofofin rahama da albarka daga Allah.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
7.
Soyayyar Annabi (ﷺ) tana hana mutum aikata saɓo, domin zuciya mai ƙauna tana jin kunyar saɓa wa masoyinta.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
8.
Duk wanda ya fi son Annabi (ﷺ) fiye da kansa da duk abin da yake mallaka, ya kai kololuwar matsayi na soyayya ta gaskiya.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
9.
Tausayinsa (ﷺ) ga al’umma hujja ce ta ƙaunarsa; ya jure wahala da ƙunci domin mu samu shiriya da tsira.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
10.
Ƙaunarsa (ﷺ) tana haifar da ladabi, biyayya, da girmamawa ga dukkan abin da ya zo da shi.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
11.
Bin sunnarsa (ﷺ) yana gyara rayuwa, yana kuma kawo daidaito tsakanin zuciya, magana, da aiki.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
12.
Soyayyarsa (ﷺ) tana cika zuciya da nutsuwa, tana kawar da damuwa da ruɗani.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
13.
Yawaita ambatonsa (ﷺ) yana cika zuciya da haske, yana kuma kawo albarkar rayuwa.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
14.
Ƙaunarsa (ﷺ) tana haɗa zukatan muminai, tana kawar da hassada da ƙiyayya tsakanin su.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
15.
Sanin sunayensa da siffofinsa (ﷺ) yana ƙara zurfin ƙauna da fahimta a zuciya.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
16.
Soyayyar Annabi (ﷺ) tana koya wa mutum haƙuri da juriya a lokacin jarabawa.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
17.
Duk wanda ya kare mutuncinsa (ﷺ) da harshensa da aikinsa, ya nuna gaskiyar ƙaunarsa.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
18.
Ƙaunarsa (ﷺ) tana motsa mutum ya kwaikwayi halayensa na gaskiya, amana, tawali’u da adalci.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
19.
Soyayyarsa (ﷺ) tana zama haske a kabari, da kuma ceton mutum a ranar alƙiyama.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
20.
Bin koyarwarsa (ﷺ) yana tabbatar da nasara da rabauta a duniya da lahira.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
21.
Ƙaunarsa (ﷺ) tana tsarkake zuciya daga riya, tana kuma rage son duniya mai yaudara.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
22.
Duk wanda ya rayu da ƙaunar Annabi (ﷺ), dukkan rayuwarsa tana zama ibada mai ma’ana.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
23.
Soyayyar Annabi (ﷺ) ita ce mafificiyar ƙauna, wacce take kai bawa zuwa Aljannar Firdausi cikin rahamar Allah.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
✍️ Auwal Aliyu Sara (A.A. Sara) 🌹💚

05/09/2025

MUMINI MAI ƘARFI...

Matanin Hadisi da Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ: «الْمُؤْمِنُ القَوِيُّ خَيْرٌ وَأَحَبّ إِلَى اللَّهِ مِنَ المُؤْمِنِ الضَّعِيفِ، وَفِي كُلٍّ خَيْرٌ، احْرِصْ عَلَى مَا يَنْفَعُكَ، وَاسْتَعِنْ بِاللَّهِ وَلَا تَعْجَزْ، وَإِنْ أَصَابَكَ شَيْءٌ فَلَا تَقُلْ: لَوْ أَنِّي فَعَلْتُ كَذَا كَانَ كَذَا وَكَذَا، وَلَكِنْ قُلْ: قَدَّرَ اللَّهُ وَمَا شَاءَ فَعَلَ، فَإِنَّ (لَوْ) تَفْتَحُ عَمَلَ الشَّيْطَانِ» رَوَاهُ مُسْلِمٌ

Tarjama da Hausa:
An karɓo daga Sayyidina Abu Hurairah (Allah Ya ƙara yarda a gare shi) ya ce: Manzon Allah ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) ya ce: “Mumini mai ƙarfi ya fi alheri, kuma ya fi soyuwa a wurin Allah, fiye da mumini mai rauni. Amma duka biyun akwai alheri a cikinsu. Ka dage wajen abin da zai amfane ka, ka nemi taimakon Allah, kada ka zama mai rauni. Idan wani abu ya same ka, kada ka ce: “Da na yi kaza, da ya kasance kaza.” Sai dai ka ce: “haka Allah Ya ƙaddara, kuma abin da Ya so Shi yake aikatawa.” Domin kalmar “da na...” tana buɗe aikin shaiɗan.” Sahihu Muslim: #2664

Darussa daga wannan Hadisi Mai albarka:

1️⃣ Ƙarfafa Imani da Ƙoƙari:
– Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Ya nuna cewa mumini mai ƙarfi ya fi soyuwa a wurin Allah, domin yana da ƙarfin zuciya, ƙarfin jiki, da ƙarfin nufi wajen yin ayyukan alheri.

