Dr, Shamsudeen Grassroot Mobilizer

Dr, Shamsudeen Grassroot Mobilizer Official platform for Dr. Shamsudeen’s political campaign. Share ideas, organize events, and drive gr

SOKOTO NDC CHAIRMAN CONGRATULATES IBRAHIM ABDULKARIM ON APPOINTMENT AS PRESIDENTIAL CAMPAIGN DGThe Chairman of the Niger...
26/10/2026

SOKOTO NDC CHAIRMAN CONGRATULATES IBRAHIM ABDULKARIM ON APPOINTMENT AS PRESIDENTIAL CAMPAIGN DG

The Chairman of the Nigeria Democratic Congress (NDC), Sokoto State Chapter, Hon. Bello Sani Yabo, has commended the party’s presidential candidate, Mr. Peter Obi, for appointing Alhaji Ibrahim Hussain Abdulkarim as Director General of the NDC Presidential Campaign Committee.

Yabo described the appointment of the Sokoto-born ICT strategist and youth development advocate as well-deserved, highlighting his wealth of experience in political coordination, youth empowerment, leadership development, and national service.

He noted that the appointment reflects Peter Obi’s inclusive leadership, national outlook, and commitment to empowering young Nigerians with meaningful leadership opportunities.

The Sokoto NDC Chairman urged other political parties to emulate this approach by involving young people in governance rather than exploiting them as political thugs during elections.

He congratulated Alhaji Ibrahim Abdulkarim and prayed for Allah’s guidance and success in his new national assignment.

DR. HAIDO YA KALUBALANCE GWAMNATIN SOKOTO KAN DOGARO DA TALLAFIN GWAMNATI TARAYYASOKOTO — Ɗan takarar gwamnan Jihar Soko...
25/10/2026

DR. HAIDO YA KALUBALANCE GWAMNATIN SOKOTO KAN DOGARO DA TALLAFIN GWAMNATI TARAYYA

SOKOTO — Ɗan takarar gwamnan Jihar Sokoto a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Dr. Shamsuddeen Aliyu Haido, ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin Jihar Sokoto ke dogaro da kuɗaɗen da take samu daga asusun gwamnatin tarayya, maimakon mayar da hankali wajen samar da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga jihar.

A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na ATS Hausa, Dr. Haido ya bayyana muhimmancin sauya salon tafiyar da tattalin arzikin jihar ta hanyar amfani da damar da Sokoto ke da ita wajen bunƙasa noma da kiwo, waɗanda suke daga cikin muhimman hanyoyin samar da arziki da ayyukan yi.

Ya nuna cewa Jihar Sokoto na da damar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ta hanyar bunƙasa harkokin noma da kiwo, tare da ƙarfafa samar da kayayyaki da sarrafa su domin ƙara musu daraja da samar da damarmakin kasuwanci.

A cewarsa, mayar da hankali kan waɗannan fannoni na iya taimakawa wajen ƙarfafa tattalin arzikin jihar, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma rage dogaro da kuɗaɗen da ake rabawa daga gwamnatin tarayya.

Dr. Haido ya kuma jaddada muhimmancin inganta hanyoyin tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida da kuma amfani da albarkatun jihar yadda ya kamata domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Wannan batu na daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a kansu wajen neman hanyoyin ƙarfafa tattalin arzikin jihohi da inganta rayuwar al’umma.

Rahoto: A.A. Yabo Zayyan
Madogara: ATS Hausa

NDC MOVES FORWARD!    3RD NDC NEC MEETING & INAUGURATION OF THE NATIONAL CAMPAIGN COUNCILA significant moment in the jou...
25/10/2026

NDC MOVES FORWARD!

3RD NDC NEC MEETING & INAUGURATION OF THE NATIONAL CAMPAIGN COUNCIL

A significant moment in the journey of the Nigeria Democratic Congress (NDC) is here!

The party is set to convene its 3rd National Executive Committee (NEC) Meeting, alongside the inauguration of the National Campaign Council (NCC), the presentation of Certificates of Return to candidates, and a special dinner.

This important gathering will bring party leaders and stakeholders together to strengthen coordination, reinforce organisational structures, and discuss the road ahead.

DATE: Monday, 26th October 2026
TIME: 10:00 AM
VENUE: JD Event Centre, Kashim Ibrahim Way, Opposite A-Class Park, Maitama District, Abuja.

🤝 A MOMENT OF UNITY. A COMMITMENT TO SERVICE. A SHARED VISION FOR NIGERIA.

As the NDC continues to organise and prepare for forthcoming electoral activities, this gathering represents an opportunity to strengthen collaboration and reaffirm the party’s commitment to democratic participation.

Together, let us build a stronger party and a better future for Nigeria!

NDC — Service to the People!

ƘUNGIYAR KURAME TA NDC A SOKOTO TA TAYA DR. HAIDO MURNAR ZAMA ƊAN TAKARAR GWAMNA JIHAR SOKOTO SOKOTO — Ƙungiyar Matasa M...
24/10/2026

ƘUNGIYAR KURAME TA NDC A SOKOTO TA TAYA DR. HAIDO MURNAR ZAMA ƊAN TAKARAR GWAMNA JIHAR SOKOTO

SOKOTO — Ƙungiyar Matasa Masu Nakasar Ji ta jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Jihar Sokoto ta aika da saƙon taya murna ga Dr. Shamsuddeen Ahmad Aliyu Haido bisa zaɓen da aka yi masa a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Sokoto a zaɓen shekarar 2027.

