30/10/2025
Mai yakai Hadisan Annabi DaΙi πππ
1. πππππ¦π π‘π πππ¬π
Manzon Allah (ο·Ί) ya na cewa : Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa katafaren gida a gidan Aljanna, Sai Sayyidina Umar (A.S) yace Ai to in haka ne sai mu dinga yawaitawa, sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa.
2. πππππ¦π π‘π πππ¬π¨
Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa haskensa har zuwa wata jumaβa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.
3. πππππ¦π π‘π π¨ππ¨
Annabi Muhammad (ο·Ί) ya ce duk wanda ya haddace ayoyi goma na farkon kahfi Allah zai kiyaye shi daga fitinar Dujjal.
4. πππππ¦π π‘π ππ¨ππ¨
Manzon Allah (ο·Ί) yana cewa Wanda ya karanta ayatul kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba.
5. πππππ¦π π‘π πππ¬ππ₯
Idan kazo zaka kwanta a shimfiΙarka da daddare to ka karanta βKulya ayyu hal kafirunβ to bazaka mutu mushriki ba idan ka mutu a wannan daren.
6. πππππ¦π π‘π π¦ππππ
Wanda ya yi alwala, bayan ya Ζare alwala sai ya ce βASH-HADU ALLA ILAHA ILLALLAH WAHADAHU LASHARIKA LAHU WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU, ALLAHUMMA JAβALNI MINATTAUWABINA WAJAβALNI MINAL MUTADHAHHIRINAβ
Duk wanda ya faΙi wannan bayan gama Alwalarsa to zaβa buΙe masa kofofin Aljanna guda takwas ya zaΙi ta wanda ya ke so yashigeta
7. πππππ¦π π‘π ππππͺππ
β’ Wanda ya yi Alwala bayan ya kammala alwalarsa kaf, sai ya ce βSUBHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIKA ASH -HADU ALLAH ILAHA ILLALLAH ANTA ASTAGFIRUKA WAβATUBU ILAIKAβ Zaβa rubuta wannan acikin wata takarda bazaβa buΙe ta ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta.
8. πππππ¦π π‘π π§πππͺππ¦
Wani Sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu Akbar kabirah, Walhamdulillahi kasirah, Wasubhanallahi bukratan waasilah, Sai Manzon Allah ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan kalma, sai ya ce ni ne Ya rasulullah sai Manzon Allah (ο·Ί) ya ce nayi mamakin waΙan nan kalmomi da ka faΙa, anbuΙe kofofin sama gaba Ιaya saboda wannan kalma da ka faΙa, Sai Abdullahi Ζan Umar yace tun daga wannan rana kullum sai na faΙi wannan kalma, ban taΙa tsallake wata rana ko wani lokaci da bana faΙar wannan kalma ba.
9. πππππ¦π π‘π π§ππ₯π
Wata Rana mun kasance muna Sallah A bayan Manzon Allah (ο·Ί) da Annabi ya Ιago daga rukuβu sai ya ce SamiβAllahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Handan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya faΙi wannan sai mutumin yace Ni ne ya Manzon Allah sai Manzon Allah ya ce Naga Malaika talatin da βyan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.
10. πππππ¦π π‘π ππ’π π
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Wanda ya yi sallar nafila raka'a goma sha! biyu tsakanin dare da rana Allah zai gina masa gida Acikin Aljannah.
Alhamdulillah - idan har ka jidaΙi kuma ka ilimantu ka rarraba wannan hadisi tsakanin yan uwa da Abokai Allah ya Amfanarda mu gabaΙaya...
Allah ka kara daΙin tsira da Aminci ga shugaban mu Annabi Muhammad (ο·Ί)
Real Suk Na Fadmah βοΈ