2️⃣ Kowane Mumini Akwai Alheri a tare da shi:
– Ko mai ƙarfi ko mai rauni, dukansu suna da alheri. Amma ana ƙarfafa mu mu nemi matsayin da yafi inganci.

3️⃣ Dagewa kan Abu mai Amfani:
– Musulmi ya kamata ya rike abin da zai amfane shi a addini da duniya, kada ya ɓata lokaci a abubuwan shirme.

4️⃣ Dogaro ga Allah:
– Wajibi ne mu nemi taimakon Allah a kowane hali, mu guji dogaro da kanmu kawai.

5️⃣ Gujewa Rauni da Kasala:
– Hadisin ya ƙarfafa musulmi kada ya zama rauni ko mai kasala wajen yin ayyukan alheri da neman halali.

6️⃣ Yarda da Ƙaddarar Allah:
– Idan wani abu ya faru, kada mutum ya yi nadama ya ce “da na yi kaza…”, sai dai ya yarda cewa duk abin da ya faru ƙaddarar Allah ne.

7️⃣ Kariya daga Shaiɗan:
– Kalmar “da na…” tana buɗe ƙofa ga shaiɗan, saboda tana kawo bakin ciki da damuwa, tana hana mutum yarda da ƙaddara.

✍️ Rubutawa: Auwal Aliyu Sara (A.A. Sara)

30/01/2025

Idan mata ba su bi umarnin da aka wajabta musu na suturce jiki ba, to su ma fa maza su sani cewa; “ba a ɗauke umarnin da aka wajabta musu na runtse gani ba.”

SURATUL ADIYAT (1-11)بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِوَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا ١ فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا ٢ فَٱلۡمُغِي...
20/01/2025

SURATUL ADIYAT (1-11)
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا ١ فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا ٢ فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحٗا ٣ فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعٗا ٤ فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا ٥ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٞ ٦ وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ ٧ وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ ٨ ۞أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ ٩ وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ ١٠ إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ ١١

Tarjama:
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Na rantse da (dawaki) masu sukuwa suna kukan ciki.
2. Sannan masu bugun ƙyastu da kofatai.
3. Sannan masu kai hari da asuba.
4. Sai s**a tayar da ƙura da ita (s**awar tasu).
5. Sai kuma s**a shiga tsakiyar taro (da mahayansu)
6. Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne ga Ubangijinsa.
7. Lalle kuma shi shaida ne a kan haka.
8. Lalle shi kuma mai tsananin son alheri ne.
9. Shin bai sani ba ne idan aka bankaɗo abubuwan da suke cikin ƙaburbura?
10. Aka kuma tattaro abubuwan da suke cikin ƙiraza?
11. Lalle a wannan ranar tabbas Ubangijinsu Masani ne game da su.

TSAKURE...Daga “Tafsirin Fayyataccen Bayani na Ma'anoni da Shiriyar AlQur'ani” na Shaihun Malami: Professor Muhammad San...
16/01/2025

TSAKURE...

Daga “Tafsirin Fayyataccen Bayani na Ma'anoni da Shiriyar AlQur'ani” na Shaihun Malami: Professor Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo (Hafizahullah).

