Tashar Faira

Tashar Faira Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tashar Faira, Grocers, Yaryasa Tudunwada, Yaryasa.

Dolen Ka Murabbin Ka Shine Haqiqar Madaɗin Annabin KaDaga Ranar Da Kabar Shi Ka Gayawa Kanka Ka Raba Hanya Da Kofar Anna...
07/05/2026

Dolen Ka

Murabbin Ka Shine Haqiqar Madaɗin Annabin Ka
Daga Ranar Da Kabar Shi Ka Gayawa Kanka Ka Raba Hanya Da Kofar Annabin Ka

Amma Inhar Ta Tabbata Irin Murabban Da S**azo Cikin Bayanin Ruhul Adab Ne

Yadda Uwa Bata Chanzuwa Zalika Ba,asauya Murabbi

Kamar Dai Yadda Bb Damar Chanza Allah
Imanin Ka Gareshi Dolen Dole Hidmar Ka Gareshi Wajiban Ziyarar Sa Gareka Farilla

Tunoshi Cikin Dukkan Daqiqa Miqa Wuya Ne

✍️ Dan Lyman Nedai

NORTH EAST /  NORTH WEST.Dayawa daga cikin Ƴan Ɗariqar Kwankwasiyya da kuma Ƴan Tayi daɗi  musamman Kanawan mu suna tuna...
02/05/2026

NORTH EAST / NORTH WEST.

Dayawa daga cikin Ƴan Ɗariqar Kwankwasiyya da kuma Ƴan Tayi daɗi musamman Kanawan mu suna tunanin magana da muke akan Rabiu Musa Kwankwaso Ƙiyayya ce da Munafurci. Allah sarki .

Ya kamata kusani cewa matuqar Zamu iya fitowa bainar Jama'a mu faɗawa duniya cewa Kashim Shettima baza muyi su ba domin basu tsinana mana komai ba, duk da cewa shi ɗan Borno ne to banga dalilin da zai hana mu magana akan wani ba domin ita dai Gaskiya ɗaya ce.

Yau ace duk wani ɗan takara a jamiyyar Adawa su janyewa Kwankwaso domin ya kara da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi da kansa yasan dole sai ya riga rana faɗiwa.

A hali da ake ciki Ceto Nigeria daga hannun Azzaluman nan ba Ƙaramin aiki bane, sannan matuqar basu haɗe wuri guda ba to definitely ana Ruwa.

Banda case da wai lallai sai Atiku Abubakar ko kuma wai au sabida shi ɗan North east ne, haba dai ai tafiyar tafi gaban nan.

A siyasa babu Addini, Kabilanci, ko son zuciya, gaskiya ce kaɗai zata tabbatar dakai da manufar ka.

Abun Alfahirin ma shine wannan karon da Shinkafa za ayi Campaign ba Taliya ba, Alhamdulillahi muna samun cigaba a hankali.

Nigeria sai Shugaban Ƙasar Kano ✊

✍️ Dan Lyman 💓💕💕💕💕❤️🌷

Tijjanawa, da carbi ake wazifa, da voters card ake kawar da ɓarna da zalunci! Please share!         ✍️ Dan Lyman Nedai
04/04/2026

Tijjanawa, da carbi ake wazifa, da voters card ake kawar da ɓarna da zalunci!

Please share!
✍️ Dan Lyman Nedai

RAJAB (4) GASKIYAR NUFIDuk wanda ya samu gaskiya a cikin jānibin Allah toh halinsa zai inganta, al'amarinsa zai cika. So...
24/12/2025

RAJAB (4) GASKIYAR NUFI

Duk wanda ya samu gaskiya a cikin jānibin Allah toh halinsa zai inganta, al'amarinsa zai cika. So da ya wa za ka samu waɗanda su ke bin tafarkin Ahlullahi amma gaskiya tana tsere musu.

Duk wanda zai bi Shehunnai dan gyara alaƙarsa da Allah, to ba bu makawa zai zama sadiqin muridi. Duk wanda ya ke bin su dan wata buƙata da ga cikin buƙatun duniya toh zai yi wahala ya samu gaskiya. Muradin Shehunnai (Na gaskiya) shine: samun Sadiqan muridai waɗanda za su gadar musu da sirrinsu..

- Shehu Ibrahim Niasse rta.

