Dr. Abba Youth Political

Dr. Abba Youth Political Dr. Abba Youth Political Initiative Forum �

Alhamdulillah 🎉Dr. Abba Youth Political initiative Forum has officially reached 200 followers on Facebook.We sincerely a...
11/05/2026

Alhamdulillah 🎉

Dr. Abba Youth Political initiative Forum has officially reached 200 followers on Facebook.

We sincerely appreciate your love, support, and encouragement. Your support continues to inspire us toward promoting youth development, unity, and community progress.

Thank you for believing in us 🤝
More impactful moments ahead, In Shaa Allah.

11/05/2026

Zagayen gaishe-gaishe da Jajantawa, har ma da duba marasa lafiya na AMARYAWA DISTRICT da megirma shugaban ƙaramar hukumar Roni ya aiwatar a jiya.

A madadin shugaban ƙaramar hukumar Roni Hon. Dr. Abba Ya'u muna ƙara miƙa saƙon gaisuwar ga al'umma AMARYAWA DISTRICT ka fin kuma mu kai ziyara RONI DISTRICT Inshallah

🙏😢

SHUGABAN DA KE JIN ZAFIN AL’UMMARSA HON. DR. ABBA YA’UTun daga ƙarfe 8:00 na safiyar jiya Lahadi har zuwa 3:00 na yamma,...
11/05/2026

SHUGABAN DA KE JIN ZAFIN AL’UMMARSA HON. DR. ABBA YA’U

Tun daga ƙarfe 8:00 na safiyar jiya Lahadi har zuwa 3:00 na yamma, shugaban ƙaramar hukumar Roni, Hon. Dr. Abba Ya’u, tare da tawagar Dr. Abba Youth Political Initiative Forum, sun gudanar da zagayen gaisuwa, jaje, duba marasa lafiya da kuma sauraron korafe-korafen al’umma a wasu mazaɓu da garuruwan ƙaramar hukumar Roni.

Mazaɓun da aka ziyarta sun haɗa da:

1) Amaryawa Ward
2) Ƴanzaki Ward
3) Gora Ward
4) Kwaita Ward
5) Zugai Ward

Wannan ziyara ba siyasa kawai ba ce, ziyara ce ta tausayi, kulawa da shugabanci na gari. Shugaban ya tsaya wajen:

• Jajantawa iyalan da s**a yi rashin ‘yan uwansu

• Taya alhini ga waɗanda gobara ta shafa

• Duba marasa lafiya

• Tare da karɓar korafe-korafe da buƙatun jama’a domin nemo mafita ga matsalolinsu.

A zahiri, shugaba na gari shi ne wanda ba ya nesanta kansa da al’umma, musamman a lokacin da suke cikin damuwa da ƙalubale. Wannan namijin ƙoƙari na Hon. Dr. Abba Ya’u ya nuna cewa yana tafiya tare da jama’arsa, yana sauraron su kuma yana jin raɗaɗinsu.

Allah ya saka masa da alheri, ya ƙara masa lafiya da hikimar ci gaba da yi wa al’ummar Roni hidima cikin tausayi, adalci da kishin jama’a.

✍️ Madaniyyu Halliru Takwardawa
Vice Chairman, Dr. Abba Youth Political Initiative Forum

Date: 11th May, 2026
Time: 05:50 PM

A LEADER WHO FEELS THE PAIN OF HIS PEOPLE,HON. DR. ABBA YA’UFrom 8:00 AM to 3:00 PM yesterday, the Executive Chairman of...
11/05/2026

A LEADER WHO FEELS THE PAIN OF HIS PEOPLE,HON. DR. ABBA YA’U

From 8:00 AM to 3:00 PM yesterday, the Executive Chairman of Roni Local Government, Hon. Dr. Abba Ya’u, alongside members of the Dr. Abba Youth Political Initiative Forum, carried out a sympathy and solidarity tour across different wards and communities within Roni Local Government Area.