Tarjama da tafsirin Aya ta (82-85) na Suratul Ghafir:

بِسْـــمِ اللٌّهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِنۡهُمۡ وَأَشَدَّ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ ٨٢ فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرِحُواْ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ ٨٣ فَلَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَا قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥ وَكَفَرۡنَا بِمَا كُنَّا بِهِۦ مُشۡرِكِينَ ٨٤ فَلَمۡ يَكُ يَنفَعُهُمۡ إِيمَٰنُهُمۡ لَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَاۖ سُنَّتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي قَدۡ خَلَتۡ فِي عِبَادِهِۦۖ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡكَٰفِرُونَ ٨٥
Tarjama:
82. Shin ba za su yi tafiya ba a bayan ƙasa sannan su duba yadda ƙarshen waɗanda suke gabaninsu ya zama? Sun zamanto sun fi su yawa, sun kuma fi su tsananin ƙarfi da barin gurabe a bayan ƙasa; to abin da s**a kasance suna aikatawa bai wadatar musu da komai ba.
83. Sannan lokacin da manzanninsu s**a zo musu da (ayoyi) bayyanannu, sai s**a nuna farin ciki da ilimin da ke gare su, abin kuma da s**a kasance suna yi wa izgili ya saukar musu.
84. To lokacin da s**a ga azabarmu sai s**a ce: “Mun yi imani da Allah Shi kaɗai, mun kuma kafirce wa abin da muka kasance muna yin shirka da shi.”
85. To imaninsu bai zamanto zai amfane su ba yayin da s**a ga azabarmu; wannan sunna ce ta Allah wadda ta shuɗe a kan bayinsa. Kafirai kuma sun yi asara a nan.

Tafsiri:
A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana daɗa jan kunnen masu ƙaryata ayoyinsa ne don neman wani abin duniya, kamar dukiya ko matsayi ko kuma don nuna girman kai da tsaurin ido, da cewa su yi yawo a bayan ƙasa mana don su gane wa idanunsu yadda ƙarshen al’ummun da s**a gabace su ya kasance bayan sun ƙaryata manzanninsu; su ga yadda Allah ya yi da su, don su ɗauki izina da wa’azi daga gare su. Waɗannan al’ummu sun fi su yawa da tarin dukiya, sun fi su ƙarfi, sun kuma fi su motsa ƙasa domin gine-gine da noma, to amma abin da s**a kasance suna aikatawa bai wadatar da su da komai ba yayin da azabar Allah ta zo musu.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babban laifinsu wanda ya jawo musu azabarsa, watau lokacin da manzanninsu s**a je musu da hujjoji bayyanannu sai s**a bijire s**a ƙaryata su, s**a ƙi amincewa da su, s**a ci gaba da ƙanƙame ilimin da suke tinƙaho da shi wanda ya saɓa wa na manzanninsu, sai azabar Allah wadda suke yi wa izgili ta saukar musu ta hallaka su.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da s**a ga azabarsa ta tunkaro su gadan-gadan sai s**a yi fargar-jaji s**a gane kuskurensu, s**a furta cewa, sun yi imani da Allah shi kaɗai, sun kafirce wa duk abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba.
A ayar ƙarshe ta wannan Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa imanin kafirai a wannan lokaci bayan sun ga azabar Allah ba zai yi musu wani amfani ba. Wannan kuwa sunnar Allah ce wadda ta riga ta shuɗe yake zartar da ita cikin bayinsa na cewa, imani ba zai yi amfani ba bayan azaba ta riga ta sauka. Kafirai kuwa sun yi mummunar asara da s**a bari har azabar Allah ta zo musu ba su tuba sun koma gare shi ba.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Yawan jama’a da tarin dukiya da tsananin ƙarfi, ba zai kare mutum daga azabar Allah ba idan har ta zo masa bai tuba ba.
2. Haɗarin yin farin ciki da ƙarya da mummunan sakamakon wanda ya yi haka.
3. Girman haɗarin da ke tattare da alfahari da amincewa da duk wani ilimi da ya ci karo da ilimin da manzannin Allah s**a zo da shi, kamar ilimin da aka kafa shi a tushen kore samuwar Allah, ko kafirce wa Allah mahalicci, da ilimin tsafe-tsafe da na duba da bokanci, da duk wani ilimi da ke ɗauke da da’awar sanin gaibu.
4. Imanin kafiri ba ya inganta bayan ya ga saukar azabar Allah, wannan ba zai tserar da shi daga wannan azabar ba.

أَدُّئَـرْ تَـفِـيَـرْ دَ قُـنْـثِـنْ زُوثِـيَـااللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُو، فَلَا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَ...
11/01/2025

أَدُّئَـرْ تَـفِـيَـرْ دَ قُـنْـثِـنْ زُوثِـيَـا

اللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُو، فَلَا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ.