Ranar Alhamis 4/12/2025 wannan shekarar , na shiga ziyarar Maulana bayan saukansu gari, tare da ƴan'uwa a gaban jama'a kowwa ya na ji sanda yai min kyakkyawan sheda da cewa "INA MAKA SHEDA DA GASKIYAR SOYAYYA" (Sidqul Mahabbati)

Na faɗi wannan ne dan godiya ga Allah, domin wannan ba ƙaramin alkhairi ba ne, in dai irin wannan Bawan Allah zai yi min kyakkyawan zato da sheda irin wannan, ka ga kenan mummunar zaton wani Kus'umi ba zai cutar da ni ba. Allah ya sakawa masu mana kyakkyawan zato da dukkanin Alkhairi Alhamdulillah!

يظنون بي خيرا ولا خير إنما
رأو حضرة المحبوب ستر جمالك

✍️ Dan Lyman Nedai

MANZUMA (Littafin Shehu Muhammadu Fal Al-alawiy Attijaniy RTA)Kashi na daya (Falalar Huduri)Shehin Malamin Yana cewa1. K...
23/12/2025

MANZUMA
(Littafin Shehu Muhammadu Fal Al-alawiy Attijaniy RTA)

Kashi na daya (Falalar Huduri)

Shehin Malamin Yana cewa

1. KA SANI! LALLAI KARANTA WURIDIN NAN ZAI SHIRYAR DAKAI WANI GWADABE DA ZAI KAIKA DAKI CAN CIKI.
Wato Karanta lazumi da wazifa da zikirin juma'a na darikar tijjaniya, zai sadar da mutum zuwa ga wani gwadabe da zai samu qwayar shiriya (Ma'arifa) ba ɓawo ba (Shari'a).

2. BARI MA! ABIN KEWAYAWA GARESU CIKIN ABINDA KE TSARKAKE MUSU ZUCIYA, GARESHI YAKE, BABU TA-BA-BA.
Sufaye wayanda suke neman tsarkin zuciya, a cikin karanta wuridin tijjaniya suke samun haka ɗin.

3. SHARAƊINSA SHINE HALARTO ZATIN TSANIN NAN NAMU DAGA FARKO HAR QARSHEN WURIDIN.

Samun Qwayar shiriya da tsarkin zuciya ta hanyar karanta wuridin tijjaniya, tana da sharadi wanda da ita ne buri yake cika. sharadin kuwa shine Halarto Suffar Shehu Tijjani yayin da kake wuridin.

Abin nufi da halartowa (huduri), shine kaji, ka yarda yana zaune a gabanka yana kallon ka bisa yadda kake yin wuridin tun daga kan ladabin da kayi a zaman ka, har zuwa niyyarka da sanin ma'anar abinda kake faɗi har ka gama.

4. YANA TARE DA KAI ADUK YADDA KAYI ZATONSA, WAYANDA S**A SAMU SHIGA, DA HAKA S**A SHIGE.
Gwargwadon yadda ka halarto shehu tijjani, gwargwadon madadin da zaka samu daga gareshi. In ma baka halarto shi ba, haka zaka gama ka tashi babu riba sai dai ladar niyya. Wayanda S**a samu muradi a tijjaniya, da qarfin huduri s**a samu hakan.

5. SHI HUDURI SHINE RAI GA DUKKAN AIKI, KAR KA SHAGALA DA ABINDA BASHI KAKE KARANTAWA A WURIDIN BA.
Wuridi ko wani nau'in ibada, huduri ne ransa. Dan haka kar ka bari wani abu ya shigo zuciyarka yasa ka manta da ma'anar abinda kake karantawa cikin wuridin.

Misali, Ana so ka karanta Istigfari yayin wazifa kana mai sanin ma'anarta kana bibiya Kamar haka: ASTAGFIRULLAH ina tuba ga Allah ALLAZI wannan da LA ILAHA ILLA HUWA babu kowa da komai sai shi ALHAYYUL QAYYUM shine rayayye kuma tsayayye (tun babu kowa ko tsayayye akan lamarinsa dana bayinsa) ✍️ Dan Lyman NedaiLyman

TAYA MURNAR SAMUN KHALIFANCI – SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI NA ALHAJI IBRAHIM DAHIRU Usman BAUCHI. Da sunan Allah Mai Rahm...
01/12/2025

TAYA MURNAR SAMUN KHALIFANCI – SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI NA ALHAJI IBRAHIM DAHIRU Usman BAUCHI.

Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai. Tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban halittu Sayyidina Muhammad Sallalahu Alaihi Wa Sallam da iyalan gidansa, da sahabbansa, da dukkanin masu bin tafarkinsa da gaskiya.

A yau muna mika sakon taya murna, cikin girmamawa da addu’ar albarka ga Sheikh Alhaji Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, bisa karɓar wannan gagarumar ragama na dorawa da wannan gagarumar hidima. Duk da kowa dama ya kwana da sanin cewa a kan hanyar ake a kullum amman yanzu akwai wani sabon yanayi da ya zarce waccen.

