TASS Pharmaceutical LTD.

TASS Pharmaceutical LTD. Pharmaceutical wholesale solutions. Quality products, competitive prices, reliable delivery.

💊💯
12/05/2025

💊💯

💯💊
12/05/2025

💯💊

,💯💊
12/05/2025

,💯💊

Tambayar Mustapha HashimuShin Alhassan azzakari na karyewa?Amsa:Azzakari bashida ƙashi, saboda haka bazai karye ba irin ...
07/05/2025

Tambayar Mustapha Hashimu

Shin Alhassan azzakari na karyewa?

Amsa:

Azzakari bashida ƙashi, saboda haka bazai karye ba irin kariyar da ƙashi keyi

Azzakari jijiyoyin tsoka ne, saboda haka baya karyewa, sai dai zai iya karkacewa yayi “bending”

Idan ɗaya dagacikin jijiyoyin tsokokin dake riƙe azzakari ta tsinke, ko s**a kamu da rashin lafiya, to azzakarin zai karkata zuwa wani ɓangare “bending”

Karkacewar azzakari babbar illa ce ga mutum musamman a wurin saduwa da iyalinsa, yana haifarda kumburin azzakari, zafi, ciwo da raɗaɗi.

Daga ƙarshe

Idan kana fama da karkacewar azzakari, babu wani magani da ake amfani dashi domin a miƙar da azzakarin, hanya ɗaya da ake bi domin dawo da lafiyarsa shine yin aikin tiyata “Surgery” a assibiti

Saboda haka kar wani yazo maka da maganin karkacewar azzakari ka siya 📌

Idan azzakarinka ya karkace, ko ciwo, ko raɗɗi to kaje assibiti.

Alhassan Mai Lafia✍️

Bari in baku wani labari mai amfaniAkwai wasu layuka biyu da aka rubuta a jikin kwalin wannan maganin, kamar haka (1-1)W...
07/05/2025

Bari in baku wani labari mai amfani

Akwai wasu layuka biyu da aka rubuta a jikin kwalin wannan maganin, kamar haka (1-1)

Wannan, yana nufin so biyu ake shan wannan maganin “per day”

Wata mata taje siyowa yaronta magani a “Pharmacy” yaron ƙarami ne sosai mai shekaru (2 zuwa 3)

Akayi rashin sa’a wanda yake siyarda maganin, yayi mantuwa bai rubuta ƙa’idar shan maganin ba

Da matar taje gida, sai ta baiwa yaron dukkan maganin a lokaci ɗaya 🥲

Gari ya waye yaron ya mutu

Daga ƙarshe hukumomi sun ɗora laifin mutuwar yaron zuwaga mai sayarda maganin, saboda yayi mantuwar rashin sanarda matar ƙa’idojin shan maganin a rubuce

Kuma aka jingina masa biyan diyyar yaron.

Saboda haka, yanada matuƙar amfani ku kiyaye wannan dokar musamman masu sayarda magani acikin unguwanni da kasuwa

Shan magani ba bisa ƙa’ida ba, yana janwo wahala ko rasa rayuwa

⚠️ ba’a shan magani sai da izini da umarnin likita

Alhassan Mai Lafia✍️

01/05/2025

Ina Mamakin Yanda mutum zai fito a gidan TV yana ƙarya saboda neman kuɗi.

Mafiyawan masu tallar maganin gargajiya, yan damfara ne kawai.

Bazanyi jam’i ba domin akwai masu sayarda magani mai amfani

Amma haka kawai zasu biya kuɗin talla a gidan talabijin (TV) sai su zauna suna sharo ƙarya tsabar damfara 😭

1. Babu maganin istimna’i (ma********on)

2. Babu maganin dake sauya genotype

3. Babu maganin ƙarin basira a makaranta

4. Babu maganin dake sauya jinin jiki (Blood group)

5. Babu maganin kansa, ko assibiti idan cutar kansa takai wani mataki, sai dai management.

6. Babu maganin waraka daga HIV/AIDS, sai dai management

7. Babu maganin farin jini, maganin farinjini shine ka koma kasuwa ka nemi kuɗi (ƙarshen farinjini kenan)

Da sauransu

Idan kayi magana sai s**e kana neman hanasu cin abinci, zaka kashe musu kasuwa

Ko su fake da cewa (Allah bai halicce kowace irin cuta ba, har sai da ya halicce magani). Tabbas hakane amma cutukan dana lissafo haryanzu Allah bai bayyanarda maganinsu ba. Duk wanda yace yanada maganinsu ƙarya yakeyi 📌

Saboda haka yakamata mutane su kiyaye

Ni tambayar da nike neman amsa shine:

Tsakani da Allah, tun yaushe kake shan maganin istimna’i da maganin sanyi na gargajiya, shin kasamu lafiya ka daina istimna’i ko haryanzu kanayi??

Wani lokacin sai ka gama kashe kuɗinka a banza, sannan kagano cewa matsalar daban take, wacce kake tunani ba ita bace,

Babu wanda aka hana neman abinci ko neman kuɗi, amma ku tsayu akan gaskiya da adalci.

Alhassan Mai Lafia✍️

Address

Kanawa Pharmaceutical Co-ordinate Whole Sale Centre (CWC) Ɗangwauro Kano
Kano

Opening Hours

Monday 09:00 - 18:00
Tuesday 09:00 - 18:00
Wednesday 09:00 - 18:00
Thursday 09:00 - 18:00
Friday 09:00 - 18:00
Saturday 09:00 - 18:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TASS Pharmaceutical LTD. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category