مَـئَـنَـا:
يَا أَللَّهْ! رَحَمَرْكَ نَكِيٰ قَوْنَا، دُوْنْ هَكَ كَرْ كَ قَيىٰلِيٰ نِ دَ كَيْنَا كُوْ دَ قِفْتَىٰوَرْ إِدُوْ نِيٰ كَ كَيوْتَتَا مِنِ شَئَنِينَا دُكَّنْسَ؛ ”بَىٰبُ أَبِنْ بَوْتَىٰوَا دَ غَسْكِيَا سَيْ كَيْ.“

SURATUL JATHIYAH (27-29)بِسْـــمِ اللَّـــهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِوَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱ...
05/01/2025

SURATUL JATHIYAH (27-29)

بِسْـــمِ اللَّـــهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِ
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَخۡسَرُ ٱلۡمُبۡطِلُونَ ٢٧ وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٖ جَاثِيَةٗۚ كُلُّ أُمَّةٖ تُدۡعَىٰٓ إِلَىٰ كِتَٰبِهَا ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ٢٨ هَٰذَا كِتَٰبُنَا يَنطِقُ عَلَيۡكُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّا كُنَّا نَسۡتَنسِخُ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ٢٩

Ma'ana:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
27. Mulkin sammai da ƙasa kuma na Allah ne. Kuma ranar da alƙiyama za ta tashi, a wannan ranar maɓarnata za su yi asara.
28. Za kuma ka ga kowace al’umma a durƙushe, kowace al’umma ana kiran ta zuwa ga littafinta, a wannan rana ne za a saka muku abin da kuka kasance kuna aikatawa.
29. (Za a ce da su): “Wannan Littafinmu ne da yake yi muku furuci da gaskiya. Lalle Mu mun kasance Muna rubuta abin da kuka kasance kuna aikatawa.”

YA ƳAN UWANA! KU ZO MU LEƘA ALJANNAR UBANGIJINMUSURATUR RAHMAN (46-61)بِسْـــمِ اللَّـــهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرّ...
04/01/2025

YA ƳAN UWANA! KU ZO MU LEƘA ALJANNAR UBANGIJINMU

SURATUR RAHMAN (46-61)

بِسْـــمِ اللَّـــهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِ
وَلِمَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ جَنَّتَانِ ٤٦ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٧ ذَوَاتَآ أَفۡنَانٖ ٤٨ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٩ فِيهِمَا عَيۡنَانِ تَجۡرِيَانِ ٥٠ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥١ فِيهِمَا مِن كُلِّ فَٰكِهَةٖ زَوۡجَانِ ٥٢ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٣ مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ فُرُشِۭ بَطَآئِنُهَا مِنۡ إِسۡتَبۡرَقٖۚ وَجَنَى ٱلۡجَنَّتَيۡنِ دَانٖ ٥٤ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٥ فِيهِنَّ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ ٥٦ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٧ كَأَنَّهُنَّ ٱلۡيَاقُوتُ وَٱلۡمَرۡجَانُ ٥٨ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٩ هَلۡ جَزَآءُ ٱلۡإِحۡسَٰنِ إِلَّا ٱلۡإِحۡسَٰنُ ٦٠ فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٦١

Ma'ana:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
46. Duk wanda kuwa ya ji tsoron tsayuwa (gaban) Ubangijinsa yana da Aljanna biyu.
47. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
48. Ma’abota rassan bishiyoyi.
49. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
50. A cikinsu akwai idanuwa (na ruwa) guda biyu masu gudana.
51. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
52. A cikinsu akwai (dangi) biyu na kowane abin marmari.
53. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
54. Suna kishingiɗe a kan shimfiɗu da shafin cikinsu na kakkauran alhariri ne. Kuma ‘ya’yan bishiyoyin Aljannatai biyun kusa suke (da kowa).
55. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
56. A cikinsu akwai (mata) masu taƙaita kallo (ga mazajensu, waɗanda) wani mutum ko aljan bai taɓa shafar su ba a gabaninsu.
57. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
58. Kai ka ce su yaƙutu ne da murjani.
59. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
60. Shin akwai wani sakamako na kyautatawa in ba kyautatawa ba?
61. Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?

