Duniyar mu a yau

Duniyar mu  a yau Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Duniyar mu a yau, Grocers, Farawa lay out, Kano.

LABARI MAI ƊAUKE DA DARASIYa yi aure, kuma a daren farko na auren (daren farko na zama da matar), sai ya gano cewa ba bu...
04/05/2025

LABARI MAI ƊAUKE DA DARASI

Ya yi aure, kuma a daren farko na auren (daren farko na zama da matar), sai ya gano cewa ba budurwa bace.

A ranar farko ya shiga cikin tashin hankali, ita kuwa tana kuka tana roƙonsa da roƙon Allah Maɗaukaki da ya yafe mata, k**ar yadda ya riga ya shirya ta kafin a ɗaura auren.

Tana kuka sosai tana roƙonsa ya ji tausayinta, ya rufa mata asiri. Ta rantse masa cewa ta tuba domin Allah, ba domin mutane ba. Kuma tana cikin ƙunci, sai dai ta samu nutsuwa ne lokacin da ta k**a hanya ta gaskiya da addini.

Saboda yawan kukanta da roƙonta, sai ya ce mata:

“Zan bar ki tare da ni tsawon watanni 7, sai daga baya na kirkiro wata ‘ƙaramar matsala’ a gidan da za ta kai mu ga saki. Amma ki tabbata cewa ba zan taɓa ki ba, ke kuma ba za ki taɓa ni ba. Za mu zauna k**ar abokai ne kawai.”

Wannan ne mafita da ya yanke bayan duk ƙoƙarin da ta yi na riƙonsa.

Ba ya kusantar ta sam. Duk da haka suna fita tare zuwa wuraren cin abinci, kasuwa, har tafiya suna yi. Amma yana kallonta k**ar abokiyar tafiya ne kawai, ba mata ba.

Bayan da watanni 7 s**a wuce, sai lokacin saki ya yi. Ta shirya kanta, tana kuka, hawaye yana zuba k**ar ruwan sama.

Tana jiran ta ji kalmomin nan:
“Na sake ki… Na sake ki… ke sakakka ce.”

Sai ya ce:
“Ba zan sake ki yanzu ba. Mu je wurin da zan kai ki, in isar da ke gidan iyayenki, sai a can in sake ki kafin ki sauka daga mota.”

S**a tafi, ta ɗauki duk kayanta. Amma sai ya tsaya a gaban wani gidan kwalliya.

Ta ce masa: “Meye wannan?”

Ya ce:
“Ina so ki shiga ki yi gyaran jiki da kwalliya k**ar yadda kika kasance a ranar farko da na aure ki.”

Ta ce:
“Ba daidai bane, iyayena zasu tambayeni, kuma me yasa zan yi kwalliya lokacin da zan dawo gida bayan an sake ni?”

Ya ce:
“Wannan shine sharaɗi na. Idan kin ƙi, zan gaya musu dalilin ainihin sakinki.”

Tayi matuƙar jin tsoro, sai ta amince. Ta shiga wurin kwalliya ta gyara kanta k**ar amarya.

Da ta koma mota, sai ya ce mata ta buɗe drawer a cikin mota. Ta buɗe — sai ta ga takardun tafiya (ticket) guda biyu da sarƙa da zobba na zinariya.

Sai ya ce mata:
“Matar da nake ƙauna… tsawon watanni 7 ban ga komai a gare ki ba sai:

1. Kina Sallah a lokacinta.
2. Kina tada ni domin Sallah a Masallaci.
3. Kina kula da gidanmu da kanki.
4. Dukkan tashoshinki na addini ne.
5. Kina girmama iyayena da naki.

Na ga ke mace ce ta gaskiya wacce ta tuba daga zunubanta. Ke kin yi kuskure, amma kin tuba. Idan Allah ya yafe miki, to wane ni mutum da ba zai yafe ba?

Daga yau, ke matata ce cikakkiya a idona.”

S**a wuce zuwa Malaysia — k**ar ranar farko ta aurensu.

