10/05/2026
نصر من الله وفتح قريب 💯💯
ALHAMDULILLAH ALA KULLI HAL 🤍📖
Cikin tsananin farin ciki da godiya ga Allah (SWT), ina taya murna ga Ya'yana yara mata waɗanda s**a samu nasara a gasar karatun Al-Qur’ani Mai Girma da Qur'an Akko Musabaqa Foundatio s**a shirya karo na 4.
🥇 Fatima Usman Murshid
Ta zama Zakara ta 1st Position a bangaren 30 Hizb.
🏅 Aishatu Usman Murshid
Ta samu 4th Position a bangaren 30 Hizb.
Hakika wannan babbar ni’ima ce daga Allah (SWT), kuma abin alfahari ne ga iyaye, malamai da al’umma baki ɗaya. Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa wannan baiwa da falala da Ya yi musu.
Allah (SWT) Ya sanya Al-Qur’ani ya zama hujja a gare su ba hujja a kansu ba.
Ya ƙara musu ilimi mai amfani, fahimta, hikima da tsoronSa.
Ya albarkaci rayuwarsu, Ya sa su zama daga cikin bayinSa na gari masu aiki da Al-Qur’ani.
Allah Ya ɗaukaka su a duniya da Lahira, Ya sanya wannan nasara ta zama mafari na manyan nasarori masu albarka. 🤲📖
Muna fatan Allah Ya ci gaba da ba su ƙarfi, dagewa da ikon kare martabar Al-Qur’ani Mai Girma.
Imam Usman Murshid Kumo