SURATU ƊAHA (105-112)بِسْـــمِ اللٌّهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِوَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡجِبَالِ فَقُلۡ ...
03/01/2025

SURATU ƊAHA (105-112)

بِسْـــمِ اللٌّهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِ
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡجِبَالِ فَقُلۡ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسۡفٗا ١٠٥ فَيَذَرُهَا قَاعٗا صَفۡصَفٗا ١٠٦ لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجٗا وَلَآ أَمۡتٗا ١٠٧ يَوۡمَئِذٖ يَتَّبِعُونَ ٱلدَّاعِيَ لَا عِوَجَ لَهُۥۖ وَخَشَعَتِ ٱلۡأَصۡوَاتُ لِلرَّحۡمَٰنِ فَلَا تَسۡمَعُ إِلَّا هَمۡسٗا ١٠٨ يَوۡمَئِذٖ لَّا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَرَضِيَ لَهُۥ قَوۡلٗا ١٠٩ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِۦ عِلۡمٗا ١١٠ ۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا ١١١ وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا يَخَافُ ظُلۡمٗا وَلَا هَضۡمٗا ١١٢

Ma'ana:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
105. Suna kuma tambayar ka game da duwatsu, to ka ce (da su): “Ubangijina zai niƙe su tilis.
106. “Sannan Ya bar ta (wato ƙasar) fili fetal.
107. “Ba za ka ga wani kwari ko tudu a kanta ba.”
108. A wannan rana ne za su bi mai kira (zuwa matattara), ba mai bauɗe masa; kuma (duk) muryoyi su yi ƙasa-ƙasa saboda (girman Allah) Mai rahama, sannan ba za ka ji (komai) ba sai raɗa.
109. A wannan ranar ceto ba ya amfani sai ga wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, kuma Ya yarda da maganarsa.
110. (Allah) Yana sane da abin da yake gaba gare su (na ranar alƙiyama) da kuma abin da yake bayansu (na ayyukan da s**a yi a duniya), su kuwa ba za su kewaye da saninsa ba.
111. Kuma dukkanin fuskoki s**a ƙasƙanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haƙiƙa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya taɓe.
112. Duk kuma wanda yake yin aiki na gari alhali kuwa shi mumini ne, to ba zai ji tsoron zalunci ba ko kuma ƙwauro.

SURATUL ƘASAS (84-88)بِسْـــمِ اللَّـــهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِمَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡ...
02/01/2025

SURATUL ƘASAS (84-88)

بِسْـــمِ اللَّـــهِ الـــرَّحْـــمَـٰــنِ الـــرَّحِـــيـــمِ
مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ٨٤ إِنَّ ٱلَّذِي فَرَضَ عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٖۚ قُل رَّبِّيٓ أَعۡلَمُ مَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ وَمَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ ٨٥ وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ ٨٦ وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بَعۡدَ إِذۡ أُنزِلَتۡ إِلَيۡكَۖ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ٨٧ وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ ٨٨

Ma'ana:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
84. Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waɗanda s**a aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da s**a kasance suna aikatawa.
85. Lalle Wanda Ya saukar maka da Alƙur’ani tabbas zai mayar da kai zuwa makoma. Ka ce: “Ubangijina Shi Ya san wanda ya zo da shiriya da kuma wanda yake cikin ɓata mabayyani.”
86. Kuma ba ka kasance kana fatan a saukar maka da littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka; to don haka kada ka zamanto mai taimakon kafirai.
87. Kuma lallai kada su hana ka (isar da) ayoyin Allah bayan an riga an saukar maka da su; kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka; kuma lallai kada ka zamanto daga mushrikai.
88. Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku.

CUTAR DA MAƘWABCI...Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare Shi) Ya ce:«Cutar da maƙwabci yana shafe...
29/12/2024

CUTAR DA MAƘWABCI...

Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare Shi) Ya ce:
«Cutar da maƙwabci yana shafe kyawawan ayyuka, kamar yadda rana take shafe (hasken) fata».
As-Silsilatus Sahiha (6/1264)

Address

Dorayi Karama
Kano
3678

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tarjamar Alƙur'ani Mai girma da harshen Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category