Marhad Media Advert Specialist

Marhad Media Advert Specialist Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Marhad Media Advert Specialist, Media news company, Katsina.

Marhad Media Advert Specialist

Muna tsara Aiyukan Tallace tallace ta Kamfanoni da Masana"antu Tare da Bayyana Aiyukan Yan'Siyasa,
Tare da labarai masu inganci

Ƙungiyar likitocin Najeriya ta yaba wa Abba Gida-Gida bisa gyara asibitoci 200 a Kano Ƙungiyar Likitoci ta Kasa (NMA), r...
22/10/2025

Ƙungiyar likitocin Najeriya ta yaba wa Abba Gida-Gida bisa gyara asibitoci 200 a Kano

Ƙungiyar Likitoci ta Kasa (NMA), reshen jihar Kano, ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gyaran sama da cibiyoyin kula da lafiya Matakin farko guda 200, tare da ɗaukaka wasu daga cikinsu da ƙananan asibitoci zuwa manyan asibitoci.

Shugaban NMA na Kano, Dakta AbdulRahman Ali, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, yayin bikin makon likitoci na shekarar 2025.

Dakta Ali ya ce wannan ƙoƙari zai inganta tsarin kula da lafiya a jihar, tare da ƙara walwalar ma’aikatan lafiya a fadin Kano.

Ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka za su ƙarfafa ma’aikatan lafiya su ƙara himma wajen gudanar da aikinsu.

Ya roƙi gwamnatin jihar da ta tabbatar da cewa an samar da yanayi mai kyau da albashi mai kyau ga ma’aikatan lafiya domin ƙara musu ƙwazo.

Shugaban ya kuma buƙaci gwamnati ta mai da hankali kan horar da ma’aikatan lafiya da sake horar da su don samun ingantaccen sakamako a hidimar lafiya.

Haka kuma, ya yi kira ga gwamnati da masu zaman kansu masu ruwa da tsaki a fannin lafiya da su haɗa kai domin cimma manufofin samar da ingantacciyar lafiya ga jama’a.

Dakta Ali ya tabbatar da cewa mambobin NMA za su ci gaba da goyon bayan manufofin gwamnatin jihar da ke da nufin bunƙasa harkar lafiya.

Yau Kwana 100 Bayan Rasuwar Muhammadu Buhari: Kuna tunaninsa kuwa ?Kwanaki 100 da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu...
22/10/2025

Yau Kwana 100 Bayan Rasuwar Muhammadu Buhari: Kuna tunaninsa kuwa ?

Kwanaki 100 da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda wasu ke tunawa da shi a matsayin jagora mai gaskiya da rikon amana.

Buhari ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan siyasar Najeriya da s**a yi mulki ba tare da almundahana ko zambar dukiyar ƙasa ba. A cewar masu nazari, rayuwarsa ta zama abin koyi ga shugabanni da ‘yan siyasa na zamani.

An ce, duk da cewa wasu sun soki mulkinsa, amma babu wanda ya musanta cewa Buhari ya bar gadon gaskiya da tsoron Allah.

Kuna tunaninsa kuwa? Me kuka dauki Buhari a naku bangaren?

Ana Fargabar Mutane Sun Rasu Sakamakon Fashewar Tankar Mai A Jihar NejaLamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata  a ya...
22/10/2025

Ana Fargabar Mutane Sun Rasu Sakamakon Fashewar Tankar Mai A Jihar Neja

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a yankin Agaie - Bida na ƙaramar hukumar Katcha. Hatsarin ya kuma haifar da cunkoson ababen hawa a wata babbar hanya.

Babbar kwamandar hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta jihar Hajiya A'ishatu Sa'adu ta tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ta bayyana ba a iya tantance adadin mutanen da s**a jikkata ba har kawo yanzu.

TALLA: Domin fara sána'ár DATA ko kuma ku dinga saka wa kanku, ku sáuké Mánhájar KSBDATA a PláyStore.
👇👇👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.ksbdata.app

Website
👇👇👇
https://

TIRKASHI: NBA ta Caccaki Hukunci Kotu bisa Umartar Mai Wushirya da ’Yar Guda su yi Aure cikin Kwana 60Ƙungiyar Lauyoyin ...
22/10/2025

TIRKASHI: NBA ta Caccaki Hukunci Kotu bisa Umartar Mai Wushirya da ’Yar Guda su yi Aure cikin Kwana 60

Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta bayyana ƙin amincewarta da hukuncin wata kotun majistare da ke Kano wadda ta umarci fitattun masu bidiyo na TikTok Idris Mai Wushirya da Basira ’Yar Guda da su daura aure cikin kwanaki 60, bayan shari’ar da ta shafi wallafa bidiyon da aka ce bai dace ba.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya fitar, NBA ta ce wannan hukunci “babban kuskure ne kuma ya sabawa ’yancin mutum da kundin tsarin mulki na ƙasar ke bayarwa.

