DLN daily news 24

DLN daily news 24 DLN24 gidan jarida online Mai bankado labarai kala kala.

03/10/2025
Gwamnan kano ya nada ɗan gwagwarmaya, Dakata a matsayin shugaban sabuwar hukumar kula da tallace-tallaceGwamnan Jihar Ka...
04/07/2025

Gwamnan kano ya nada ɗan gwagwarmaya, Dakata a matsayin shugaban sabuwar hukumar kula da tallace-tallace

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Kabiru Saidu Dakata a matsayin Darakta Janar na Hukumar Tallace-Tallace da Allunan Talla ta Jihar Kano (KASA).

Kafin wannan sabon nadin, Dakata shi ne Darakta Janar na Cibiyar Wayar da Kan Jama’a kan Adalci da Gaskiya (CAJA).

KASA na daga cikin sabbin hukumomi guda huɗu da gwamna Yusuf ya amince da su domin ƙarfafa manyan cibiyoyi da kuma inganta ayyukan gwamnati a faɗin jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

Ga jerin sabbin shugabannin da matsayinsu kamar haka:

Dr. Bashir A. Muzakkar – Darakta Janar, Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano (KASITDA).

Kabiru Saidu Dakata – Darakta Janar, Hukumar Tallace-Tallace da Alamomi ta Jihar Kano (KASA).

Dr. Fatima Abdul Abubakar (Amneef) – Darakta Janar, Hukumar Kariya ga Jama’a ta Jihar Kano (KASPA).

Engr. Isyaku Umar Kwa – Mataimakin Manajan Darakta, Hukumar Gidaje ta Jihar Kano.

Hamisu Musa Gambo Danzaki – Babban Sakataren Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano.

Barr. Isma’il Nasarawa – shugaban Cibiyar Yaƙi da Cin Hanci.

25/06/2025

Alhamdulillah

15/06/2025

Opening FIFA CLUB WORLD CUP

10/06/2025

Gidan labarai

10/06/2025

A.Y.B textile NIG

31/05/2025

Ya Allah

16/05/2025

MADALLAH DA WANNAN KAMFANI MAI ALBARKA. kuringa siyan kaya a hanninsu amintattune.

07/05/2025

BARKANMU DA RANA

Dr Haruna Maiwada shugaban kamfanin Maiwada Global Concept ya zama Dan amanar sarkin Katsina a yau.
04/05/2025

Dr Haruna Maiwada shugaban kamfanin Maiwada Global Concept ya zama Dan amanar sarkin Katsina a yau.

Address

Kano
100101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DLN daily news 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category