Mika'il

Mika'il Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mika'il, Grocers, Indabawa, Kano.

11/08/2025
11/08/2025

mk

10/08/2025

Abubuwa guda biyar da bai kamata saurayi da budurwa su yi ba.

1. Yin Hira da Juna a Sirrince

Saurayi da budurwa ba su da aure tsakaninsu, don haka yin hira da juna a sirri ko zama su biyu kawai haramun ne. Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Babu wani namiji da zai yi shisshigi da wata mace sai Shaiɗan ya zama na uku.”
— Tirmidhi
Hakan yana iya janyo fadawa cikin haram, zubar da mutunci, da rugujewar tarbiyya.

2. Taɓa Juna
taɓa juna, runguma, ko sumbata duk zina ce ta ido da hannu. Allah ya hana kusantar zina.
“Kada ku kusanci zina, lallai ita alfasha ce kuma mummunan hanya.”
— Suratul Isra’i: 32
Soyayya tsakanin saurayi da budurwa kafin aure yawanci tana kaiwa ga irin waɗannan laifukan.

3. Musayar Hotuna da Bidiyo Masu Kawo Sha’awa.
musayar hotuna, musamman waɗanda ke bayyana jiki ko da ɗan kadan, haramun ne. Hakan na iya tayar da sha’awa, ya kai ga zina ko halin da ba za a iya jurewa ba. Hakanan yana iya janyo sharri da yaduwar alfasha.

4. Yin Alkawarin Aure da Rayuwa Kamar Ma’aurata
Saurayi da budurwa da ke rayuwa tamkar an yi aure tsakanin su da kiran juna “miji” da “mata,” ko cin zarafin iyayen juna suna aikata laifi a doka da addini. Ba a amince da a yi soyayya irin ta aure sai bayan auren.

5. Rungumar Juna a Cikin Jama’a ko Aikata Abubuwan da S**a Bambanta da Tarbiyya

abin da ya sabawa kunya da tarbiyya a bainar jama'a, kamar runguma, magana da dariya marar amfani ko bayyanar da sirrin juna, haramun ne kuma yana ƙara lalata tarbiyyar Musulmi. Wannan na iya zama ishara ce ga rashin ladabi da mutunci.

Shawara
Ɗabi'u marasa kyau tsakanin saurayi da budurwa kafin aure ba wai kawai haramun ne a Musulunci ba, yana iya shafar rayuwar aure nan gaba, taɓa mutunci, da janyo fushin Allah.

Allah Ya shiryar da matasa Ya kare mu daga fadawa cikin ɗabi'un da s**a sabawa addini.

10/08/2025

Yadda Zaki Gane Namiji Yana Da Niyya Da Gaske Akan Ki

Yana gabatar da ke ga mutanen da suke da muhimmanci a wurinsa.

Yana nuna sha’awa a rayuwarki, ba kawai kamanninki ba.

Yana son jin yadda ranar ki ta kasance da gaske.

Yana sauraronki ba tare da yana duba wayarsa ba.

Ba ya wasa da hankalinki ko yin wasa da zuciya.

Yana ɗaukar lokaci da ke ko da yana da aiki sosai.

Yana tare da ke ba sai idan yana buƙatar wani abu ba.

Yana girmama ra’ayinki ko da bai yarda da su ba.

Yana shirya al’amura, ba kawai fitowar gaggawa ba.

Yana gaya miki yadda yake ji ba tare da tsoro ba.

Milhart ✍️

10/08/2025

A duk salloli biyar da za ki yi a rana, ki tabbata kin roƙi Allah kariya daga sharrin mayaudaran samari.
Soyayyar yanzu ta zama abin cewa Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.

Kar ki bari a miki wayau.
Kar ki bari ki zubar da mutuncinki da na iyayenki.
Kar ki bari ya ga tufafin da addininki ya miki sutura.

Ki tuna ke ’ya ce da aka haifa bisa sunnah.
Ki tuna ke kanwar wasu ce.
Ki tuna ke yayar wasu ce.
Ki tuna ke uwa ce wata rana.

Shin yaya za ki ji idan ’yarki ta aikata abin da k**e yi yanzu?

Har yanzu akwai lokaci. Lokaci bai kure ba.
Ki tuba, ki gyara, ki koma ga Allah, Allahu Ghafoorur-Raheem.

10/08/2025

Mace tana son namiji mai kamala, mai gayu, mai kamshi🥰

Wanda ya iya sa kaya da karkata hula wanda ke da tausayi da hankali wanda yasan yakamata ba tare da jiran an tambaye shi ba.

Mace tana son namiji mai kawaici da kunya, wanda zai nuna tausayinta a aikace, ba da baki kawai ba🥰

Wanda yasan yakamata akanki shine me cikakken zati da kwarjini a idon mace

Wannan abubuwa ne da suke sa namiji ya zama abin kwarjini a idon mace.

Namiji mai tsafta, mace tana kallonshi a matsayin cikakken mutum🥰

Namiji mai zuciyar yi, wanda yasan yakamata a koda yaushe, wanda idan ya yi magana zaki kasance cikin nishadi

Mace bata son namiji mai hayaniya ko surutu da yawa tana bukatar namiji mai nutsuwa da hankali.

Wanda yake nuna kishinta a fili, ko a gaban kowa
Wanda zai iya bata kariya daga kowanne irin abun ƙi

Wanda yake da kamun kai da class
Ba wanda kowace mace ta san dariyarsa da muryarsa ba
Wanda yake da nutsuwa da hangen nesa.

mace idan ta samu namiji da irin wannan qualities din tasan cewa
ta samu gwarzo na nunama Sa'a wlh duk namijin da yakeda wannan qualities din kwarjini yakeyi na musamman🥰

Amma ba irin wanda yake ballagazar da kanshi ba wanda ko wacce mace tasan dariyarshi da muryanshi wanda besan yakamata ba

Gareki ukty, Namiji baya kaunar mace mara nutsuwa, mai saukin samu, wacce ta shahara da kulawa da kowane namiji.

Namiji baya so ya ga wacce yake so tana yawan hulɗa da maza, tana yawan dariya da kule-kule da su.

Namiji baya son mace mara tarbiyya, wacce bata da mutunci ko kamun kai.🥺

Wlh duk namijin da ya fahimci cewa kina da sabgogi da yawa da maza, zai cireki daga jerin matan da yake so ya aura. Zai dauke ki a matsayin mace mara daraja.

Ki kasance mace mai daraja, mai tsare mutuncinta, wacce namiji zai kalle ta ya ce wannan ce uwar 'ya'yana nan gaba

Allah yadatar damu

07/08/2025

Address

Indabawa
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mika'il posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category