The visit covered the following wards:

1- Amaryawa Ward
2- Yanzaki Ward
3- Gora Ward
4- Kwaita Ward
5- Zugai Ward

This was not just an ordinary political visit — it was a humanitarian and compassionate outreach aimed at standing with the people during difficult moments.

During the tour, Hon. Dr. Abba Ya’u:

sympathized with families who lost their loved ones,

condoled with victims affected by fire outbreaks,

visited and checked on sick people,

and also listened to complaints and concerns raised by members of the communities in order to seek lasting solutions to their challenges.

Indeed, true leadership is not about staying far from the people, but about standing with them in moments of pain, hardship, and need. This noble effort by Hon. Dr. Abba Ya’u clearly reflects a leader who listens, cares, and shares in the feelings of his people.

May Almighty Allah continue to strengthen and guide him in serving the people of Roni with wisdom, compassion, and justice.

✍️ Madaniyyu Halliru Takwardawa
Vice Chairman, Dr. Abba Youth Political Initiative Forum

Date: 11th May, 2026
Time: 05:41 AM

KO YANZU DR. ABBA YA'U YA BAR SIYASA YA KAFA LEGACY WANDA AL'UMMA BAZA SU MANTA DA SHI BAKamar yanda kuke gani, wasu sab...
03/05/2026

KO YANZU DR. ABBA YA'U YA BAR SIYASA YA KAFA LEGACY WANDA AL'UMMA BAZA SU MANTA DA SHI BA

Kamar yanda kuke gani, wasu sabbin ƙyanƙyasa ne na jami'an sojojin Nigeria da shugaban ƙaramar hukumar Roni ya shigewa gaba har s**a kai ga nasara, wannan ba iya siyasa ba ce, gina al'umma ne.

Muna roƙon Allah ya basu damar yin aiki cikin adalci, Ubangiji Allah ya tsare mana su, shi kuma Dr. Allah ya ƙaro masa dama domin cigaba da gina goben matasan mu Amin summa Amin

01/05/2026

Jajirtaccen shugaba ne, kuma asali ne, Ubangiji ya ƙara inganta shiri

DR. ABBA YOUTH POLITICAL INITIATIVE FORUM ZAƁAƁƁEN SHUGABAN RONI YA DUBA MATSALAR ZAIZAYAR ƘASA A MAZABAR TUNAS Zaɓaɓɓen...
28/04/2026

DR. ABBA YOUTH POLITICAL INITIATIVE FORUM

ZAƁAƁƁEN SHUGABAN RONI YA DUBA MATSALAR ZAIZAYAR ƘASA A MAZABAR TUNAS

Zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Roni, Hon. Dr. Abba Ya’u, ya kai ziyarar gani da ido a mazabar Tunas domin tantance irin barnar da matsalar zaizayar ƙasa ta haifar a yankin.

A yayin ziyarar, shugaban ya samu rakiyar kansilan mazabar Tunas, Hon. Sani Littafi, tare da Hon. Musbahu Ibrahim (Unguwar Mani), wanda ke matsayin Supervisory Councillor na sashen kuɗaɗen shiga (Revenue).

Ziyarar ta bai wa shugaban damar duba halin da ake ciki a wurin da matsalar ta auku, tare da fahimtar matakan gaggawa da ya kamata a ɗauka domin dakile cigaban wannan matsala da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Hon. Dr. Abba Ya’u ya jaddada kudirinsa na ganin an magance matsalar cikin gaggawa, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru wajen nemo mafita mai ɗorewa domin kare al’ummar yankin daga irin wannan barazana.

Ya kuma tabbatar da cewa jin daɗin al’umma da walwalarsu na daga cikin manyan manufofinsa, yana mai cewa zai ci gaba da sanya ido kan duk wasu matsaloli da s**a shafi rayuwar jama’a a faɗin ƙaramar hukumar.

A ƙarshe, al’umma sun nuna godiya bisa wannan mataki, tare da addu’ar Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa cikin nasara.

Abubakar Lawan
Director, Media And Publicity
Dr. Abba Youth Political Initiative Forum
Tuesday, 28 April 2026

Address

Roni

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Abba Youth Political posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share