A cikin wasiƙar da ƙungiyar ta aike wa Dr. Haido mai kwanan wata 13 ga Satumba, 2026, ta bayyana farin cikinta da wannan matsayi, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa gogewarsa da jagorancinsa za su taimaka wajen bunƙasa jam’iyyar da kuma ci gaban Jihar Sokoto.

Ƙungiyar ta kuma tabbatar da cikakken goyon bayanta ga Dr. Haido da jam’iyyar NDC, tana mai cewa mambobinta a faɗin jihar a shirye suke su bayar da gudummawa wajen ayyukan jam’iyya da harkokin zaɓe na shekarar 2027.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yi kira ga Dr. Haido da ya ba da kulawa ta musamman ga al’ummar masu nakasar ji, musamman matasa, ta hanyar samar da damarmakin ayyukan yi, shirye-shiryen ƙarfafa matasa, koyon sana’o’i da sauran shirye-shiryen ci gaba da za su inganta rayuwarsu.

Ta jaddada muhimmancin tabbatar da daidaiton dama ga masu buƙatu na musamman, tare da ganin cewa ba a bar su a baya ba wajen samun moriyar shirye-shiryen ci gaban jihar.

Wannan saƙon ya nuna buƙatar ƙungiyar na ganin an ƙara mayar da hankali kan haɗa masu nakasa cikin shirye-shiryen ci gaban al’umma, musamman ta fuskar ilimi, sana’o’i, aikin yi da walwalar matasa.

Rahoto: A.A. Yabo Zayyan

24/10/2026
DR. HAIDO CONDOLES THE FAMILY OF LATE MALAM ABUBAKAR ALIDr. Shamsuddeen Aliyu Haido has extended his heartfelt condolenc...
24/10/2026

DR. HAIDO CONDOLES THE FAMILY OF LATE MALAM ABUBAKAR ALI

Dr. Shamsuddeen Aliyu Haido has extended his heartfelt condolences to the family of the late Malam Abubakar Ali, who passed away today after an illness.

Dr. Haido expressed his sympathy to the bereaved family, praying that Almighty Allah forgives the deceased, grants him Aljannatul Firdaus, and gives his family the strength and patience to bear this great loss.DR. HAIDO CONDOLES THE FAMILY OF LATE MALAM ABUBAKAR ALI

Dr. Shamsuddeen Aliyu Haido has extended his heartfelt condolences to the family of the late Malam Abubakar Ali, who passed away today after an illness.

Dr. Haido expressed his sympathy to the bereaved family, praying that Almighty Allah forgives the deceased, grants him Aljannatul Firdaus, and gives his family the strength and patience to bear this great loss.

DR. HAIDO YA KARƁI SHAHARARREN ƊAN WASAN BARKWANCI DAN GWARI DA TAWAGARSA CIKIN JAM’IYYAR NDCSOKOTO — A ci gaba da karɓa...
24/10/2026

DR. HAIDO YA KARƁI SHAHARARREN ƊAN WASAN BARKWANCI DAN GWARI DA TAWAGARSA CIKIN JAM’IYYAR NDC

SOKOTO — A ci gaba da karɓar sabbin mambobi cikin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), ɗan takarar gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Shamsuddeen Aliyu Haido, ya karɓi shahararren ɗan wasan barkwanci, Dan Gwari, tare da tawagarsa, a gidansa da ke Sokoto.

A yayin tarbar, Dr. Haido ya bayyana farin cikinsa da matakin da Dan Gwari da tawagarsa s**a ɗauka na shiga jam’iyyar NDC, tare da ba su tabbacin cewa za su samu cikakken haɗin kai da goyon baya a tafiyar siyasar da s**a shiga.

A nasa jawabin, Dan Gwari ya bayyana cewa shawarar shiga jam’iyyar NDC ta samo asali ne daga irin goyon bayan da Dr. Shamsuddeen Aliyu Haido ke bai wa matasa, musamman ta fuskar samar da ayyukan yi da buɗe musu ƙofofin samun ci gaba.

Ya kuma yi alƙawarin bayar da gudummawarsa ta hanyar harkar barkwanci da nishaɗi domin tallafa wa ayyukan jam’iyyar, daga matakin jiha har zuwa ƙasa baki ɗaya.

Taron karɓar sabbin mambobin ya samu halartar wasu shugabannin jam’iyyar, ciki har da sakataren jam’iyyar da mai kula da tsara harkokin yaƙin neman zaɓe (Campaign Coordinator), tare da sauran jiga-jigan NDC.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sabbin masu sha’awar shiga jam’iyyar, yayin da Dr. Shamsuddeen Aliyu Haido ke ƙarfafa hulɗa da matasa da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar Sokoto.

Rahoto: A.A. Yabo Zayyan

Address

Diori Hammani Road Kofar Marke Sokoto
Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr, Shamsudeen Grassroot Mobilizer posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category