Samun Khalifanci wannan babban Shehi wanda ya zama babban Khalifa a cikin Darikar Tijjaniyya ba kawai matsayi ba ne na shugabanci, sai dai mu ce wani babban nauyi ne na cigaba da, tarbiyyartar da muridai da ganin sun samun, tsarkakewar zuciya da jagorantar al’umma cikin hikima da nutsuwa. Wannan matsayi alama ce ta cewa:

Kyakkyawar tarbiyyar da ya gada daga mahaifinsa, babban mujaddadi na zamanin nan. Tsayawa tsayin daka wajen tsare Amanat al-ṭarīqa da inganta hadin kai tsakanin muridai.

Kalubalen da ke gabansa:

Ba wani nauyi ne da zai zo ba tare da kalubale ba. Akwai bukatar:

1. Tsayawa tsayin daka wajen kare martabar darikar Tijjaniyya daga dukkan rudani ko rikice-rikicen da kan taso daga masana ko marasa masaniya. Domin Alhaji Ibrahim akwai bambanci a tsakanin jiya da Yau.

2. Kula da hadin kan ƴaƴa da muridai, domin wannan shi ne ginshikin na tarbiyar Shehul Islam Alhaji Ibrahim Niasee da Shehu Tijjani wanda s**a shimfida.

3. Kara daidaita jama’a a cikin zamanin da duniya ke fuskantar kalubalen tunani, akida, da rikice-rikicen musamman na kafofin sadarwa zamani.

4. Ciyar da darikar gaba ta hanyar ilmantarwa, wayar da kai, da tabbatar da cewa koyawar ta haɓaka kauna, “mu’amala mai inganci” wanda dama mun shaida hakanan wajen wannan sabon Khalifa.

Dan Lyman Nedai dashi da masoyana Zakiru Musdafa Kura Sanin Sharifee Shamsu Alh Magaji Na

Yanzu Yanzu: An kammala tona kabarin da za'a binne malam Dahiru usman Bauchi a Gobe jumma'a idan Allah ya kaimu!Allah ta...
27/11/2025

Yanzu Yanzu: An kammala tona kabarin da za'a binne malam Dahiru usman Bauchi a Gobe jumma'a idan Allah ya kaimu!

Allah ta'ala yaji kanshi da rahama taré da sauran mutane baki daya 🙏

DDan Lyman NedaiYana tawassali da wajan da zaa ajiye Maulana amasaukinsa sbd hidimar da ya yiwa Qur'ani da addinin musulunci da dariqar shehu tijjani Rta da failar shehu abiyamin buqatuna nida masoyana kafatan musamman. Maulaya ZZakiru Musdafa KuraSSanin Sharifee ShamsuFFadimatu ZaharaBBarhama Zallah NiassAAlh Magaji Na BarhamaJJafaru DayyariMMustapha Nafadar Begen AnnabiDan liman masoyinkune wallahi

FASSARAR LITTAFIN RUHUL ADAB (4)Rubutun jiya da kuma na shekaranjiya ba sa cikin jerin baitocin littafin ruhul Adab na b...
27/11/2025

FASSARAR LITTAFIN RUHUL ADAB (4)

Rubutun jiya da kuma na shekaranjiya ba sa cikin jerin baitocin littafin ruhul Adab na biyar da kuma na hudu. Yanzu za mu ta shi a baitin na hudu Sayyadi Shinawi Muhammad Batijjane wannan baitin shi ne na hudu jerin baitocin kuma insha Allah yanzu jere za mu dinga kawo su.

Shehu ya ce:

(4) طريق مخض الفضل والرضوان
أسس بالسنة والفرقان

Wannan darika da na ke kiranku zuwa riko da ita to hanya ce ta tsantsar falala da samun yardar Allah.

طريق

"Hanya ko hanya ta kaiwa ga Allah"

Hanyar da a ke nufi ita ce ta tsarkake zuciyoyi daga datti na son duniya, har sai bawa ya zama wuri mai karɓar falalar Allah da yardarsa.”

"مخض الفضل الرضوان"

Wato hanyar tsantsar falala da yardar Allah.

Kalmar “مخض” tana nufin “tacewa” kamar yadda ake tace tsakuwa a cikin tsaba har sai tsabar ta zama tsantsarta.

Shehu yana nuni da cewa dariƙa ce da take tace halayen mutum har sai ya tsarkaka.

“Al-faḍl” falala ce ta Allah “Ar-Riḍwān” kuma yardarsa ce kamar yanda Ubangiji ya ke cewa.