S**a yi watan hutu mai daɗi k**ar sabbin ma'aurata.

Tambaya:
Me kuke tunani game da hikima da hangen nesa na wannan mutumin?

Kuma me kuka koya?

02/05/2025

MAZA 😂😂😂

Uwargida: Maigida ka bada kuɗin Yau zanje Awo

Maigida: nawa ne kuɗin?
Uwargida: dubu 3

Maigida: Gaskiya dubu 3 yayi yawa, tare zamu je Asibitin Yau 🙄
Uwargida: To shikenan 🤷

An shiga Asibiti ɗakin masu awo, zai shigo tace A'a maza basa shiga akwai mátan mutane a ciki 🥴

Maigida: to
Uwargida ta shiga ta fito tace ya bada kuɗin kati.

Maigida: ba kinada kati ba? 🤔
Uwargida: Eh, amma duk awo sabon kati ake siya.

Maigida: Ok nawa ne?
Uwargida: dubu 2

Maigida: Ya mika mata kuɗin ta shige ciki. Can ta sake fitowa
Uwargida: Maigida kuɗin awon Jini

Maigida: awon jini kuma 🤔
Uwargida: Eh, (tana haɗe fuska)

Maigida: nawa?
Uwargida: dubu 2 (ta karɓe ta shige)
Ta ƙara fitowa tace Kudin duba motsin Yaro 😏

Maigida fa ya fara gajiya uwargida tace a zuciyarta ''ba dai kace zaka biyoni ba'' 🤷

Maigida: nawa ne kuɗin? 😩
Uwargida: dubu 2 da ɗari biyar 🥴

Maigida: ya bayar yana haɗa fuska
Uwargida: Ta ƙara fitowa, dear ance kuɗin auna bugun zuciyar Yaro 😏

Maigida: Wai dan Allah nawa ma kika ce in baki gaba ɗaya kuɗin awon da farko? 😢
Uwargida: (Tana Murmushi), dubu 3
Maigida: Ya miƙa mata dubu uku ta shige 😀😃

Kunsan me?😂😂😂 Uwargida tana fitowa taga ba Maigida ba dalilinsa 😂 ashe wata mata ya samu a gefe ya bata dubu 3 yace dan Allah idan Matarshi ta ƙara fitowa ta bata 😂

Tun daga ranar bai ƙara cewa zai bita Asibiti ba 😂😂😂

26/03/2025
Aameen yrabb 🤲
25/03/2025

Aameen yrabb 🤲

Dr Jameel ya wallafa Hakan cikin wani sako daya buga a Shafinsa na Facebook k**ar haka:"YIN HOTO LOKACIN BADA SADAKAAbu ...
25/03/2025

Dr Jameel ya wallafa Hakan cikin wani sako daya buga a Shafinsa na Facebook k**ar haka:

"YIN HOTO LOKACIN BADA SADAKA

Abu ne mai matuqar sosa zuciya ganin yadda ake daukar video na musamman da hotunan mutane a cikin yanayi na qasqanci lokacin da ake raba musu sadaka.

Bawan Allah! Ka nemi yardar Allah. Allah yana gani kuma ba ya mantuwa. Shi ne zai biya ka ba mutane ba. Kar ka nemi yabon me yabo in ba Allah ba.

Bawan Allah! Ko dan Allah ka bayar, ai kare mutuncin mai karbar sadakar wani abu ne mai muhimmacin gaske. Tambarin hotonka a kan buhun shinkafa ba shi Allah ke buqata ba. Samuwar tambarin neman yardar Allah a zuciyarka shi Allah ke so.

Sadakarka shuka ce. Yi mata kyakkyawar shuka domin haduwa da ita a qabarinka ko a filin Qiyama.

Jameel Muhammad Sadis"

Laylatul Qadr Night are coming.🌙🌃❤️‍🩹
18/03/2025

Laylatul Qadr Night are coming.🌙🌃❤️‍🩹

Alhamdulillah🙏
27/12/2024

Alhamdulillah🙏

Address

Farawa Lay Out
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar mu a yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category