Abdulqader Idres Mustapha G-Sarki

Abdulqader Idres Mustapha G-Sarki I'm Abdulkadir Idris Mustapha G-Sarki, Am. Living in maraban Jos which is in kaduna State Nigeria ?

17/08/2023
12/08/2023
23/09/2022

*SAƘO ZUWA GA IYAYE*

Haƙiƙa al'amarin tarbiyyar ƴaƴa musamman ƴaƴa mata, abu ne mai muhimmanci matuƙa, wanda da yawa a wannan lokacin mafi yawan iyaye s**a yi sakaci ƙwarai a kan sa.

Za ka samu yarinya ta fara girma ta kai shekara sha biyar 15, amma iyaye ba su damu da ina ta ke zuwa ba, yaushe ta ke dawowa makaranta ; da ƙawayen da ta ke mu'amala da su.

Saboda haka, yana da kyau iyaye sun sanya idanu a kan ƴaƴansu musamman ƴaƴa mata. Akwai wasu shawarwari masu tsada da na tsara zan baiwa iyaye, domin katange ƴaƴansu daga maɓarnata:

*1.* Sanin waɗanda ƴaƴanku suke mu'amala da su a fili da kuma boƴe?

*2.* Sanya ido game da suturar da ƴarku/ɗanku suke sanyawa musamman lokacin da za su fita gida

*3.* Hanasu kallon wasu tashoshin da ake yaɗa ɓarna da lalata tarbiyya.

*4.* Dakatar da ita daga fita gun saurayi da sunan soyayya, idan ba aurenta zai yi ba.

*5.* Sanya ido da bincike a cikin wayoyinsu, da kuma suwa suke mu'amala da su a wayar.

*6.* Lura da lokacin da suke kwanciya barci da daddare.

*7.* Sanyasu suyi muraji'ar abin da aka musu a makaranta.

*8.* Ƙoƙarin zama da su domin jin matsalolinsu, da kuma shawarwari.

*9.* Ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakaninku da malamansu na boko da Islamiyyah.

*10.* Bayan kunyi iya bakin ƙoƙarinku sai ku biye da yi musu addu'a, Allah ya shiryar muku da su hanya madaidaiciya.

07/09/2022

Address

Makers Road No C3 Kaduna
Makera
DANUMMAH

Opening Hours

Monday 09:00 - 07:00
Saturday 09:00 - 07:00

Telephone

+2349028403193

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdulqader Idres Mustapha G-Sarki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abdulqader Idres Mustapha G-Sarki:

Share

Category