A cewar sa “babu wata kotu da ke da ikon tilasta mutane su yi aure, ko da kuwa tsakanin maza da mata ne da ake zargi da aikata wani laifi. Yin hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kuma ya saɓawa ƴancin ɗan Adam."

Ƙungiyar ta ƙara da cewa aure lamari ne na yardar juna tsakanin manya, ba abin da za a iya amfani da shi a matsayin hukunci, gyaran hali, ko ladabtarwa ta doka ba.

NBA ta kuma yi kira da a sake duba hukuncin da mai shari'a Halima Wali ta yanke, tare da tabbatar da cewa irin wannan umarni mara tushe bai sake faruwa ba.

Haka kuma, ƙungiyar ta umarci Kwamitin Kare ’Yancin Jama’a da na Mata na NBA da su sa ido kan lamarin domin tabbatar da cewa an kiyaye doka da adalci.

“Ba a taba yarda cewa wata kotu ko wata hukuma ta tilasta aure ga kowa ba. Yin hakan take kundin tsarin mulki da mutuncin ɗan adam,” in ji NBA.

Idan Atiku ya mara wa Peter Obi baya, cikin ruwan sanyi zai kayar da Tinubu a zaben 2027 - Tsagin jam'iyyar LabourKarin ...
22/10/2025

Idan Atiku ya mara wa Peter Obi baya, cikin ruwan sanyi zai kayar da Tinubu a zaben 2027 - Tsagin jam'iyyar Labour

Karin bayani: https://da.gd/pjwyLA

CIKIN HOTUNA: Jagoran Jam’iyyar NNPP na Kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya halarci bikin taron cikar shek...
22/10/2025

CIKIN HOTUNA: Jagoran Jam’iyyar NNPP na Kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya halarci bikin taron cikar shekarunsa 69, na musamman da aka shirya domin girmama shi a dakin taro na Afficent, dake Nassarawa GRA, a Kano, tare da abokansa, da kuma masoyansa da s**a hallara domin taya shi murna.

#
Ganye24

DA DUMI DUMI: Hukuma ta kai samame tare da rufe wani gidan shan sh**ha da ke kan titin Abdullahi Bayero, a tsakiyar birn...
19/10/2025

DA DUMI DUMI: Hukuma ta kai samame tare da rufe wani gidan shan sh**ha da ke kan titin Abdullahi Bayero, a tsakiyar birnin Kano.

# Ganye24

DA DUMI DUMI: Tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya halarci jana’izar Marigayi Raila Amolo Odinga, wanda a...
19/10/2025

DA DUMI DUMI: Tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya halarci jana’izar Marigayi Raila Amolo Odinga, wanda aka binne a garinsu na Nyamira, yankin Bondo, a ƙasar Kenya.

An gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin Trump a AmurkaƘarin bayani - https:marhadmediaadvert//bbchausatrib.al/T0b1...
19/10/2025

An gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin Trump a Amurka

Ƙarin bayani - https:marhadmediaadvert
//bbchausatrib.al/T0b1BdA

‘Yansandan Kano sun saki ɗanjarida Dan’uwa Rano bayan zargin ɓata wa ɗansiyasa sunaƘarin bayani Marhadmediaadvert  hausa
19/10/2025

‘Yansandan Kano sun saki ɗanjarida Dan’uwa Rano bayan zargin ɓata wa ɗansiyasa suna

Ƙarin bayani Marhadmediaadvert hausa

Shin kuna Ganin Sojoji zasu iya Karɓe Mulki a Najeriya?
19/10/2025

Shin kuna Ganin Sojoji zasu iya Karɓe Mulki a Najeriya?

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un Allah Ya Yi Wa Haziƙin Matashin Ɗan Śanda DSP Salisu Sulaiman Hadejia Rasuwa, Yau Alh...
16/10/2025

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un

Allah Ya Yi Wa Haziƙin Matashin Ɗan Śanda DSP Salisu Sulaiman Hadejia Rasuwa, Yau Alhamis a garin Katsina bayan fama da gajeruwar jinya.

An shedi matashin da hali na gari, yana da kirki da mutunta mutane.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Address

Media News Company
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Marhad Media Advert Specialist posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share