Imam Nafiu Abubakar Almadani

Imam Nafiu Abubakar Almadani أنا لست بشيء🚶
لكن أنا عبدالله👌
أن الله عز وجل خلقني🧑
من ماء نطفة💧
هذاهوأصلي✊
كيف أتكبر❓
I LOVE M

Ya ku maza masu neman aure, abu ne mai kyau mutum ya nemi matar da ta haddace Al-Qur'ani, domin wannan babban falala ne ...
10/06/2026

Ya ku maza masu neman aure, abu ne mai kyau mutum ya nemi matar da ta haddace Al-Qur'ani, domin wannan babban falala ne da ni'ima daga Allah.

Amma yana da muhimmanci ku sani cewa haddar Al-Qur'ani kaɗai ba ita ce ma'aunin kyakkyawar mace ba.

Kafin ka zaɓi mace, ka duba:

🌹 Tarbiyyarta da mu'amalarta da iyayenta da sauran mutane.
🌹 Tsoron Allah da yadda take kiyaye addininta a aikace.
🌹 Kyawawan halaye kamar haƙuri, ladabi, tawali'u da gaskiya.
🌹 Fahimtarta game da hakkokin aure da zamantakewar iyali.

Manzon Allah ﷺ ya nuna muhimmancin addini da kyawawan halaye wajen zaɓen abokin zama.
Domin akwai masu haddar Al-Qur'ani amma ba sa aiki da abin da s**a haddace yadda ya kamata, kamar yadda akwai waɗanda ba hafizai ba amma suke da kyakkyawan ɗabi U da addini da tarbiyya.

Al-Qur'ani a ƙirji babban alheri ne, amma Al-Qur'ani a ɗabi'a da aiki shi ne mafi girman alheri.

Allah Ya ba ku ikon zaɓar abokan zama nagari waɗanda za su taimaka muku wajen bauta masa da gina gida na gari.

"Kar ka tsaya kan abin da ido yake gani kawai, ka duba abin da hali da tarbiyya suke nunawa."

Rashin Mutunci da Rashin Kunya na Wasu Matasa a Wannan Zamani 😭Abin takaici ne yadda a wannan zamani wasu daga cikin mat...
09/06/2026

Rashin Mutunci da Rashin Kunya na Wasu Matasa a Wannan Zamani 😭

Abin takaici ne yadda a wannan zamani wasu daga cikin matasa s**a mayar da shafukan sada zumunta wajen yaɗa bidiyoyi da hotunan da s**a saɓawa tarbiyya da ɗabi'un Musulunci.

Abin da a da ake ɓoyewa saboda kunya, yanzu wasu suna nunawa duniya gaba ɗaya ba tare da jin nauyin Allah ko na al'umma ba.

Allah Maɗaukakin Sarki yace:
﴿ إِنَّ الَّذِينَ يُحِبُّونَ أَنْ تَشِيعَ الْفَاحِشَةُ فِي الَّذِينَ آمَنُوا لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ﴾
"Lalle waɗanda suke son alfasha ta yaɗu a cikin muminai, suna da azaba mai raɗaɗi a duniya da lahira." (Suratun Nur: 19)

Haka kuma Annabi ﷺ yace:
"كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا الْمُجَاهِرِينَ"
"Dukkan al'ummata za'a yi musu afuwa sai waɗanda suke bayyana saɓo a fili." (Bukhari da Muslim)

Ya kamata matasa su sani cewa shahara ta hanyar yaɗa badala ba nasara ba ce, illa ce da za ta jawo fushin Allah, rushe mutunci, da lalata tarbiyyar al'umma.

Duk wanda ya taimaka wajen ɗauka, yaɗawa, ko kallon irin waɗannan abubuwa yana da nasa kaso na alhakin.

Iyaye, malamai da shugabanni suna da nauyin kula da matasa, basu tarbiyya, da kuma jan hankalinsu zuwa ga abin da zai amfane su a duniya da lahira.

Allah ya shiryar da matasanmu maza da mata, ya tsare su daga fitintinu na zahiri da na boye, yasa su zama abin alfahari ga addininsu da al'ummarsu.

