06/09/2022
Da Yawa Za ka Ga Maza Su Na Ta Fama Da Ɗurawa Kan su Maganin Sanyi Wai Ba Sa Iya Tabuka Komai A Gida .
Daga: Ibrahim Jamila
Wlh lafiyanku kalau talauci ne kawai kesa wasu Suke Ganin basuda lafiya ..
Yo Ina kaga lafiya pampers ya kare , Babu abinci gida ,kana tunanin an kusa komawa makaranta zaka biyawa Yara biyar kudin makaranta Ina kaga halin tabuka komai
Misali ma ace cin zaki da maiko ke jawo rashin kokarin Ina talaka yaga zaki da maikon
Idan mutum yaji wasu kudade masu zafi a account wlh nan da nan zakaga wasu kuzari sun shiga jikin ka , zakaga ranar Allah Allah ma kake dare yayi ka siyo gasusassun Kaji kacewa madam yaufa ranar kara'i ne
Soyayyar ranar da kake da kudi da ranar kakeda wasu damuwa daban ne akan ranar da kake fama da talauci don haka ku rage shan magunguna ku Nemi kudi itace matsalar dakuwar ku
Da fatan Kun dauki darasin yau