20/01/2026
MUN CIKA WATAN RAJAB 1447
Sanarwa daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
اللهم صل على محمد وعلى آل محمد
Ana sanar da al'umma cewa, saboda rashin samun labarin ganin jinjirin wata a jiya Lahadi, yau Litinin watan Rajab ya cika kwana talatin (30) cur.
Don haka gobe Talata za ta zama 1 ga watan Sha'aban 1447, in sha Allah.
Kada a manta da addu'o'i ma'thurai na watan Sha'aban musamman ma munajatin Sha'abaiyyah na Amirul Mu'minin (AS) da sauran addu'o'i da salloli a wannan wata mai albarka. Allah Ta'ala Ya gamar da mu da katari; Ya kai mu zuwa watan Ramadan cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki.
Allah Ya ba mu sa'a.
Wassalam
30/Rajab/1447
19/01/2026