Uwa maba da mama

Uwa maba da mama Wannan shafi anbude shi ne don yabawa ga iyaye musamman iyaye mata.

03/06/2025

Tsarki ya tabbata ga Allah
Allah kai mana yadda muke so .

MATSALOLIN MU A FILI SUKE 1. Muna aure ba tare da soyyayya ba. 2. Muna haihuwa ba tare da yin tarbiyya ba. 3. Muna salla...
03/06/2025

MATSALOLIN MU A FILI SUKE

1. Muna aure ba tare da soyyayya ba.

2. Muna haihuwa ba tare da yin tarbiyya ba.

3. Muna salla ba tare da tsaron Allah ba.

4. Muna koyan ilmi ba tare da aiki ba.

5. Muna magana ba tare da gaskiya ba.

6. Muna daukan alƙawari ba tare da cikawa ba.

7. Muna karɓar amana ba tare da kulawa ba.

8. Muna son kuɗi ba tare da Sana'a ba.

9. Muna son Annabi (SAW) ba tare da bin koyarwar sa ba.

10. Muna son Aljannah ba tare da aiki ba.

11. Muna son a amsa mana addu'a ba tare da cin halal ba.

12. Gamu da bala'in son duniya da ƙin mutuwa.

Mafita kawai mu tuba mu gyara, muce Allah mun tuba ka yafe mu.

Shege AI ku dubi yadda ya mai dani
03/06/2025

Shege AI ku dubi yadda ya mai dani

30/05/2025

Allah ya fahimtar damu
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Professor Isa Ali Pantami

Farfesa Mai Saida Tumatir!Wannan bawan Allah Farfesa ne guda a jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua Katsina, daga Department of B...
29/05/2025

Farfesa Mai Saida Tumatir!
Wannan bawan Allah Farfesa ne guda a jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua Katsina, daga Department of Biology. Ya riƙe sana'arsa na karantarwa, yake harbin tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Ga sana'a ga academia. Sunansa Professor Nasir Hassan Wagini.

Jama'a bamu san wani halin rayuwa ne wannan Farfesa ya sami kansa a ciki ba. Toh amma bisa ga dukkan alamu, bayi da girman kai ko miskala zarratin. Hakazalika, yana alfahari da neman halal maimakon cin dukiyan al'ummanmu.

Wallahi ya burgeni kwarai da gaske. Muna yi masa addu'a da fatan Alheri. Allah Ubangiji Ka daafa masa. Allah Ubangiji Ka kara daukaka shi. Amin Ya Rabbi.

Daga shafin Engr Jabir Wada Isah

Uwa da da kenan. Allah ya karbi ibada ya dawo daku lafiya ya kara wa mama lafiya da tsawon rai 🙏    Umar Shuaibu Malumfa...
29/05/2025

Uwa da da kenan. Allah ya karbi ibada ya dawo daku lafiya ya kara wa mama lafiya da tsawon rai 🙏
Umar Shuaibu Malumfashi

Address

Malumfashi
Malumfashi
832103

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Uwa maba da mama posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category