07/06/2026
NGWLG001✅️
ASSALMU ALAIKUM JAMA'ARMU
Akwai Wani Abu Da Nalura Dashi A Ingawa Game Da Rarraba Makamai A Gwamnatance
Itadai Ingawar A Fahimtarnu Takasu Kashi Ukkune
1. Ingawa ta Tsakiya
2. Ingawa ta Kudu
3. Ingawa ta Arewa
Na Farko Ingawa Ta Tsakiya Tanada Mukamai Kamar Haka
1. Dan Takarar Reps a Ingawa
2. Chairman a Ingawa
3. Commissioner a Ingawa
Da Dai Sauransu
Na Biyu Munada Ingawa ta kudu inda keda Mukamai kamar haka
1. Secretary for the Chairman of Ingawa Local Government From Yaya
Na Ukku Munada Ingawa Ta Arewa inda Mukeda Mukamai Kamar Haka
1. E.S Of Ingawa Local Government From Yandoma
2. V.C Of Ingawa Local government From Yandoma
3. STILL Dan Takarar Majalisar jaha From Yandoma
Dadai sauransu.....!
Shin Abun Tambayar Anan Shine Mu Yen Yankin Ingawa Ta Kudu Bamu Cancenci Shiga Duk Irin Wannan Fagen Na Siyasa Ba Koko? Bayan Kuma Muke Kawo Kashi Hamsin 50 Bisa Dari kuri'ar Karamar hukumar Ingawa Tohm Gaskiya Yakamata Ayi Mamu Adalci.
Sannan Ina Kara tini Ga Gwamnati akan batun hanyar Manomawa yanxu lokacin damina yayi kuma yanxu ne lokacin da mukafi bukatar taimako akan wannan hanyar saboda itadai wannan hanyar mahimmancin ta shine farkon harda ceton Al'ummar yankin Manomawa Da Kewayenta Saboda Da zaran ansamu mace mai nakuda wallahi idan ba sa'a har ta ranta zata iyayi saboda mace mai ciki kafin akawota asibiti daga manomawa zuwa Ingawa adai wannan hanyar tofa zataji jiki idanma wannan ne zamuce Alhamdulillah Sabanin haka muyi jimamin rasata ko abindake cikinta hanyar ga Duwatsu, Ga Ramuka, Sannan Ga Ruwa Amma Duk inda Akayi Mamu Koda Furojace Daidai Da Karfin Wanda Zaiyi Aikin Tofa Zamuji Dadin wannan aikin kaga memakon ace azagaya yadauki minti 20 zuwa 30 a wannan hanyar cikin minti 12 zuwa 15 anceci rai biyu.
Toh Don Allah Muna kira Da Babbar Murya Akan Wannan Koken Namu,
Tun Kafin Kuxo Fara Rokonmu Akan Mu Zabeku Mu Jama'ar Wannan Yankin
We Need Help
And We Need Justice
✍️
C.E.O ACTIVE ALMUSTAPHA ADAMU MANOMAWA