وَرِضْوَانٌ مِّنَ اللّٰهِ أَكْبَرُ

72: Tauwba

"Yardar Allah ce mafi girma" daga duk wata ni’ima.”

Sai kalmar

أسس

"An gina ta, ko an kafa ta".

بالسنة والفرقان

Bisa a kan tafrakin sunna da kuma Alƙur’ani mai girma (Furqān = Alƙur’ani).

Maulanamu Shehu Tijjani yana cewa:

كلُّ ما جئنا به في الطريقة فهو مؤسَّس على السنة، ومن خالفها فليس منا

"Duk abin da muka zo da shi cikin Darikar, an gina shi ne bisa sunnah; kuma wanda ya saba da sunnah, to ba daga cikinmu ba ne.”

Jawahir Ma'ani

A wani wajen Shehu Tijjani yana kara ce mana

الطريقة التي نحن عليها هي طريق محمد، من سلكها وصل، ومن خالفها ضلّ.
(جواهر المعاني، ج 1 ص 51)

“Wannan hanyar da muke kai ita ce hanyar Annabi Muhammad , wanda ya bi ta zai isa (ga Allah), wanda ya saba mata zai bata.”

Maulanmu Shehul Islam yana kara jaddada mana cewa:

الطريقة هي تصفية القلوب من كدر الأغيار، حتى يصير العبد محلاً لفيض الفضل والرضوا

Darikar Tijjaniyya hanya ce ta samun ma’rifa ta hanyar bin sunnar Dan Lyman Nedai

Babban Shehin Musulunci Hadimin Alƙur’ani  Jagoran Darikar Shehu Tijjani. Ta'aziyyar mu ga daukacin dukkan mutane. Rashi...
27/11/2025

Babban Shehin Musulunci Hadimin Alƙur’ani Jagoran Darikar Shehu Tijjani.

Ta'aziyyar mu ga daukacin dukkan mutane.

Rashin Maulana Sheikh babban rashi ne da ya shafi al’umma gaba ɗaya. Maulana Sheikh mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar ɗan adam musulmai Kirstoci da wadanda su addini rashin ba iya na musulmi ba ne na daukacin al'ummar duniya ne domin an shafe shekaru ana jawo hankulan matasa, domin shiryar da zukata, gyara halaye, da ɗora mutane a kan hanya madaidaiciya.

Yana daga cikin fitattun shugabannin da ba sa gajiya da karantarwa, nasiha, da yin wa’azi cikin hikima. Rashin Maulana Sheikh ya bar rata da ba za a ciketaba. Wannan rashi ya shafi kowa saboda hasken da ya rika haskawa ga daukaci al’umma. Allah Ya ba kowa hakuri rashi.

Ta'aziyyar Mu Ga Dukkan Musulmi

Ya ƴan’uwa Musulmi, mun yi rashi na wani fitaccen malami wanda ya tsaya tsayin daka wajen raya sunnah da kiyaye martabar Musulunci.
Maulana Sheikh yana daga cikin waɗanda s**a tsaya tsayin daka wajen kyautata tarbiyya, karantar da Alƙur’ani, da sanyawa mutane ƙaunar yin ibada.

Wannan rashi ba iya ga ƴan ɗariƙar ne s**a yi ba rashin na kowa da kowa ne a da'irar musulunci ina mika sakon ta'aziyya ga daukacin musulmai duniya.

Ta'aziyyar Mu Ga dauakacin Ƴan Ɗariƙar Tijjaniyya.

Ya jama'ar Darikar Maulanmu Sheikh Tijjani Yau mun ta shi babban rashi na ɗaya daga jigon kantagarmu a karani na Ashirin daya Maulana Sheikh ya rayu cikin bin tsari, kiyaye adabun darika, da raya kalmomin manyan mashahuran awliya’i na wannan darikar riko da hanyarsa shi ne ya zamo mana tilas

Rashin Maulana Sheikh tana nuni da cewa lokaci ya yi da za mu ƙara dagewa wajen bin tafarkin da ya bari tafarkin tarbiyya, tsafta, ibada, da tsantsar biyayya ga Allah.

Ta'aziyyar Mu ga Ahlul-faidah

Ya Ahlul-Faidah, ku ne waɗanda s**a sha rabon tarbiyyarsa kai tsaye.
Wannan lokaci ne na nutsuwa da matsa ƙaimi. Kada mu bari aikin ya tsaya.
Mu kasance kamar yadda Maulana Sheikh yake so:daga Dan Lyman Nedai

Address

Yaryasa Tudunwada
Yaryasa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tashar Faira posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category