Samun mai kuɗi shine yayi wuya, yau idan miji kikeso to gobe za'a iya ɗaura aurenki 😹😹Alhassan Mai Lafia
03/06/2026

Samun mai kuɗi shine yayi wuya, yau idan miji kikeso to gobe za'a iya ɗaura aurenki 😹😹
Alhassan Mai Lafia

*IDAN KA TASHI CIKIN DARE KA CE “YA ALLAH”… TO KA SAN ALLAH YANA SONKA 🤲*😭 Ya kai bawan Allah…*Ba kowa bane Allah yake t...
25/05/2026

*IDAN KA TASHI CIKIN DARE KA CE “YA ALLAH”… TO KA SAN ALLAH YANA SONKA 🤲*

😭 Ya kai bawan Allah…

*Ba kowa bane Allah yake tashi cikin dare*

_Akwai mutane yanzu, suna barci cikin gafala, wasu cikin saɓo🔥_

wasu ma basu tuna Allah ko sau ɗaya ba…

*Amma kai…* Allah Ya tashe ka cikin dare. Ka ji wani abu a zuciyarka yana cewa:

> “Ka yi addu’a…” 🤲

*Wallahi wannan rahma ce mai girma.*

😭 Ka sani ?

Akwai lokaci a cikin dare: inda Allah yake saukowa zuwa saman duniya cikin rahamarsa…

Sai Yace:

> “Waye yake roƙona in ba shi ? Waye yake neman gafara in gafarta masa ?” 😭

Amma mutane da yawa suna barci… suna rasa wannan babbar ni’ima.

*😭 Ya kai ɗan’uwa…*

_Kada ka raina raka’a biyu cikin dare, hawaye ɗaya saboda Allah, ko addu’a ɗaya daga zuciya mai gaskiya._

_Domin akwai mutane da addu’ar dare ta canza rayuwarsu da tahajjud ya zame musu mafitar matsaloli, da kuka cikin sujada ya zama dalilin gafarar zunubansu. 🤲_

Ga addu’a mai girma da ya dace ka yawaita a cikin dare:

> اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي

Ma’ana:

> “Ya Allah! Kai Mai yawan afuwa ne, Kana son afuwa, Ka yi mini afuwa.” 🤲

😭 Ka tashi dare ko da mintuna kaɗan ne… ka tsaya gaban Allah.

Ka gaya masa....

*damuwarka, zunubanka, burinka, kukanka…*

Domin Allah baya ƙin bawansa idan ya zo gare Shi cikin tawali’u. 🤲

😭 Wataƙila:

*addu’ar dare ɗaya, hawaye ɗaya, ko sujada ɗaya…*

ita ce zata canza rayuwarka gaba ɗaya.

Kuma ka sani…

A ranar Alƙiyama… akwai wasu mutane da fuskokinsu zasu haskaka saboda:

*sujada cikin dare, kuka saboda tsoron Allah, da addu’ar da babu wanda ya sani sai Allah. 😭*

🤲 Ya Allah… Ka sanya mu cikin masu tashi dare domin neman yardarka…

*`Ameeen Thumma Ameen 🤲`*

Labaran Musulunci
🙏🙏🙏🙏🙏😁😁✍️

Roba roba baya layyah 😁
25/05/2026

Roba roba baya layyah 😁

24/05/2026

*Innah Lillahi Wa Innah Ilaihi Raji'un🥹*
*Yan Uwa Mata Akula Pls🙏🥹*

Auren wuri alheri ne mai girma sosai, kuma babbar hanyar kare mutunci.Wadannan yaran, abun sha'awa tunda gasu ƙananan sh...
23/05/2026

Auren wuri alheri ne mai girma sosai, kuma babbar hanyar kare mutunci.

Wadannan yaran, abun sha'awa tunda gasu ƙananan shekaru dasu da zaiyi wahala su haura shekaru 18 Amma gashi an hadasu haɗi na auren sunnah, har ma sun haifu, dayake abun arziki akayi, uwa na farin ciki uban na farin ciki, haka iyayen su, harda yi musu hoto ana nunawa.

Wannan itace koyarwar Musulunci, addini yana son duk wata kofa ta rufe wata barna.

Nidai an burgeni anan sosai fa, kuma sun bani sha'awa sosai.

Allah yasa iyaye musamman masu hali su rinka yin ire-iren haka ga yaran su, domin kare su tun suna kanana...

