12/02/2024
Dalilaii Guda Wadanda Ake Tunanin Sune S**a Bawa Najeriya Matsala q katawarsu da Ivory Coast Mai Masaukin Baki
1.Ivory Coast ta karanci Najeriya:
Da farko dai Najeriya ta ci kasar Ivory Coast a wasansu na rukuni 1- 0, inda 'yan kasar s**a yi ta nuna rashin jin dadinsu a matsayinsu na masu masaukin baki har ta kai s**a yi bore ciki har da kone-kone. Hakan ya sa kungiyar ta Elephants tsayawa ta yi karatun ta-nutsu domin karantar takun wasan 'yan Super Eagles. Kuma wannan gano lagon Najeriya da ita Ivory Coast ta yi hakika ya taka muhimmiyar rawa wajen bai wa mai masaukin bakin nasara kan Najeriyar.
2.Najeriya ta koma tsaron gida:
Tun bayan cin kwallo daya tilo da 'yan Najeriya s**a yi a minti na 38 da fara wasa sai 'yan wasan Super Eagles s**a koma s**a tare a bakin raga domin tsaron gida maimakon kokarin ganin sun kara jefa kwallaye. "Hakan ba karamar illa ya yi wa Najeriya ba bisa la'akari da yadda 'yan Ivory Coast din s**a yi ta kai wa Najeriya hare-hare iri-iri su kuma Super Eagles s**a koma kariya kawai," in ji Jantile.
3. Tsakiyar Najeriya ta dare:
Masanin ya ce tun ba a je ko'ina ba sai tsakiyar 'yan wasan Najeriya ta b***e bat inda 'yan wasan s**a koma buge-buge ba tare da basira ba. "Sun koma yin ci da karfi ba tare da hadin kai ba inda s**a rinka amfani da basirarsu ba ta kocin ba," in ji Bashir Jantile.