Sardauniyyah

Sardauniyyah Darusa musa

05/03/2023

Da yardar Allah (S.W.A) duk cigaban da Gwamnatin Mairgirma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da sauran Gwamnatocin baya sukayi zamu ɗaura daganan, haɗi da ingantasu. Kuma Da yardar Allah (S.W.A), zamu baiwa Jahar Sokoto da Mutanen ta fifiko akan komai. Daman taken tafiyar tamu shine . Tafiyar tana ƙumshe da shiraruwa masu anfani da zasu shafi Jama'ar Jahar Sokoto kai tsaye.

Kuma InshaAllahu ba zamu baku kunya idan kuka zaɓe mu. Zamu ƙara bunƙasa tattalin arziki, kuma zamu ƙara kawo hanyoyin da Gwamnati zata rinƙa dogaro da kanta ba tareda mun wahalda Mutanen Jahar Sokto ba. Ko ba komai duk wani cigaba da zamu kawo domin anfanin Jahar Sokoto ne bai ɗaya.

Idan kuka zaɓe mu a ranar Assabar mai zuwa, da yardar Ubangiji, Allah Mai kowa da komai, Sokoto sai dai ta ƙara cigaba ba kan ta koma baya ba. Zamu ƙirƙiri hanyoyi domin ganin tarbiyar Matasan mu bata taɓarɓare ba. Kuma zamu ƙirƙiri yi masu hanyoyi a dokance domin dogaro da kansu ta kowane fanni na rayuwar su.

Munyi tanadin shiraruwa masu tarin yawa da Matan Jahar Sokoto zasu anfana dasu, waɗanda addinin mu na Musulunci ya yarda dasu ta hanyar kare mutuncin su da ƙimar su a idanun duniya. Tafiyar daman tana bisa tubalin girmama Shugabannin mu, Sarakunan mu, Malaman mu, Matan mu, Matasan mu da kuma Ƴaƴan mu na birni da ƙauye da ikon Allah.

Allah Ya ƙara tabbatar ma Jam'iyyar mu ta PDP a dukkan zaɓuɓɓukan da ke tafe nasara. Amin Ya Allah.

5 ga Watan Maris, 2023.

Address

Darusa Musa Gabas
Sokoto
YA,UUMAR

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sardauniyyah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sardauniyyah:

Share

Category