ALAMOMIN SON AURE TA BANGAREN  MATA ........🧕💞1.Idan kaga mace🧕 tana hira da saurayi a inda tasan babanta zai iya kallon...
22/05/2026

ALAMOMIN SON AURE TA BANGAREN MATA ........🧕💞

1.Idan kaga mace🧕 tana hira da saurayi a inda tasan babanta zai iya kallon ta AURE TAKESO💞 ,👈

2.Idan kaga mace 🧕 tana riha da suurayi a inda tasan yayanta zai iya kallon ta AURE TAKESO💞, 👈

3.Idan kaga mace🧕 tana yawan zama a daki ita kadai AURE TAKESO💞, 👈

4.Idan kaga mace🧕 tana fitowa tsakar gidan su tazauna ta 6ata rai idan aka tambaye meke damun ki tace bbu AURE TAKESO💞, 👈

5. Idan kaga mace 🧕 tana waya da saurayi a gidan su kuma tana daga murya AURE TAKESO💞,

6. Idan kaga mace 🧕 tana yawan murmushi ita kadai AURE TAKESO💞, 👈

7.Idan kaga mace 🧕 tana yawan status da waqoqi ko vedios na soyayyah💞 AURE TAKESO💞, 👈

8.Idan kaga mace 🧕 tana yawan kula samari🧔 AURE TAKESO💞, 👈

9.Idan kaga mace🧕 tana yawan sambatu ita kadai AURE TAKESO💞, 👈

10. Idan kaga mace 🧕 ta tsaya ta karanta wannan posting din tsaff AURE TAKESO 💞. 👈
🫣😒🫣🚶

Na barku lafiya 🚶🤗😎🤣

Duniya Takusa tashi  ka karanta dan Allah Akwai wani Wanda yake bada Labari cewaAkwai wata mata wadda tasamu mijin aure ...
20/05/2026

Duniya Takusa tashi ka karanta dan Allah

Akwai wani Wanda yake bada Labari cewa

Akwai wata mata wadda tasamu mijin aure Sai ya siyamata wata babbar waya wadda acikin set ɗinta ba’a samun masu kalar Wannan wayar

Matsaloli suna ta shiga tsakanin ta da shi,Yau ayi fada gobe a shirya,haka yaci gaba da Hakuri,wata Rana Sai ransa ya6ace yarasa yanda zayayi hakurin sa yaQare,Sai ya tura abokin sa Domin ya anso wayar da ya bata

Abokin nasa Sai ya tura yaron sa Domin ya kar6o wayar,yana anso wayar wajen shige shiren sa Sai yashiga (trash) yana shiga babu abunda yagani Sai videon ta lessbian da ita da Qawayen ta da kuma Wanda tayi ita kaɗai

Kuma yarinyar idan kaganta zakace malama ce,Tana sanya hijabi da NiQab kuma bata shigar banxa Amma Sai dai kash ta 6ata rayuwar ta Akan Wannan Abu da takeyi…

🌸 Nasiha Akan Taimakon Bazawara da Miskini ❤️> “’Yan’uwa…” 🤲Kada mu raina taimakon bazawara 😢musamman wacce ta rasa miji...
19/05/2026

🌸 Nasiha Akan Taimakon Bazawara da Miskini ❤️

> “’Yan’uwa…” 🤲

Kada mu raina taimakon bazawara 😢
musamman wacce ta rasa mijinta 💔
tana fama da rainon yara da damuwar rayuwa 😔

Wasu matan 🌿
suna boye hawaye a cikin dare 😢
suna kokarin ganin ‘ya’yansu sun rayu cikin kwanciyar hankali ❤️

Addinin Musulunci 🤲
ya karfafa mana guiwa wajen taimakonsu 🌿
da tausaya musu ❤️
da share musu hawaye 😔

Ka tuna 🤲
wata karamiyar kyauta ❤️
ko taimako 🌿
ko magana mai dadi 😢
na iya zama silar farin cikin rayuwarsu ❤️

Kada ka wulakanta bazawara ❌
kada ka cutar da ita ❌
domin Allah yana son masu tausayi 🤲🌿

📖 Hadisi

> قال رسول الله ﷺ:
((الساعي على الأرملة والمسكين كالمجاهد في سبيل الله))
(Bukhari da Muslim)

📝 Ma’ana:

> “Mai taimakon bazawara da miskini kamar mai jihadi ne a hanyar Allah.” ❤️🤲

> “Ka share hawayen bazawara 😢
Allah zai share naka 🤲❤️”

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Nafiu Abubakar Almadani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category