Kwankwaso kawai 2027

Kwankwaso kawai 2027 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kwankwaso kawai 2027, Grocers, Lokoja 2hundred unit, Lokoja.

12/02/2026

Kafa Hukumar Sharia da Hisbah da Shura da hukumar Zakka da waƙafi da Hukumar tace finafinai, A Shekarar 2000, shi ne laifin Kwankwaso a wajan Amvrka

~ Cewar Malam Aminu Ibrahim Daurawa

12/02/2026

🚨Jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya sun mayar da martani kan matakin wasu ƴan majalisar wakilan Amurka na gabatar da ƙudurin neman a dauki mataki kan Najeriya bisa zargin musguna wa Kiristoci.

Ƙudurin ya nemi a sanya takunkumin hana da kuma riƙe kadarorin tsohon ministan tsaro Rabi'u Kwankwaso da kuma ƙungiyoyi biyu na makiyaya.

Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan da kuma NNPP mai adawa duk sun soki lamirin ƙudurin.

Mai magana da yawun jam'iyyar APC, Bala Ibrahim ya ce bai k**ata a yi amfani da shaci-fadi wajen ƙaƙaba takunkumi kan ƴancin zirga-zirga na wani mutum ba ba tare da ji daga gare shi ba.

Ita kuma jam'iyyar NNPP ta musanta cewa Kwankwaso ya take hakkin yin addini duk da cewa a lokacin mulkinsa ne aka amince da amfani da shari'ar Musulunci a jihar Kano a shekara ta 2000.

A wata ganawa da manema labarai, mai magana da yawun jam'iyyar NNPP na ƙasa Ladipo Johnson ya ce me ya sa ba a zargi sauran gwamnonin da jihohinsu s**a amince da shari'a ba sai Kwankwaso kadai.

A ranar Laraba ne wasu ƴan majalisar wakilan Amurka s**a gabatar da wani ƙuduri a majalisar na neman ɗaukar matakai kan Najeriya domin daƙile zargin musgunawa Kiristoci.

(Daga BBC)

12/02/2026

Jam'iyyar APC ta soki kudurin da Amurka ta yi na zargin Kwankwaso da tauye yancin addini ga Kiristoci.

BBC ta ruwaito cewa, mai magana da yawun jam'iyyar APC, Bala Ibrahim ya ce "bai k**ata a yi amfani da shaci-fadi wajen ƙaƙaba takunkumi kan ƴancin zirga-zirga na wani mutum ba ba tare da ji daga gare shi ba.

12/02/2026

A duk faɗin Duniya bani da ko sisin kobo ko dukiya a wata ƙasar waje tun daga Niger har Amurka, kuma duk faɗin duniyar nan ƙasar Saudiyya ce za a hana ni shiga in damu, ina zaton ƙaddamar da shari'ar Musuluncin da nayi a zangon mulkina na na farko shine silar wannan hayaniyar, kuma mun riga mun yi babu gudu babu ja da baya.
- Rabiu Musa Kwankwaso

19/01/2026

YANZU-YANZU: Bayan kujerar Umarah an sake biyawa Malam Haruna kujerar aikin hajjin bana daga wata baiwar Allah hajiya Fatima Zinariyar Arewa

Allah ya saka da Alkairi ya sa hakan ya zama silar daw wayar farin ciki a zuciyarsa

19/01/2026

Kwankwaso yayi ta'aziyya kan kisan gillar da aka yiwa mata da ’ya’yanta shida a unguwar Chiranchi dake Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana jin daɗinsa bisa gaggawar da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta yi wajen cafke manyan waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a Chiranchi dake yankin ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yau ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana kisan a matsayin mummunan aiki da ya girgiza zukatan al’umma.

Ya yabawa ’yan sandan kan hanzarin da s**a nuna, yana mai kira ga hukumomi da su tabbatar an gudanar da cikakken bincike tare da hukunta masu laifin yadda doka ta tanada.

Har ila yau, ya yi kira ga al’ummar Kano da su ƙara lura da juna, su ƙarfafa alakar makwabtaka da tsaron al’umma, domin hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.

A ƙarshe, Kwankwaso ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayiyar da ’ya’yanta, Ya sanya su a Aljannar Firdaus, Ya kuma bai wa iyalansu haƙuri.

19/01/2026

Kwankwaso ya yaba wa ‘yansanda bisa k**a waɗanda ake zargi da kisan uwa da 'yayanta 6 a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana jin dadinsa kan saurin k**a waɗanda ake zargi da kisan Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, Kano.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, Kwankwaso ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan aiki na tashin hankali da ya girgiza zuciya, yana mai cewa kisan uwa da kananan ’ya’yanta abin tausayi ne matuka kuma ya jefa al’ummar Kano cikin bakin ciki.

Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mazauna Dorayi Chiranchi da kuma daukacin al’ummar Jihar Kano, yana mai cewa zuciyarsa da addu’arsa suna tare da su a wannan lokaci na jimami.

Kwankwaso ya kuma yabawa Rundunar ’yansandan Jihar Kano bisa gaggawar daukar matakin bincike na sirri da ya kai ga k**a manyan wadanda ake zargi cikin ‘yan awanni bayan faruwar lamarin.

A cewarsa, wannan saurin daukar mataki da ‘yansanda s**a yi ya bayar da wani haske na samun adalci duk da tsananin muguntar kisan.

Tsohon gwamnan ya bukaci hukumomi da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargin gaban shari’a cikin gaggawa, domin a hukunta su yadda doka ta tanada kuma a hana sake faruwar irin wannan mummunan aiki a gaba.

Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su kara zage damtse wajen sa ido, su kula da juna tare da karfafa hadin kan al’umma domin dakile tashin hankali da inganta tsaro.

Kwankwaso ya kammala da yin addu’ar Allah Ya jikansu da rahama, Ya sanya su a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansu hakuri da juriyar jure wannan babban rashi.

19/01/2026

Kwankwaso zai koma jam'iyyar ADC a ranar Alhamis mai zuwa bayan kammala shirye shiryen da cimma dai-dai to, inda ake sa ran zai yiwa Peter Obi mataimakin shugaban ƙasa.

TALLA:

Albishirinku masu sana'ar siyar da katin kiran waya ko data, fitaccen kamfanin nan mai suna VTUPoint, ya samar da sashin ƙirƙirar katin waya, zasu baka daman buga adadin lambobin da kake so tun daga katin.

₦100-₦200-500, zuwa sama ka sanya sunan ka ko sunan gari unguwa ko layunku ko kuma duk irin sunan da kake so domin fitar da katin waya na takarda wato printing recharge card na ko wane irin layi ka siyar wa da kwastomomin ka, domin samun gwaggwaɓar riba.

𝗞𝘂 duba comments section akwai link don 𝘀𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗮𝗽𝗽 ɗ𝗶𝗻 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗣𝗹𝗮𝘆𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.msorgdevelopers.vtupoint

03/10/2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya halarci wani gagarumin biki na kaddamar da cibiyar al'adu a Legas a ranar Laraba.
Biki ne da ya hada manyan baki a lokacin, kuma har aka gano yana gaisawa ta girmamawa ga Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II.

Address

Lokoja 2hundred Unit
Lokoja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kwankwaso kawai 2027 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category